Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Litinin 18/05/2026

  • Sadis Buba
  • Pantami
  • xxx
  • Nafiu Gombe
  • Mace da ƴarta mai lalaurar Autism
  • wata mata
  • BBC reporter

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba da Usman Minjibir

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen shafin a yau.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, mu kwana lafiya

  2. Iran ta girke na'urar tsaron samaniya a tsibirin Qeshm

    Rahotonni daga Iran na cewa ƙasar ta girke na'urorin tsaron sararin samaniya a tsibirin Qeshm.

    Kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ruwaito cewa an girke na'urorin ne saboda ''ƙananan tsuntsaye''

    A cewar Tasnim, kamar yadda ta ambato abin da ta kira ''majiyoyi masu ƙarfi'' na cewa an girke na'urorin ne a Tsibirin Qeshm domin lalata hare-haren abokan gaba.

  3. Elon Musk ya gaza samun nasara a ƙarar da ya shigar da OpenAI

    Elon Musk bai yi nasara a ƙarar da ya shigar kan OpenAI, kamfanin ƙirƙirarariyar basira da aka samar da shi sai dai daga bisani ya soki kamfanin da sauka daga kan tsarin amfanar da al'umma.

    Wani alƙali a California ya ce bai shigar da ƙarar shugaban kamfanin Sam Altman kan lokaci ba.

    Manyan attajiran na zargin junansu da ƙoƙarin amfani da kamfanin wajen samun maƙudan kuɗaɗe a cikin shekara uku.

    Duniya ta zuba ido sosai kan rikicin manyan tattajiran biyu da aka yi tsammanin zai kawo wani gagarumin sauyi a makomar ƙirƙirarriyar fasaha

  4. Danjuma Goje ya rasa takarar Sanatan Gombe a APC

    Tsohon gwamnan Kaduna

    Asalin hoton, Danjuma Goje

    Sanata Muhammad Danjuma Goje ya rasa tikitin takarar sanatan Gombe ta Tsakiya a jam'iyyar APC, a yunƙurinsa na wakiltar mazaɓar a karo na biyar.

    A zaɓen ƴartinƙen da aka gabatar a mazaɓar Sanata Goje ya sha kaye a hannun DCP Mohammed Ahmed (mai ritaya) da ke samun goyon bayan gwamnan jihar.

    Baruren zaɓen da ke sanya ido kan zaɓen Dr Habu Dahiru ya ce DCP Ahmed ya samu ƙuri'a 42,785, yayin da Sanata Goje ya samu ƙuri'a 10,425, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Tun shekarar 2011 Sanata Goje ke wakiltar mazaɓar, bayan kammala wa'adinsa biyu na gwamnan jihar.

    A baya-bayan nan Sanata Goje ya samu saɓani da gwamnan jihar Muhammad Inuwa Yahaya.

  5. Mutum huɗu sun mutu gommai sun jikkata zanga-zangar Kenya

    Ministan harkokin cikin gida na Kenya ya ce aƙalla mutum huɗu ne suka rasu wasu gommai suka jikkata a lokacin zanga-zangar nuna rashin amincewa da ya ƙarin farashin man fetur da ƙasar ta alaƙanta da yaƙin Iran.

    Kipchumba Murkomen ya ce ana ci gaba da bincike kan lamarin.

    Al'ammurra da dama sun tsaya cak sakamakon yajin aikin direbobin motocin haya da suka fara a yau Litinin.

    Yan sanda sun kama masu zanga-zangar sama da 200 tare da harba hayaƙi mai sa hawaye kan masu zanga-zangar.

    Mai magana da yawun rundunar yansanda a Nairobi, Issa Mohamud ya ce za su yi amfani da dukkan ƙarfinsu da doka ta ba su dama wajen shawo kan tarzoma da dawo da zaman lafiya, domin a cewarsa wannan tarzoma ce, ba zanga-zanga ba.

  6. Ko dakatar da ƴan fim na iya gyara masana'antar Kannywood?

    yanwasan

    Asalin hoton, IG/Multiple

    Masana'antar Kannywood ta daɗe tana fuskantar ƙalubale daga cikin gida da kuma waje, waɗanda sukan yi cikas ga harkokinta, har wasu lokutan takan tsaya cak.

    Amma daga cikin manyan ƙalubalen da suka ɗaga hankali masana'antar akwai rigingimun ciki, musamman tsakanin hukumar tace fina-finai - wadda a baya-bayan nan take ƙarƙashin shugabancin ɗan fim - da wasu jarumai.

