Manyan ƙungiyoyi na zawarcin Rogers, Liverpool da City da Arsenal na son Cameroon

Lokacin karatu: Minti 2

Dan wasan tsakiya na Aston Villa da Ingila, Morgan Rogers, na iya jan hankali a kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ta bazara, bayan da Arsenal, da Manchester United da Chelsea suka sabunta sha'awarsu kan dan wasan mai shekaru 23. (Times)

Haka kuma, Bayern Munich na daga cikin kungiyoyin da ke sha'awar Rogers, kuma za su iya fafatawa da kungiyoyin Premier League domin daukar sa. (Mirror)

Kungiyar Juventus na kara samun kwarin gwiwa wajen kokarin daukar golan Brazil Alisson Becker daga Liverpool, inda rahotanni ke cewa dan wasan mai shekaru 33 na bude kofar komawa gasar Serie A. (La Gazzetta dello Sport)

Masu kungiyar Liverpool, wato Fenway Sports Group, sun yi imanin cewa dan kasar Holland Arne Slot zai ci gaba da zama kocin kungiyar a kakar wasa mai zuwa duk da rashin nasarar da suka yi a wannan makon. (Telegraph)

Ana sa ran Aston Villa na cikin kungiyoyin da ke son daukar golan Manchester City da Ingila James Trafford, mai shekaru 23 a wannan bazara. (Football Insider)

Dan wasan tsakiya na Chelsea, Enzo Fernandez, tare da wakilinsa sun ba kungiyar hakuri kan kalaman da ya yi yayin da yake buga wa kasarsa wasa a Argentina, inda ya ambaci yiwuwar komawa Real Madrid. (Sky Sports)

Real Madrid na iya kara kaimi wajen kokarin daukar dan wasan gefe na Bayern Munich da tawagar France, Michael Olise mai shekaru 24, wanda kuma Liverpool ke zawarcinsa, a kasuwar bazara. (Christian Falk)

Liverpool da Manchester City sun shiga sahun Arsenal wajen zawarcin matashin dan wasan gaba na Bayer Leverkusen da Cameroon, Christian Kofane mai shekaru 19. (Teamtalk)

Har yanzu kungiyar Nottingham Forest ba ta karbi wani sabon tayi a hukumance ba kan dan wasan tsakiya na Ingila, Elliot Anderson mai shekaru 23, amma tana shirin karbar tayi kafin gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya, inda Manchester City da Manchester United ke sha'awar sa. (Talksport)

Kungiyar RB Leipzig da Castello Lukeba sun cimma matsaya cewa dan wasan baya zai bar kungiyar a wannan bazara ba, yayin da Arsenal, da Chelsea, da Liverpool da Manchester United ke duba yiwuwar daukar sa. (Teamtalk)