Arsenal na zawarcin Yildiz, Real Madrid ta shiga jerin masu neman Scott

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal na zawarcin ɗan wasan gefe na ƙasar Turkiya, Kenan Yildiz mai shekara 21, daga Juventus, amma ta na fuskantar hamayya daga Bayern Munich da Real Madrid. (Corriere dello Sport)
Real Madrid na duba yiwuwar shiga takarar neman ɗan wasan tsakiya na Bournemouth da Ingila, Alex Scott (mai shekara 23), bayan ta sanya ido kan ɗan wasan a cikin ƴan makonnin nan. (Teamtalk)
Chelsea ce ke kan gaba wajen zawarcin Scott daga Bournemouth, yayin da Liverpool da Arsenal su ma suke nuna sha'awar ɗaukar sa. (Telegraph)
Real Betis za ta yi watsi da duk wani yunƙuri na neman dan wasan gaba Troy Parrott—wanda kwantiraginsa ke ɗauke da sharaɗin biyan fam miliyan 85 idan ana son sayensa—a daidai lokacin da ake ta raɗe-raɗin cewa ɗan wasan mai shekara 24, wanda ke wakiltar Jamhuriyar Ireland, zai iya komawa Tottenham. (Estadio Deportivo)
Ƙungiyoyi da dama a gasar Premier League na sa ido kan dan wasan tsakiya na Sevilla, Lucien Agoume, ɗan kasar Faransa mai shekara 24, kuma kwantiraginsa na ɗauke da sharaɗin biyan kusan fam miliyan 35 idan ana son sayensa. (AS)
Liverpool da Chelsea sun shiga jerin ƙungiyoyi masu zawarcin ɗan wasan baya na Nottingham Forest, ɗan ƙasar Brazil, Murillo, amma ba za a bar ɗan wasan mai shekara 24 ya bar filin wasan City Ground a watan Janairu ba. (Football Insider)
Ɗan wasan gaba na Monaco, Folarin Balogun mai shekara 25, har yanzu yana sha'awar komawa gasar Premier League duk da cewa yunƙurin ɗan wasan na tawagar Amurka na komawa Everton ya ci tura a ranar rufe kasuwar musayar ƴan wasa ta bazara. (Talksport)
Barcelona da Inter Milan na daga cikin manyan ƙungiyoyin Turai da ke sa ido kan ɗan wasan baya na Bosnia, Tarik Muharemovic mai shekara 23, amma Leeds United ba ta da niyyar sayar da ɗan wasan da ta ɗauko daga Sassuolo kan fam miliyan 34 a wannan bazarar. (Football Insider)
AC Milan na iya neman ɗaukar ɗan wasan gaba na Real Madrid, ɗan ƙasar Brazil Endrick, a matsayin aro a watan Janairu, amma yarjejeniyar ba za ta ƙunshi sharaɗin ba da damar ɗaukar ɗan wasan mai shekara 20 kan kwantiragin dindindin ba. (Gazzetta dello Sport)
Tsohon kocin Chelsea da Tottenham, Antonio Conte, na jin daɗin hutun da yake yi daga harkar ƙwallon ƙafa duk da raɗe-raɗin cewa zai iya komawa aikin horaswa a Manchester United ko Juventus.(Football Italia)