    A zamanin tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ne aka ƙirƙiri hukumar tace fina-finai domin sanya ido kan yadda masana'antar take gudanar da harkokinta, musamman fina-finai da bidiyo.

    A zamanin, da Malam Abubakar Rabo ke shugabantar hukumar, an yi ta kai ruwa-rana tare da kiraye-kiraye daga masana'antar da a mayar da shugabancin hukumar a ƙarƙashin kulawar ƴayan masana'antar.

    Sai dai daga zamanin Isma'ila Na'Abba Afakallah zuwa yanzu da Abba El-Mustapha yake shugabantar hukumar, an dakatar da ƴan fim da mawaƙa da dama, ciki har da waɗanda aka tura gidan kaso.

  7. Pakistan ta girke ''dakarunta 8,000'' a Saudiyya

    Sojojin Pakistan

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa Pakistan ta girke dakarunta 8,000 da jiragen yaƙi da na'urorin kare sararin samaniya a Saudiyya a wani ɓangare na yarjejeniyar tsaro tsakanin ƙasashen biyu.

    A baya ma'aikatar tsaron Saudiyya ta bayyana batun aikata dakarun na Pakistan da jiragen yaƙinta zuwa Saudiyyar, ba tare da bayyana cikakken bayan game da shirin ba.

    Reuters ta ambato wasu majiyoyin gwamnatin Pakistan na cewa za a girke makaman da sojojin ne domin kare Saudiyya daga hare-haren wasu ƙasashen.

    Majiyoyin sun ce jiragen sojin sun haɗa da jiragen yaƙi 16, mafi yawansu ƙirar JF-17 waɗanda aka ƙera da hannun China.

    A farkon watan Afrilu ne aka aika wa Pakistan jiragen jiragen.

  8. Iran ta musanta illata jagoran addininta Mojtaba Khamenei

    Iran President Press Office / Handout /Anadolu via Getty Images

    Asalin hoton, Iran President Press Office / Handout /Anadolu via Getty Images

    Daraktan hulɗa da jama’a na Ma’aikatar Lafiya ta Iran, Hossein Kermanpour, ya ce rahotanni da ke yawo kan cewa Mojtaba Khamenei ya samu mummunan rauni ba su da tushe.

    Ya bayyana cewa fuskar sa ba ta lalace ba, kuma babu wani sashe na jikinsa da aka yanke, duk da jita-jitar da ta bazu.

    Ya ce an samu rahotannin hare-hare a yankin kusa da Pasteur, inda ofishin gwamnati da gidan jagoran juyin juya hali yake, abin da ya jawo cunkoso da rikici a tituna.

    A cewarsa, Ministan Lafiya ya garzaya zuwa Asibitin Sina domin duba halin da ake ciki, inda aka tabbatar cewa babu wanda ya ji rauni a farkon lokaci.

    Kermanpour ya kuma bayyana cewa daga baya aka kawo Mojtaba Khamenei asibiti, inda aka gano cewa yana da ƙananan raunuka ne kawai.

    An ce an shirya dakin tiyata, amma ba a buƙaci wani babban aiki ba, sai dai an yi ɗinkin wasu raunuka, musamman a ƙafa.

    Rahoton ya kuma ambaci cewa Mojtaba Khamenei bai bayyana a bainar jama’a ba tun bayan rahotannin naɗinsa, yayin da wasu jami’ai da jakadan Iran a Cyprus suka yi iƙirarin cewa ya ji rauni a sassa daban-daban na jikinsa.

  9. Ba a mika mana wani shawarar shirin yarjejeniyar dena kai hari ba - Iran

    Iran ta musanta rahotannin da ke cewa Saudiyya ta gabatar da shawarar rattaɓa hannu kan yarjejeniyar dena kai hari tsakaninta da wasu ƙasashen yankin.

    Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghaei, ya ce a yayin da aka tambaye shi kan batun: “Ba zan iya cewa an gabatar da wani takamaiman shiri ba.”

    A ‘yan kwanakin nan, wasu rahotanni da suka haɗa da na jaridar Amurka The Wall Street Journal sun bayyana cewa Saudiyya ta gabatar da shawarar ƙulla yarjejeniyar dena kai hari tsakanin Iran da ƙasashen yankin Gabas ta tsakiya ba..

    A cikin rikicin da ya haɗa Iran da Isra'ila da Amurka wanda ya fara a ranar 28 ga Fabrairu, Iran ta ce ta kai hare-hare da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙi kan wasu wurare a ƙasashen yankin.

  10. Majalisar WHO na zama na musamman kan Ebola da Hantavirus

    ..

