Yadda ilimin 'ya'ya mata yake a Borno shekara 10 bayan sace 'yan matan Chibok
Yadda ilimin 'ya'ya mata yake a Borno shekara 10 bayan sace 'yan matan Chibok
An wallafa
Yayin da a wannan makon ne ake ake cika shekara10 da sace 'yan matan sakandaire ta garin Chibok, BBC Hausa ya yi duba kan ilimin 'ya'ya mata a jihar.
Yanzu haka idan ba an faɗa maka cewa jihar Borno ta yi fama da rikicin Boko Haram na fiye da shekara 10 wanda ya lalata al'amura ciki har da karatun zamani, ba lallai mutum ya fahimci hakan ba.
Tun daga irin tsarin gine-ginen makarantun da kuma irin kayan koyo da koyarwa da aka saka a makarantun lallai jihar Borno ka iya bugun kirji wajen ci gaban karatun 'ya'ya mata.
Sashen Hausa na BBC ya kai wata ziyarar aiki a birnin Maiduguri inda ya leka makarantar 'yan mata ta GGC da ke birnin kuma ga abin da wakiliyar sashen, Badriyya Kalarawi ta gane mana.



