Fernandes ne gwarzon marubuta labarin tamaula na 2026

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 4 zuwa 8 ga watan Mayun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Dalilai 4 da suka jefa Real Madrid cikin ruɗani, Real Madrid

    Maimakon makon nan ya karkata gaba ɗaya kan wasan da ke da matuƙar muhimmanci na El Clásico tsakanin Real Madrid da Barcelona, rahotanni sun mamaye shi da labaran rikici da rashin kwanciyar hankali a ɗakin canja kaya a Real Madrid.

    Idan Real Madrid ta sha kashi a ranar Lahadi a wasan hamayya a La Liga, hakan zai bai wa Barcelona damar lashe kofin bana karo na biyu a jere, ita kuwa Real Madrid za ta kare kaka biyu a jere ba tare da ɗaukar kofin ba.

    Sai dai yayin da Barcelona — wadda ita ma ta taɓa shiga rikici ba da dadewa ba — ke ci gaba da samun nasarori, Real Madrid na fuskantar ruɗani sakamakon rashin jin daɗi daga magoya baya da rashin tabbas kan makomar koci da kuma zarge-zargen rikici tsakanin ƴan wasa. Latsa nan domin ci gaba da karanta labarin.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  2. , Daga Jaridu

    Barcelona na da dama har ta iya yuro miliyan 100 ta sayi dan wasan Argentina mai kai hari Julian Alvarez daga Atletico Madrid to amma kungiyar ta tsaya ta ga ko dan wasan mai shekara 26 zai nemi barin kungiyar kafin su yi zawarcinsa. (Mundo Deportivo)

    Dan wasa mai kai hari na Serbia Dusan Vlahovic, mai shekara 26, zai kasance ba shi da sauran kwantiragi a bazaran nan da Juventus, kuma yana jiran Barcelona ko Bayern Munich su dauke shi. (Sportmediaset, daga Football Italia)

    Manchester City na tattaunawa da dan bayanta na Crotia Josko Gvardiol mai shekara 24 a kan tsawaita kwantiraginsa da kungiyar. (Sky Sports)

    Brighton, da Leeds United da kuma West Ham ka iya shan kan Brentford a kokarin da take yi na sayen matashin dana bayan RB Salzburg, Jannik Schuster, dan Austria mai shekara. (Teamtalk)

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  3. Palace za ta ɗauki Iraola madadin Glasner da zarar an kammala kakar nan, Premier League

    Kocin Bournemouth, Andoni Iraola, ne ke kan gaba a jerin ƴan takarar karbar aikin Crystal Palace, domin maye gurbin mai horarwa, Oliver Glasner wanda zai bar ƙungiyar a karshen kakar nan.

    Glasner, wanda ya jagoranci ungiyar zuwa wasan ƙarshe na farko a tarihin gasar Turai, zai bar Selhurst Park a wannan watan bayan da ya tabbatar da shawarar sauka daga mukaminsa tun watan Janairu.

    Palace ta kai mataki na gaba wajen neman wanda zai maye gurbinsa, kuma majiyoyi da dama sun nuna cewa Iraola — wanda a watan da ya gabata ya sanar da cewa zai bar Bournemouth — shi ne zaɓin farko na ƙungiyar.

    Baya ga Iraola, an fahimci cewa kocin Coventry City, Frank Lampard da kocin Ipswich Town, Kieran McKenna da tsohon kocin Tottenham Hotspur, Thomas Frank da tsohon kocin Nottingham Forest, Sean Dyche da na Fulham, Marco Silva da kuma na RC Lens, Pierre Sage duk suna cikin sunayen da Palace ta bincika.

    BBC Sport ce ta fara bayyana sha’awar Palace ga Iraola tun watan Janairu. Haka kuma an danganta shi da aikin horaswa a Athletic Bilbao, amma an nada kocin Jamus Edin Terzić a wannan makon.

    Yanzu Palace na ɗaukar matakai masu ƙarfi domin shawo kan Iraola ya ci gaba da zama a Premier League kakar wasa mai zuwa.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  4. Messi na ganin ya kamata Brazil ta je gasar kofin duniya 2026 da Neymar, Brazil

    Ɗan wasan Argentina da kuma Inter Miami, Lionel Messi yana daga cikin waɗanda ke ganin cewa Neymar Jr. ya kamata ya shiga gasar FIFA World Cup mai zuwa tare da Brazil.

    Messi, wanda ya yi wasa tare da Neymar tsawon shekara huɗu a Barcelona, sannan kuma shekara biyu a Paris Saint-Germain, ya ce ya dace Neymar ya buga gasar kofin duniya ta bana kuma ta karshe a tarihinsa.

    A halin yanzu Neymar yana buga wa ƙungiyarsa Santos FC tamaula, inda yake kuma shugabanta a Campeonato Brasileiro Série A, amma raunin gwiwa ya rage masa wasanni da ya yi karawa takwas a 2026.