    Asalin hoton, WHO

    Majalisar hukumar Lafiya ta Duniya ta fara zamanta dangane da ɓarkewar cutar Ebola da ta Hantavirus.

    Shugaban majalisar, Victor Atallah Lajam yana gabatar da jawabinsa.

    Kuma nan gaba kaɗan ne shugaban hukumar ta WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus zai gabatar da nasa jawabin.

  11. Halin da ake ciki a DR Kongo bayan ɓarkewar cutar Ebola

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɓarkewar cutar Ebola da ake fama da ita a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo na haifar da damuwa mai tsanani ga al'ummar ƙasar.

    Cutar ta fara yaɗuwa na tsawon makonni kenan ba tare da an gano ta da wuri ba a wani yanki da rikicin yaƙi ke wahalar da aikin agaji da kula da lafiya.

    Nau'in cutar Ebola ɗin da ke yawo a wannan karon yana daga cikin nau'ikan da ba kasafai ake samunsu ba, abin da ke nufin akwai ƙarancin hanyoyin magance ta idan ta kama mutum, duk da cewa tana kashe kusan mutum ɗaya cikin uku da suka kamu da ita.

    Hukumomi sun ce akwai kusan mutane 250 da ake zargi sun kamu da wannan nau'in cutar Ebola, yayin da aka riga aka samu mutuwar kusan 80. Wannan yana nuna cewa cutar ta riga ta bazu fiye da yadda ake tunani tun farko, lamarin da ke sa wannan lokaci ya zama mai muhimmanci wajen daƙile yaduwar ta kafin ta ƙara yaɗuwa zuwa yankuna masu yawa.

    Ko da yake yawanci, ɓarkewar Ebola kan tsaya ne a ƙananan yanki, masana lafiya na tunawa da mummunan ɓarkewar cutar a shekarar 2014 zuwa 2016 a yammacin Afirka, inda mutane 28,600 suka kamu da cutar.

  12. Yajin aiki kan tashin farashin mai ya durƙusar da sufuri a Kenya

    ..

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Dubban ƴan Kenya da harkokin kasuwanci a ƙasar sun shiga wani hali bayan da masu ababen hawa na haya suka tsunduma yajin aikin gama gari domin nuna fushi kan ƙarin farashin man fetur da hukumomi suka yi.

    Muhimman tituna sun zama kufai a Nairbo, babban birnin Kenya lamarin da ya sa jama'a suka zaɓi daɓa sayyadarsu zuwa wajen aiki yayin da wasu yankunan ƙasar suka shiga irin wannan yanayi na matsalar sufuri.

    Harkokin kasuwanci a wasu yankunan Nairobi sun tsaya cak sannan makarantu sun buƙaci ɗalibai su zauna a gidajensu.

    Masu zanga-zanga dai suna toshe tituna. Yajin aikin na zuwa ne kwana biyu bayan da hukumomi suka ƙara farashin mai zuwa matakin da bai taɓa kai wa ba inda aka ƙara farashinsa da kusan kashi 20 cikin 100.

    Kenya, kamar sauran ƙasashen Afirka, ta dogara sosai kan man da ake shigowa da shi daga yankin Gulf, da a yanzu yaƙin Iran ya shafa.

  13. Toshe Mashigar Hormuz na shafar ƙoƙarin kai agaji ga mabuƙata - WFP

    Mataimakin Babban Daraktan Hukumar Samar da Abinci ta Duniya, Carl Skau ya shaida wa BBC cewa ci gaba da toshe Mashigar Hormuz sakamakon yaƙin Iran na shafar ayyukan hukumar na samar da tallafi ga mutanen da ke cikin tsananin buƙata.

    Ya ce tashin farashin man fetur ne ya fi tasiri inda kuɗaɗen da WFP ke kashewa suka ƙaru da kashi 25 cikin 100.

    Sannan ana samun hauhawar farashin kayayyaki a ƙasashe da dama da ke fama da matsalar tsaro.

    Mista Skau ya ce ƙarancin taki sakamakon toshe mashigar zai shafi harkokin noma tare da janyo mummunan tasiri idan aka gaza samar da maslaha musamman a Gabashin Afirka da ta dogara sosai wajen samun kayayyaki daga Yankin Gulf.

  14. Kotu ta umarci a biya Shakira kusan dala miliyan 70

    Shakira

    Asalin hoton, Getty Images

    Babbar Kotu a Sifaniya ta umarci hukumomin haraji na ƙasar da su biya fitacciyar mawaƙiyar nan Shakira, kusan dala miliyan 70 sakamakon shari'ar da aka shafe shekara takwas ana yi.

