Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin sulhun Sanata Barau da Abba Bichi zai ɗore?
A wani mataki da masu sa ido kan siyasar Kano ke ganin zai iya rage zaman ɗar-ɗar da ya mamaye wasu sassan jam'iyyar APC a jihar Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci sulhun siyasa tsakanin Sanata Barau I. Jibrin, da ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Bichi Abubakar Kabir Bichi.
Sulhun ya zo ne a daidai lokacin da lissafin siyasar shekarar 2027 ke ƙara jan hankali, inda manyan jam'iyyun siyasa ke yunƙurin haɗa kan shugabanninsu da magoya bayansu domin fuskantar zaɓe mai zuwa.
Taron sulhun wanda ya gudana a Abuja a ranar Laraba, mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature ya ce shugabannin biyu sun samu damar tattauna saɓanin da ke tsakaninsu, tare da duba hanyoyin da za su yi aiki tare domin ci gaban jam'iyyar APC a Kano da kuma ƙasa baki ɗaya.
Sanarwar ta ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya buƙaci Sanata Barau da Abba Bichi da magoya bayansu da su ajiye duk wani saɓani a gefe, inda ya jaddada cewa nasarar APC a matakin ƙasa da jiha ba za ta samu ba sai an samu haɗin kai, fahimtar juna da sadaukarwa daga kowa.
Ya ce yayin da ake shirin babban zaɓen shekarar 2027, wajibi ne shugabannin jam'iyyar su haɗa kai domin tallafa wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, gwamnatin Kano da kuma dukkan ƴan takarar APC.
Saɓanin siyasa
Sanarwar ta ce gwamnan ya bayyana cewa saɓanin siyasa wani ɓangare ne na tsarin dimokuraɗiyya, amma bai kamata a bari irin waɗannan sabani su zama sanadin raunana jam'iyya ko kawo cikas ga ƙoƙarin da ake yi na ci gaba da bunƙasarta ba.
Haka kuma ya yi kira ga magoya bayan ɓangarorin biyu da su rungumi wannan sulhu tare da kauce wa kalaman zagi, cin mutunci da duk wani abu da zai iya haddasa rabuwar kai a cikin APC.
"Daga yau ban sa ran wani daga cikin magoya bayanku zai fito yana zagin ɗan uwansa. Dole ne mu kawo ƙarshen waɗannan abubuwan da ke ɗauke mana hankali daga abubuwan da suka fi muhimmanci," in ji Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Ya kuma jaddada cewa APC gida ɗaya ce, inda ya ce ya ɗaura wa dukkan masu ruwa da tsaki alhakin warware rikice-rikice ta hanyar tattaunawa, shawara da mutunta juna.
Sanarwar ta kuma ƙara da cewa Sanata Barau Jibrin da Abubakar Kabir Bichi sun yi kira ga magoya bayansu da su guji rura wutar rikici ko tayar da husuma a tsakanin mambobin jam'iyyar.
Sun bayyana cikakken goyon bayansu ga APC tare da alƙawarin ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa domin tabbatar da nasarar jam'iyyar a zaɓe masu zuwa.
Haka kuma sun yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa shiga tsakani a lokacin da ya dace, tare da samar da sulhu da suke fatan zai zama mai ɗorewa, domin karfafa haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin shugabanni da magoya bayan APC a Kano.
Rikicin Sanata Barau da Abba Bichi
Saɓanin da ke tsakanin jiga-jigan guda biyu ya ƙara bayyana ne a ƴan kwanakin baya, inda takun-saƙa da gugar zana da kuma shaguɓe suka dabaibaye siyasar jihar, ko da yake rikici ne da ake yi a cikin duhu.
Rahotanni sun ambato cewa, duk da cewa akwai wata jiƙaƙƙiya a ƙasa tsakanin jiga-jigan siyasar biyu, amma lamarin ya ƙara tsami ne bayan da mataimakin gwamnan jihar Murtala Sule Garo ya yi wasu kalamai masu kama da jirwaye da kamar wanka a wani taro da ya gudana a Bichi.
Garo ya bayyana a wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, inda yake cewa duk wanda ya taɓa Abba Bichi sai ya ji su "ba a Bichi ba ko a Kabo ne".
Wannan zance ya haifar da maida martani daga ɓangaren magoya bayan Sanata Barau Jibrin.
