Yarinyar da ta tsere wa auren wuri daga ƙarshe ta zama matar shugaban ƙasa

.
    • Marubuci, Megha Mohan, Maggie Latham and Alvaro Alvarez
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
    • Aiko rahoto daga, Sierra Leone
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 7

Ba ta ɓata wani lokaci ba lokacin da muka tambayi Fatima Bio cewa wane irin wahala ta fuskanta a matsayin ƴar ci-rani a London.

Nan take ta ce "Gwamma haka a kan a ce an aurar da kai ga wani tsohon banza," ta faɗa kai-tsaye, kafin daga baya ta fashe da dariya - inda take nufin shirin da mahaifinta ya taɓa yi na aurar da ita tun tana ƴar ƙarama.

Abubuwa da dama sun sauya daga wancan lokacin.

Daga baya ta zama ƴar fim, daga nan kuma sai ta haɗu da wani mutum lokacin da take tattaunawa da shi kan ƴan ƙasar Sierra Leone da suka yi fice a London, inda daga baya ta aure shi.

Wannan mutumi shi ne Julius Maada Bio - kuma a yanzu shi ne shugaban ƙasar Sierra Leone.

A matsayinta ta matar shugaban ƙasa, ana yi wa Fatima kallon mai kwarjini, sannan kuma a gefe ɗaya ana mata kallon mai raba kawuna.

Wasu matasa na kallon ta a matsayin jagorar kawo sabon tsarin siyasa a ƙasar, wadda ke hanƙoron kare mata da yara mata, yayin da wasu ke ganin ta a matsayin wadda ta fiye zaƙewa kuma ta cika tsoma baki cikin harkokin jam'iyyar mijinta.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An mata ihu, wasu kuma sun kwarzonta ta a majalisar dokokin ƙasar bayan wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na sada zumunta wanda ya ƙunshi wani mai safarar ƙwaya, wanda ta musanta masaniya kan hakan.

Sai ta bar dariyar da take yi, ta natsu ta fara ba mu labarin abin da ya sa ta fara fafutikar yaƙi da auren wuri a Saliyo, wanda ya fito fili a shekarar 2024.

Ita ma dai da ƙyar ta sha daga auren wuri. Tana ƴar shekara 13 ne mahaifinta mai haƙar ma'adinai a lardin Kano ta shirya aurar da ita ga wani mutum mai kimanin shekara 30 wanda take yi wa kallon kawu tun tana ƙarama.

"Ba a tattauna da ni ba, kawai an yanke shawarar ne," in ji ta.

Amma kafin auren, lokacin da ta kai shekara 16 a shekarar 1996, sai aka fara yaƙin basasar Saliyo, wanda ya janyo tsaiko a shirye-shiryen aure, har ta samu damar tserewa zuwa London.

Fatima Bio ta isa London ne a ranar Kirsimeti a filin jirgin Gatwick sanye da riga kawai ba tare da rigar sanyi ba, amma duk da tsananin sanyi da ake yi, farin cikin tsira ya fi muhimmanci a gare ta.

"Zuwa Ingila ne ya cece ni. A can na samu muryata, na samu ƴancina, sannan na fara tsayawa da ƙafufuna, sannan yanzu nake iya tsayawa wasu ƙananan yara," in ji ta.

.

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, A 2022, Bio ta halarci taro a Fadar Buckingham inda ta jagoranci jawabi kan muhimmancin wayar da kan mutane kan cin zarafin mata

Akwai gidajen haya masu sauƙi, duk da cewa akwai sharuɗa da dole mutum ya cika kafin ya kama su. A irin gidajen ta fara sauka a London, kuma har yanzu a gidan take rayuwa tare da ƴaƴanta.

Sai dai tana shan suka a kafafen watsa labarai a Birtaniya da Saliyo na yadda Uwargidan shugaban ƙasa take cigaba da riƙe gidan haya.

Amma ta kare matakin nata, "ƴaƴana dukkansu ƴan Birtaniya ne," in ji ta. "Ina biyan kuɗin haya ne da kuɗina, don haka ban aikata wani laifi ba."

A wata sanarwa, hukumar kula da gidaje ta Southwark ta shaida wa BBC cewa ba ta magana kan masu zama a gidagen haya, amma ta ƙara da cewa, "idan mun tabbatar mutum na cika sharuɗan da suka dace ba mu cika damuwa ba. Muna gudanar a bincike lokaci bayan lokaci domin tabbatar da haka."

Mun ziyarce ta a gonar da ke gidanta da ke kusa da masaukin shugaban ƙasa a birnin Freetown, inda take zaune da mijita Julius Bio, wanda tsohon soja ne da ya zama shugaban ƙasa a 2018, sanan aka sake zaɓen sa a 2023.

 Bio na kiwon kaji da shanu a gidan gonarsu a Freetown
Bayanan hoto, Bio na kiwon kaji da shanu a gidan gonarsu a Freetown

A gonar, matar shugaban ƙasar tana nuna alamar samun kwanciyar hankali sama da aikin da muka ga tana yi a waje.

Ta zagaya da mu cikin gonar muna tattaunawa kan wasu abubuwan da ba a cika tattaunawa ba kamar jinin haila. Saliyo ba ta da doka kan bayar da kyautar audugar mata a makarantu kamar yadda yake a Kenya da Botswana da Afirka ta Kudu da Zambia.

Ƙungiyoyi irin su asusun ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya sun bayyana cewa a Saliyo, mata na daina zuwa makaranta saboda jinin haila saboda suna fargabar ɓata kayan makarantarsu.

"Yara na rashin zuwa makaranta aƙalla sau 80 a shekara saboda jinin haila. Wannan ya sa nake ziyartar makarantu ina raba musu auduga. Ina so yara mata su yi karatu domin su zama cikin waɗanda ake damawa da su."