    Ta yi maraba da hukuncin inda ta ce matakin ya fayyace komai bayan tsawon shekarun ƙunci da ta ce ta fuskanta na ƙoƙarin ɓata mata suna.

    Shakira ta sadaukar da nasararta ga ɗumbin mutanen da suka fuskanci ƙalubale makamancin haka.

    Kotun ta gano cewa an yi ta karɓar miliyoyin daloli a matsayin haraji a hannun Shakira a 2011 bisa kuskure kuma kotun ta gano cewa a lokacin doka ba ta hau kan mawaƙiyar ta biya haraji ba a matsayin mai zama a Sifaniya.

    A don haka kotun ta umarci a mayar mata da cikakken kuɗin tare da kuɗin ruwa.

  15. Najeriya na ƙara sa ido bayan ɓarkewar Ebola a Congo

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Daƙile Yaɗuwar Cututtuka a Najeriya, NCDC ta ce duk da cewa ba a samu ɓullar cutar Ebola ba a ƙasar, tana ƙarfafa matakai don sa ido sakamakon mutuwar mutum 88 a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo da kuma samun mutum guda da aka bayar da rahoton ya kamu da cutar a Uganda.

    Cikin wata sanarwa da Darakta Janar na hukumar, Jide Idris ya fitar a ranar Lahadi, hukumar NCDC tana shirya ayyukan wayar da kai da kuma a faɗin ƙasar.

    Matakin na zuwa ne yayin da Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ayyana ɓarkewar Ebola a Congo da Uganda a matsayin babban abin damuwa.

    Hukumomin lafiya ta ce ɓarkewar cutar tana ɗauke da babban haɗari saboda tuni aka gano ƙwayar cutar a Uganda sannan kuma an samu mutanen da suka kamu a Kinshasa da ke Congo.

    Cutar da ta fara ɓulla a Lardin Ituri na Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo ta shafi kusan mutum 246.

  16. Kotu ta ba da belin El Rufai kan naira miliyan 100

    ...

    Asalin hoton, Nasir El-Rufai/X

    Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El Rufai.

    An bayar da belinsa ne kan naira miliyan 100 da mutum guda da zai tsaya masa kan makamancin kuɗin.

    Mai Shari'a Joyce Abdulmalik ta bayyana tsauraran ƙa'idodin belin inda ta ce wanda zai tsaya masa dole ne ya zama mazaunin Maitama ko Asokoro da ke Abuja sannan kuma dole a miƙa wa kotu takardar shaidar mallakar wata kadara.

    Kotun ta kuma sake bayar da umarni cewa dole ne wanda zai tsaya masa ya zama ma'aikacin gwamnatin tarayya da ke mataki na 17 na ɗaukan albashi sannan kuma ya nuna shaidar albashi na aƙalla wata uku.

    Kotun ta umarci El Rufai ya miƙa duka fasfonsa na fita ƙasar waje da yake da su.

    Mai shari'a Abdulmalik ta kuma umarce shi da ya riƙa zuwa hukumar DSS kowace Juma'ar ƙarshe ta wata domin ya cike rajista har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan ƙarar.

    Kotun ta kuma gargaɗe shi kan saɓa ƙa'idojin da ta ce za su iya sa wa a soke belin da aka ba shi.

  17. Isra'ila ta halaka kwamandan Islamic Jihad da ƴarsa a Lebanon

    Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Lebanon ta ce wani harin makami mai linzami da Isra'ila ta kai kan wani gida a gabashin Lebanon ɗin ya kashe wani kwamandan ƙungiyar Islamic Jihad, da ƴarsa.

    A wani hari na daban kuma ma'aikatar lafiya ta ƙasar ta ce wasu hare-haren sama na Isra'ilar a kudancin Lebanon ɗin ya kashe mutum biyar, da suka haɗa da yara biyu.

    Can a Gaza ma jami'an lafiya sun ce an kashe mutum biyar a wani hari da Isra'ila ta kai, uku daga cikin mutanen sun mutu ne a harin sama kan, wani wuri da ake dafa abincin jama'a a kusa da asibitin Al- Aqsa a tsakiyar birnin na Gaza.

    Rundunar sojin Isra'ila ba ta ce komai ba dangane da hare-haren nata na baya-bayan nan walau a Lebanon ɗin ko a Gaza.

  18. An kashe malami guda cikin malaman da ƴanbindiga suka sace a Oyo

    Gwamna Seyi Makinde

    Asalin hoton, Gov. Seyi Makinde

    Gwamnan jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya, Seyi Makinda ya ce malaman makaranta bakwai aka sace sakamakon hare-haren da ƴanbindiga suka kai kan wasu makarantu uku a ƙaramar hukumar Oriire ranar Juma'a.

