Algeria na fuskantar babban matsalar masu tsaron raga, gabanin Gasar Cin Kofin Duniya, kuma tana fatan magance wannan matsala ta hanyar dawo da wani tsohon ɗan wasa daga ritaya.
Oussama Benbot, wanda ya yi ritaya daga tawagar, bayan da bai samu buga wasa ba a Gasar Cin Kofin Afirka (AFCON) a Morocco a ƙarshen shekara, na iya zama mafita ga wannan matsala.
Wannan ya biyo bayan raunin da ya rutsa da wasu masu tsaron ragarta da dama: Melvin Mastil da Luca Zidane duk jinya, yayin da Anthony Mandrea ba zai buga gasar ba.
Benbot mai shekara 31 ya taka rawar gani sosai a ƙungiyar USM Alger, inda ya taimaka musu kaiwa wasan ƙarshe a CAF Confederation Cup, inda za su karɓi bakuncin Zamalek SC a wasan zagayen farko ranar Asabar.
Rahotanni daga kafofin yada labarai na Algeria sun nuna cewa a baya kocin ƙasar, Vladimir Petkovic ya yi fushi da Benbot saboda rashin jin daɗinsa kan rashin samun dama a tawagar ƙasa.
Amma matsalar da tawagar ke fuskanta a yanzu ta sa aka sake kiransa cikin shirin kasar da za a sanar daga baya a wannan wata.
Luca Zidane, ɗan shahararren ɗan wasan Faransa Zinedine Zidane, ya kasance zaɓin farko a AFCON amma ya yi wasan da ba su gamsar ba, sannan ya samu mummunan rauni a muƙamuƙi da ƙugu a wasa da Granada.
Mastil ya yi tiyatar hernia, yayin da Mandrea ya ji raunin kafada a horo, abin da zai sa shi rasa gasar da za a yi a Kanada, Mexico da Amurka.
Mandrea ya kasance zaɓi na farko na Algeria tsawon shekaru biyar, amma bayan saukar kulob ɗinsa Caen zuwa mataki na uku a Faransa, Petkovic ya bayyana cewa ba zai dinga kiran ‘yan wasa daga matakin ƙasa sosai ba.
Zidane mai shekara 27, wanda ya wakilci Faransa a matakin matasa, ya sauya ƙasar da yake wakilta zuwa Algeria a watan Satumba domin zama madadin Alexis Guendouz.
Amma Guendouz shi ma ya ji rauni kafin AFCON, kuma bayan dawowarsa bai sake samun matsayin farko ba a MC Alger.
Rashin tabbaci ya kai ga kiran ɗan shekara 19 Kilian Belazzoug duk da cewa bai taɓa buga wasa a kulob ɗinsa Stade Rennais ba, kuma bai taka leda a wasannin gwaji biyu da ya je ba.
Algeria na cikin rukunin J a gasar, tare da Argentina, Austria da Jordan — rukunin da zai zama mai wahala sosai, musamman idan matsalar mai tsaron raga ta ci gaba.