Me Inec za ta yi kan ƴantakara fiye da ɗaya da jam'iyyun adawa suka tsayar?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Wa'adin da hukumar zaɓen Najeriya ta sanya ga jam'iyyun siyasa su kammala gudanar da zaɓen cikin gida sannan kuma su miƙa sunayen ƴan takararsu da za su tsaya musu takarar zaɓen 2027, ya wuce.

Duk da cewa dai jadawalin zaɓen 2027 da hukumar ta Inec ta fitar har yanzu wani abu ne da ke gaban kotu, dukkannin jam'iyyun sun fitar da sunayen waɗanda za su tsaya musu takarar shugabancin ƙasa.

Bugu da ƙari, duk da cewa jam'iyyu sun kammala zaɓen fidda gwani, har yanzu akwai batutuwa masu sarƙaƙiya a jam'iyyu da dama.

Saboda haka yanzu tambayar da ake ita ce mene ne abu na gaba ga waɗannan jam'iyyu da ƴan takararsu musamman waɗanda suka tsayar da guda biyu?

PDP - Goodluck Jonathan ko Sandy Onor?

Da dama dai daga cikin jam'iyyun adawa sun dare zuwa gida biyu inda kowane ɓangare ya fitar da nasa ƴan takarar, yanzu mene ne makomar ƴan takarar?

Jam'iyyar hamayya ta PDP ita ce gaba wajen rabuwar kai, inda ƴan takara guda biyu suka fito a matsayin ƴan takarar shugabancin ƙasa.

Ɓangaren da Kabiru Turaki ke jagoranta ya fito da tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan a matsayin ɗan takarar shugabancin jam'iyyar a 2027.

Shi ma tsagin da Abdulrahman Mohammed ke shugabanci wanda ke samun goyon bayan ministan Abuja, Nyesom Wike, ya tsayar sanata Sandy Onor.

Goodluck Jonathan dai har yanzu bai ce uffan ba dangane da ko ya amince da zai tsaya ko kuma bai amince ba.

To amma kuma shi sanata Onor ya amince da tsayawa takarar inda ya ce zai yi gangamin neman a zaɓe shi ba tare da ɓata lokaci ba.

Daga ƙarshe dai hukumar zaɓe ta Inec ce za ta faɗi wane ne halastaccen dan takara bisa la'akari da shari'o'in kotu duk da cewa akwai yiwuwar batun ya sake komawa ga kotu domin tantancewa.

ADC - Atiku ko Ibe Kachikwu?

Ita ma jam'iyyar hamayya ta ADC na da mutum biyu da suka fito takarar shugaban ƙasar kamar yadda take da ɓangarori guda biyu.

Ɓangaren tsohon ɗantakarar shugaban ƙasa a 2023, Ibeh Kachikuwu ya tsayar da Kachikun a matsayin ɗan takara, inda shi kuma ɓangaren shugaban jam'iyyar, sanata David Mark ya tsayar da tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar.

Ita ma dai wannan jumurɗa kotu ce kawai za ta iya warware ta a nan gaba.

Labour Party - Ahanotu ko Okereke?

Kamar sauran jam'iyyun na adawa a Najeriya, ita ma jam'iyyar Labour Party, LP mutum biyu ne suka fito daga cikinta a matsayin masu neman kujerar shugaban Najeriya a zaɓen 2027.

Dukkannin ɓangarori biyu da suke taƙaddama a jagorancin jam'iyyar sun tsayar da ƴan takararsu, inda ɓangaren Nenadi Usman ya sanar da Chibuzo Okereke a matsayin ɗan takara, shi kuma ɓangaren Julius Abure ya sanar da sunan Kennedy Ahanotu.

A yanzu dai za a iya cewa babu wata shari'a da ake yi kan jagoranci a jam'iyyar LP to amma wannan jumurɗar na nuni da cewa dole ko dai hukumar zaɓe ko kuma kotu ne kawai za su gyara al'amarin.

SDP - Adebayo ko Gabam?

Jam'iyyar SDP ko kuma Social Democratic Party na ɗaya daga cikin tsoffin jam'iyyun siyasa a Najeriya amma kuma ita ma ta hadu da nata rikicin cikin gidan da ya janyo fitar da ƴan takara guda biyu a jam'iyyar.

Ɓangaren Shehu Gaban ya tsayar da Adewole Adebayo a matsayin ɗan takararsa, inda daya tsagin ya bai wa Abimbola Atanda takarar shugabancin Najeriyar a zaɓen 2027.

Gabam dai ya tsaya kai da fata cewa shi ne halastaccen shugaban jam'iyyar ta SDP duk da cewa wani hukuncin kotun ƙoli ya musanta iƙrarin nasa.

Inec na fuskantar shari'a

Ita kanta hukumar zaɓen Najeriya na da tata shari'ar da take fuskanta kuma hukuncin da za a yanke ka iya shafar jadawalin zaɓen na 2027 da hukumar ta fitar.

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja dai ta soke wasu daga cikin jadawalin zaɓen 2027 da INEC ɗin ta fitar to amma duk da haka hukumar zaɓen ta ce ta ɗaukaka ƙara.

Kuma babu tabbas dangane da haƙiƙanin lokacin da kotun ɗaukaka ƙarar za ta yanke hukunci to amma dai hukuncin ne kawai zai fayyace ko zaɓen 2027 zai kasance kamar yadda hukumar ta Inec ta tsara.

Jadawalin zaɓen da Inec ta fitar dai ya nuna cewa zaɓen fidda gwani na jam'iyyu zai kammala ne a ranar 30 ga watan Mayu, sai kuma abin da zai biyo bayansa na miƙa sunaye da takardun ƴan takarar jam'iyyun.

Jam'iyyun na da tsakanin 27 ga watan Yuni zuwa 8 ga watan Agusta domin miƙa takardun ƴan takara da muƙaman da suke nema.

Kuma bayan miƙa takardun, Inec za ta buga jerin sunayen daga ranar 1 ga watan zuwa 29 ga Agusta, inda kuma gangamin yaƙin neman zaɓe zai fara daga ranar 19 ga watan na Agusta.