    Da yake magana da manema labarai ranar Lahadi, Mista Makinde ya ce an sace malamai bakwai yayin hare-haren inda ya tabbatar an kashe malami guda.

    "Mun samu wani bidiyo da safiyar nan cewa ƴan ta'addan sun kashe ɗaya daga cikin malaman," in ji shi.

    Ƴansanda da hukumomin gwamnati sun ce har yanzu suna ƙoƙarin gano ainahin adadin ɗaliban da suka ɓata.

    Kafafen yaɗa labarai sun ce aƙalla yara 45 aka sace.

    Gwamnan ya ce wasu daga cikin jami'an tsaron da suka kai ɗauki lokacin har-haren ƴanbindigar sun ji rauni.

    Mista Makinde ya ce gwamnati tana yin duk mai yiwuwa domin dawo da ɗaliban hannun iyayensu inda ya ce za su riƙa gabatar da bayanai kowace rana domin sanar da halin da ake ciki.

    Zuwa yanzu dai babau wata ƙungiya da ta ɗauki nauyin kai hare-haren.

    Da farko an rufe makarantu a yankin da alamarin ya faru sai dai gwmanatin daga bisani ta bayar da umarnin a buɗe su sakamakon ruɓnya jami'an tsaro da aka yi.

    Najeriya dai ta fuskanci matsalar sace-sacen mutane da ƴanbindiga ke yi inda ake kai hari kan makarantu don neman kuɗin fansa. An fi samun irin hare-haren a arewacin Najeriya amma lamarin na zama abin damuwa a wasu yankunan kudu maso yammacin ƙasar.

  19. Sojojin Mali sun 'kashe farar hula 10' a harin jirgi mara matuƙi

    Tambarin sojin Mali

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni daga Mali na cewa wani harin jirgin sama maras matuƙi da dakarun gwamnati suka kai ya hallaka fararen hula aƙalla goma, yayin da suke shirin wani bikin aure a yankin San na tsakiyar ƙasar.

    Kamfanin dillancin labarai na Faransa, ya ce wata majiya ta jami'an tsaro ta ce sojin na gwamnatin Mali sun hari wani jerin gwanon babura ne.

    Wani mazaunin yankin ya ce abin da ya kamata ya zama na farin ciki ya zama na baƙin ciki da tashin hankali.

    Lamarin ya faru ne yayin da a watan da ya gabata Malin ta fuskanci gagarumar matsalar tsaro inda mayaƙan da ke da alaƙa da ƙungiyar Al-Qaeda da kuma Buzaye ƴan tawaye suka kai mata wasu jerin hare-hare da suka jijjiga gwamnatin sojin ƙasar ta yammacin Afirka.

  20. Sabbin hare-haren Najeriya da Amurka sun kashe mayaƙan ISIS fiye da 20

    Sojojin Najeriya

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Najeriya da Amurka sun ce sun sake kai jerin hare-hare kan sansanonin mayaƙan ISIS da ke arewa maso gabashin Najeriyar a wani ɓangare na ayyukan fatattakar masu iƙirarin Jihadi a yankin.

    Amurka ta ce an kai hare-haren ne ranar Lahadi bisa haɗin gwiwa da gwamnatin Najeriya.

    Sojojin Najeriya sun ce samamen na baya-bayan nan an ƙaddamar da su ba tare da wata matsala ba a yankin Metele da ke jihar Borno.

    A cewar sojojin, an kai samamen ne bayan da aka gano taruwar ƴan ta'adda a wajen inda suka ce hare-haren sun halaka fiye da mayaƙan Iswap da Isis 20.

    Hare-haren na baya-bayan nan na zuwa ne kwana ɗaya bayan wani hari na haɗin gwiwa na Najeriya da Amurka wanda ya yi sanadin mutuwar Abu Bilal al-Minuki, da ƙasashen biyu suka bayyana shi a matsayin ƙusa a ƙungiyar Isis.

    Hukumomi sun ce samamen wani ɓangare ne na ƙoƙarin murƙushe mayaƙan.

    Cikin wata sanarwa da aka fitar yau Litinin, rundunar Amurka da Afirka, Africom ta ce bayanan sirri da aka tattara sun tabbatar cewa mayaƙan Isis ne a wajen sannan kuma babu wani sojin Najeriya ko Amurka da lamarin ya shafa.

    Rundunar ta ce kashe mayaƙan na ƙara raunana ƙarfin ƙungiyar na shirya share-hare da ke barazana ga tsaron Amurka da ƙawayenta.