A wani bidiyo na daban kuma an ga shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen Sanata Barau, Injiniya Rabi'u Sulaiman Bichi na mayar da martani cikin kan masu ingiza rikicin da yake tsakaninsa da Sanatan.
'Tinubu na iya taimakawa sulhun ya ɗore'
Masu nazarin siyasa na ganin cewa nasarar wannan sulhu za ta dogara ne kan yadda shugabannin biyu da magoya bayansu suka ɗauki sulhun a aikace, musamman a lokacin da siyasar 2027 ke ƙara ɗaukar zafi a jihar Kano.
Masanin kimiyyar siyasa a Jami'ar Bayero da ke Kano, Farfesa Kamilu Sani Fagge ya ce sulhu tsakanin ƴan siyasa masu taƙun-saka a yanki guda yana da matuƙar muhimmanci domin kauce wa asarar siyasa da kuma tabbatar da zaman lafiya.
A cewarsa, rikice-rikicen cikin gida kan iya hana ƴan siyasa cimma burinsu na siyasa tare da raunana jam'iyyarsu.
"A siyasance, rigingimu musamman a yanki ɗaya suna da hatsari sosai. Da farko dai, su kansu za su iya rasa zaɓe saboda kowa zai yaƙi kowa ne, ya yi ƙoƙarin rusa abokin hamayyarsa. Ka ga su za su iya rasawa, jam'iyyarsu ma ta rasa," in ji shi.
Ya kawo misalin Kano, inda ya ce irin waɗannan rikice-rikice sun taɓa haddasa koma baya ga wasu fitattun 'yan siyasa.
"Misali, a Kano lokacin da Ghali Na'Abba da Kwankwaso suka yi ta rigingimu, a ƙarshe sai faɗi kawai suka yi. Don haka rashin sulhu zai iya kawo irin wannan sakamako."
Farfesa Fagge ya kuma yi gargadin cewa rashin sulhu ba wai ga siyasa kaɗai yake da illa ba, har ma yana iya shafar zaman lafiyar al'umma baki ɗaya.
"Rashin sulhu zai iya haifar da fitina da za ta iya shafar jiha baki ɗaya. Don haka saboda zaman lafiya kaɗai ma akwai buƙatar a samu sulhu."
Dangane da ko sulhun zai ɗore baki ɗaya, Farfesa Fagge ya ce hakan ya danganta da yadda ɓangarorin suka karɓi yarjejeniyar.
"Idan sun yi amannar cewa an yi adalci, za a zauna lafiya. Amma idan wani ɓangare yana da shakku kan sulhun, za a iya barin baya da ƙura."
Sai dai ya bayyana cewa akwai alamun da ke nuna sulhun na iya samun karɓuwa daga ɓangarorin biyu, musamman saboda dangantakarsu da Shugaba Bola Tinubu.
"Ina ganin yadda ƴan siyasar suka saka ƙwansu a kwando ɗaya, wato suna goyon bayan Tinubu za a iya zama lafiya. Ina ganin sulhun nan akwai sa hannun Tinubu, don haka nake tunanin zai yi wahala wani ya ƙi karɓa, ko da kuwa akwai sauran rina a kaba."
'Suna yi wa juna kallon barazana'
Game da da tushen rigingimu tsakanin ƴan siyasa a yanki ɗaya, ya ce sau da yawa kowanne na kallon ɗayan a matsayin barazana.
"Ko da ɗaya Sanata yake nema, ɗaya kuma ɗan Majalisa, idan ɗaya na kallon ɗayan a matsayin barazana, dole za a riƙa samun rigima."
Ya kuma ce akwai wasu mutane da ke cin moriyar rikice-rikicen siyasa, waɗanda ke taimakawa wajen ƙara ruruta wutar saɓani.
"Akwai masu zuga da suke samun abinci daga rigingimun. Sannan kuma siyasa ba ta akida da manufa ba ce, siyasa ce ta biyan buƙata. Mutane sun fi kallon biyan buƙatun kansu."
Sai dai ya ce har yanzu ana iya sulhunta ɓangarorin da ke kallon juna a matsayin abokan hamayya idan sun fahimci irin asarar da rikici zai iya haifar musu.
"Za a iya yin sulhu muddin sun hango cewa dukkansu za su iya yin asara, musamman idan suna ganin za su bata ran shugaban ƙasa, wanda zai iya ƙin ba su goyon baya. Kuma ka ga hankalinsa yana kan Kano saboda yawan ƙuri'un jihar."