Duk da wannan matakin ya sa ta samu masoya, har ta kai ga zama shugabar ƙungiyar matan shugabannin ƙasashe Afirka wato Organization of African First Ladies for Development (Oaflad), wasu na ganin tana wuce makaɗi da rawa.

An sake zaɓar Julius Bio shugaban Saliyo ne a 2023 kuma wa'adinsa na biyu zai ƙare ne a 2028

Asalin hoton, JOHN WESSELS/AFP via Getty Images

Bayanan hoto, An sake zaɓar Julius Bio shugaban Saliyo ne a 2023 kuma wa'adinsa na biyu zai ƙare ne a 2028

Tana shiga cikin harkokin jam'iyyar SLPP mai mulki, inda take tashi tana jawabi a tarukan kamfe ko da kuwa mijinta bai halarta ba.

A lokacin da ake ƙaddamar da zaɓukann ƴan majalisar ƙasar a ranar 7 ga watan Agusta, wasu daga cikin ƴan majalisar sun yi mata ihu, amma daga bisani ta bayyana cewa ko a jikinta.

"Lamarin ya nuna cewa ba dukkan maza ba ne masu ilimi. Ba dukkan maza ba ne suka aminta da ƙarfafa gwiwar mata da samar da daidaito. Na daɗe ina fafutikar taimakon mata. Ina jin matsalolinsu ne sai in miƙa ga gwamnati domin a ɗauki mataki," in ji ta.

Bio ta ce tana wayar da kan mata ne domin su kasance cikin waɗanda ake damawa da su a mulki
Bayanan hoto, Bio ta ce tana wayar da kan mata ne domin su kasance cikin waɗanda ake damawa da su a mulki

A kwanakin da muka yi tare, Fatima Bio ta bayyana cewa tana so ta gyara yadda ake kallon ƙasarta. Da muka halarci taron kammala karatu a makarantar Choithram inda ta gabatar da jawabi, mun ga yadda ƴan mata suka riƙa tare ta suna magana da ita.

Bio Musulma ce, addinin da ke da kaso 77 na ƴan ƙasar, amma mijinta Kirista ne, kuma su ne kashi 21 a ƙasar. Ta ce sukan halarci Coci da Masallaci a tare.

Bayan halartar taron Coci ne aka mata sukar da ta fi ɗaga mata hankali. A watan Janairun 2025, kafar Reuter ta ruwaito Leijdekkers wanda ake kira da "Chubby Jos" wanda yana ɗaya daga cikin fitattun dilolin ƙwaya da ake nema a Birtaniyya ya fito a wani bidiyon da ta wallafa.

Da BBC ta tambaye ta game da yadda aka yi ƙasurgumin dilan ƙwaya ya fito a bidiyonta, sai ta ce ba ta ma san shi ba.

Ƴansandan Holland sun ce Leijdekkers - wanda ke sanye da farar riga mai doguwar hannu - na cikin manyan dilolin ƙwaya

Asalin hoton, Facebook via Reuters

Bayanan hoto, Ƴansandan Holland sun ce Leijdekkers - wanda ke sanye da farar riga mai doguwar hannu - na cikin manyan dilolin ƙwaya

"Ban san shi ba saboda ni ba mai aikata laifi ba ce. Ba na kai mutane Coci. Ni Musulma ce, don haka ba zan san mutanen da suke cikin Cocin ba."

Ta kuma yi watsi da raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa Leijdekkers na da ɗa da ƴar da take riƙewa, wadda shugaban ƙasa ya haifa da wata.

Umaru Fofana ya ce tuni ƴan Saliyo sun daina maganar Leijdekkers.

"Talauci ya yi katutu, ga rashin aikin yi. Kullum kowa ta kansa yake yi," in ji shi, inda ya ƙara da cewa babu wanda zai ɓata lokaci yana maganar wani wanda ake nema a Turai.

Tun bayan da turawa suka gano lu'u-lu'u a ƙasar a tsakankanin 1930, har yanzu talakawan ƙasar ba su gani a ƙasa ba.

Sannan yaƙin basasar ƙasar da aka yi a shekarar 1991 zuwa 2002, wanda ma'adinin na cikin abubuwan da suka janyo shi, tare da taimakon dakarun tsohon shugaban Laberiya Charles Taylor ya yi ajalin dubban ƴan ƙasar, sannan ya raba miliyoyi da muhallansu.

Sannan kuma annobar Ebola da ta Covid-19 sun ƙara ɗaiɗaita ƙasar, sannan kuma ga tsadar rayuwa da ta ta'azzara a ƙasar bayan tsadar man fetur saboda yaƙin Rasha a Ukraine.

Tsadar rayuwa ta ƙara jefa ƴan ƙasar cikin ƙunci

Asalin hoton, SAIDU BAH/AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Tsadar rayuwa ta ƙara jefa ƴan ƙasar cikin ƙunci

Haka kuma a daidai lokacin da ake cigaba da tattaunawa kan raɗaɗin da ƴan ƙasar suke ciki na talauci, an fara tattaunawa kan arzikinta.

Amma ta ƙi yarda ta yi magana kan batun, musamman kan zargin iyalanta na da manyan gidajen alfarma a Gambia.

Haka kuma masana harkokin siyasa a ƙasar ta Saliyo na tattauna yiwuwar ganin Fatima Bio wata rana a cikin ƴan takarar neman shugabancin ƙasar.

Shi kansa shugaban na fuskantar ƙalubale, musamman kan taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasar.

"Ba na hanƙoron zama shugabar ƙasa. Komai na Allah ne. Na yi imani da Allah matuƙa, kuma ina da yaƙinin duk abin Allah ke so, shi ne yake faruwa kuma babu wanda ya isa ya hana."