Hotunan bikin auren gata a jihar Kebbi

.
Bayanan hoto, Gwamnatin jihar Kebbi ta gudanar da auren 'yan mata da na zawarawa kimanin 300 a jihar
An wallafa
.
Bayanan hoto, Angwayen sun caɓa ado a wajen auren gatan da aka gudanar a jihar Kebbi
..
Bayanan hoto, An bai wa ma'auratan kayan abinci a matsayin gayan gara
..
Bayanan hoto, An kuma samar wa amaren da kayan ɗaki da kujeru
..
Bayanan hoto, Gwamnatin jihar ce ta biya sadakin duka amaren
.
Bayanan hoto, Gwamnatin jihar ta ce an zaɓo ma'auratan ne bisa sahalewar iyayensu
.
.
Bayanan hoto, Sarkin Gwandu, Alhaji Dr. Muhammad Iliyasu Bashar ne ya bayar da auren amaren a matsayin waliyyinsu
.
Bayanan hoto, Bayan ɗaura auren mai ɗakin gwamnan jihar, Hajiya Nafisa Nasir ta haɗa wa angwayen da amaren walima
.
Bayanan hoto, Kakakin majalisar dokokin jihar Hon Ankwe Zuru ne ya wakilci gwamnan jihar a wajen ɗaurin auren
.
Bayanan hoto, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da Mansur Isah Yelwa na daga cikin malaman da suka halarci auren