Masallaci mafi girma a Afirka ta Yamma da tseren kekuna cikin hotunan Afirka

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Wasu daga cikin zaɓaɓɓun hotunan Afirka da na ƴan nahiyar a wasu sassan duniya cikin makon da ya gabata.

Yara na wasan ƙwallon ƙafa
Bayanan hoto, Ranar Laraba ke nan wasu yara na wasan ƙawallon ƙafa a birni mafi girma na Ivory Coast, wato Abidjan.
Masu tseren keke
Bayanan hoto, Amanuel Ghebreigzabhier na Eritrea kan gaba a tseren keke na gasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa karo na bakwai ranar Asabar.
Jama'a a tsattsaye a unguwa
Bayanan hoto, Mazauna garin Bukavu, na Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Kongo, sun taru domin tattaunawa a wani taro da ƴantawayen M23 suka shirya ranar Alhamis bayan sun karɓe birnin.
Mawaƙa na waƙa

Mawaƙi John Legend na Amurka kenan a lokacin taron waƙe-waƙe na Global Citizen da aka yi a Rwanda ranar Juma'a.

Wata mata a tsaye da tufafin ƙawa
Bayanan hoto, Wata mata sanye da kaya daga kamfanin 'yar Najeriya da Birtaniya mai yin kayan ƙawa Tolu Coker a lokacin makon bikin tallata kaya na London ranar Lahadi.
Wasu yara sanye da kayan ƙungiyar agaji ta Izala suna tafiya
Bayanan hoto, Wasu yara ƴan ƙungiyar agaji ta Izala ke nan a birnin Jos na Najeriya, ranar Alhamis.
Wani mutum na sharar masallaci
Bayanan hoto, Ana gyara masallaci mafi girma a Afirka ta Yamma - Masallacin Massalikoul Djinane da ke Dakar, a Senegal ranar Alhamis domin shirin fara azumi.
Namiji ɗauke da jariri da wata mace
Bayanan hoto, Mai ɗaukar hoto Cem Ozdel a lokacin da ya je Gambia inda ya ziyarci bikin suna na Ngente - biki ne na Musulunci da al'ada inda ake raɗa wa jariri suna da aski
Mata a teku
Bayanan hoto, Mai ɗaukar hoto Cem Ozdel ya je bakin teku kuma inda ya ga jiragen masunta a Tanjeh inda mata ke jira su kwaso kifayen da aka kamo
Zakuna biyu da zakanya zaune
Bayanan hoto, Ranar Asabar kenan wasu zakuna biyu da zakanya a gandun namun daji na Johannesburg suna hutawa a inuwa
Wani mutum na tuƙa kwale-kwale a ruwa
Bayanan hoto, Ranar Juma'a kenan inda wani mutum ke tuƙa kwale-kwale a gasar tseren kwale-kwale ta Dusi a Afirka ta Kudu.