Wankan a cikin ƙanƙara, shan madara da sauran sirrukan nasarar Salah

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Nada Hesham
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
A lokacin da Mohamed Salah ya sanar da cewa zai bar Liverpool a karshen kakar bana, tsohon kocinsa Jurgen Klopp ya yaba masa tare da kiransa da "daya daga cikin zararan 'yan kwallon kafa da aka taba yi a duniya."
Tsohon kocin na Liverpool ya horar da Salah na tsawon shekara biyar a Anfield, inda ya zura kwallo 156, ya lashe gasar zakarun turai da Premier da sauran su.
Lallai ba shakka Salah na cikin zaratan 'yankwallo a duniya, amma kwarewa a filin ba ne kadai abin lura.
Ya zama wani jigo abin koyi ba a Liverpool kadai ba, har da wasu wuraren daban.

Asalin hoton, Getty Images
A wani kauye mai suna Nagrig a Masar ya taso. Ya fara was a ne a kungiyar Al Mokawloon Al Arab, inda yake tafiyar awa 14 kullum a mota domin atisaye.
Sai dai bai fara samun nasara da daukaka a dare daya ba.
"Na kasance ba na samun damar buga wasa. Kullum sai dai in je in koma gida ban buga wasa ba," in ji shi a tattaunawarsa da Sport Illustrated.
Ya kara da cewa sai watarana ya je wajen mahaifinsa yana kuka.
"Sai mahaifina ya fada min cewa in kara hakuri domin duk wanda ya samu nasara, sai da ya sha gwagwarmaya."
Salah ya ce wannan maganar ce ta sauya masa tunani, sannan ya kara kwazo da juriya.
Bayan wasu shekaru ne Salah ya bar Masar zuwa turai, inda ya fara da kungiyar Basel da ke buga gasar Swiss Super League.
"Daga ranar da na bar Masar ne ya daura wa kaina cewa duk rintsi sai na dage wajen samun nasara," kamar yadda ya bayyana a wani shirin matasa a takabijin Masar mai suna Kol

Asalin hoton, Getty Images
Haka kuma Salah bai fara samun nasara a turai ba zuwa daya. Ya sha wahala a Chelsea, inda ya kasance ba ya samun damar buga wasa.
Dole ya koma Italiya, inda ya buga kungiyoyin Fiorentina sannan ya koma Roma.
Daga baya ne ya koma Ingila, inda ya fara taka wasa a kungiyar Liverpool.
"Daga ganina za ka san na canja idan ka duba yadda nake a shekara biyar da suka gabata," in ji a tattaunawarsa da BBC a kakarsa ta farko a Anfield.
Bayan shekara tara, lallai za a iya cewa Salah ya bar tarihi mai kyau a Liverpool da ma Ingila.

Asalin hoton, Getty Images
Irin rawar da Salah ya taka a kakar 2017 zuwa 18 ne ya sa aka rera masa wakar "Mo Salah, Mo Salah. Salah la-la, la-la. Sarkin kwallon Masar.
Haka kuma duba da irin yadda Salah yake Musulmi, mawakan sun rera wasu baitoci da ke cewa, "idan ya sake zuwa wasu kwallayen zan zama Musulmi."

Asalin hoton, Getty Images
Salah na cikin 'yan kwallon kafa da suka fi gudu a yanzu kamar yadda kidddigar Opta ta 2021 ta nuna.
Yana iya gudun kilomita 36.64k a duk away daya.
Salah mutum mai kokari da jajircewa. Misali duk da kasancewar mai amfani da kafar hagu, ya dage matuka wajen horar da kansa ya fara amfani da kafar dama.
Amma a wajen Salah, babu lokacin hutu, domin da zarar ya gama wasa yake fara tunanin ko dai atisaye ko was na gaba.
Yana zuwa atisaye a gym akalla sau biyu a rana. Yana kuma wanka a cikin kankara domin jiki ya wattsake.
Haka kuma yana rawar yoga domin jikin ya sake tare da gujewa yawan samun raunuka.

Asalin hoton, Getty Images
Jajircewarsa ba ta tsaya a atisaye ba, yana kula sosai da irin cimakansa.
Ba ya wasa da cin abinci da ke dauke da dukkan sinadarai masu gina jiki, musamman kwai da dankali da madara da ganyayyaki da 'yan'yan itatuwa.
Sannan idan ya koma gida Masar, yana cin wata shinkafa da ake hadawa da albasa da latas da ake kira da koshary.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A Masar ana masa kallon mutum mai kima da mutunci, kuma abin koyi ga matasan kasar.
"Ina so mutanen Masar suka amfani da ni a matsayin abin koyi. Ina so matasa su tashi tsaye wajen neman cikar burinsu."
Sannan ya assasa gidauniyar Mohamed Salah domin taimakon marayu da gajiyayyu a kasar.
Haka kuma a Liverpool, ana masa kallon mutum mai saukin kai da mutunci.
Ana alakanta karin samun hadin Kai a birnin da zuwansa, da raguwar kalaman batanci da kuma samun karin Musulmai magoya bayan ga Liverpool.
Yanzu dai ana rade-radi ne kan makomar Salah bayan barin Liverpool.
A shekarar 2023 ne Liverpool ta ki amincewa da tayin Fam miliyan 200 daga kungiyar Al-Ittihad ta Saudiyya.
Haka kuma sauran manyan kungiyoyin Saudiyya guda uku wato Al Nassr da Al Hilal da Al Alhli suna zawarcinsa.
Bayan haka kuma akwai kungiyoyi a Italiya da Turkiyya da suke zawarcinsa, sai kuma kungiyoyin Amurka.
A gasar kasa da kasa kuma, babban burinsa shi ne lashe gasar kofin Afirka.