    Ya sha fama da raunin gwiwa da ya bukaci tiyata a Disamba da kuma wata karin tiyata a Maris, inda ya ci ƙwallaye uku kuma ya bayar da biyu aka zura a raga a wannan kakar.

    Messi ya ƙara bayyana halayen Neymar da cewa mutum ne na “musamman,” yana rayuwa yadda yake ji ba tare da damuwa da ra’ayoyin mutane ba, yana jin daɗin rayuwa cikin sauƙi.

    Neymar ya koma Santos inda ya fara buga ƙwallon ƙafa daga (2009–2013), bayan ya sha fama da rauni a idon ƙafa a zamaninsa a Paris Saint-Germain, sannan kuma ya yi fama da raunin a Al-Hilal SFC wanda ya takaita zamansa a can.

    Tun 2013 Neymar ya kasance muhimmin ɗan wasa a tawagar Brazil, amma bai buga mata wasa ba tun 2023 saboda rauni da matsalar rashin kuzari, duk da cewa ya taka leda a gasar World Cup sau uku a baya.

    Live

    Asalin hoton, EPA

  5. , Daga Jaridu

    Manchester City ce a gaba wajen neman daukan dan gaban Real Madrid da Brazil Vinicius Jr, mai shekara 25, wanda shekara daya da dan lokaci suka rage masa a kwantiraginsa a Bernebau. (Teamtalk)

    Bayern Munich ta tuntubi Newcastle United a kan dan gabanta na gefe kuma dan Ingila Anthony Gordon, mai shekara 25, sai dai akai tazarar fam miliyan 20 a kan yadda Newcastle ta yi masa kudi da kuma yadda Munich ta taya shi. (Mail)

    Dan gaban Paris St-Germain Bradley Barcola zai iya barin kungiyar a bazara, kuma tuni Arsenal, da kuma Barcelona suka nuna sha'awarsu a kan dan Faransan mai shekara 23. (Sky Sports)

    Kociyan Tottenham Roberto de Zerbi yana son amfani da damar da kungiyar take da ta saye dan wasan tsakiya Joao Palhinha na Portugal mai shekara 30 a kan fam miliyan 27, wanda kungiyar ta karba aro daga Bayern Munich. (Mail)

    Live

    Asalin hoton, Getty Images

  6. Marubuta labarin tamaula sun karrama Fernandes na Man United, Manchester United

    Ƙyaftin ɗin Manchester United Bruno Fernandes ya lashe kyautar gwarzon marubuta labarin tamaula, wato “Footballer of the Year” ta Football Writers’ Association.

    Ɗan wasan tawagar Portugal ya ci ƙwallo takwas, ya bayr da 20 aka zura a raga a wasa 34 a dukkan fafatawa a Man United a wannan kakar.

    Fernandes ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta wasan Man United a karkashin kocin rikon kwarya, Michael Carrick.

    Duk da cewa Man United na shirin kammala kakar wasa ta bana ba tare da lashe kofi ba karo na biyu a jere, amma ta samu tikitin buga Champions League a baɗi, bayan da take mataki na uku a kan teburi, kuma saura wasa uku-uku a kammala kakar nan.

    Fernandes shi ne ɗan wasan Man United na farko da ya lashe wannan ƙyauta tun bayan Wayne Rooney a 2010.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  7. Bournemouth na binciken Jimenez kan saƙonni da ya wallafa, Bournemouth

    Bournemouth ta cire mai tsaron baya Alex Jimenez daga cikin ƴan wasanta, yayin da take bincike kan wasu saƙonni da suka bayyana a kafafen sada zumunta.

    Dan wasan mai shekara 21 daga Sifaniya, wanda ya koma buga gasar Premier League daga AC Milan a bazarar bara, ba zai buga wasan Premier League da za su yi da Fulham ranar Asabar ba.

    Jimenez ya fara buga wa Bournemouth wasannin aro kafin daga bisani ya rattaba hannu na dindindin ga ƙungiyar yankin kudancin Ingila a watan Fabrairu kan yarjejeniyar da za ta kare zuwa shekarar 2031.

    Ya buga wasa 32 a wannan kakar a Bournemouth kuma ya ci ƙwallo ɗaya, a nasarar gida da suka yi da ci 3-2 kan Liverpool FC.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  8. Ko rashin Rodri na taɓa ƙwazon Man City?, Manchester City

    A tsawon rayuwar Manchester City da nasarorin da ta samu tare da Rodri, abu guda ya fito fili; ƙungiyar Pep Guardiola tana taka rawar gani sosai idan yana wasa fiye da lokacin da baya nan.

    Wannan batun na cikin alkaluma da suke zahiri. Tun bayan fara wasansa na farko a watan Agustan 2019, City tana da kaso mafi kyau na nasara, tana cin ƙwallaye da yawa, kuma ƙwallaye kaɗan ke shiga ragarta, sannan tana mallakar ƙwallo sosai a wasannin Premier League idan ɗan wasan Sifaniyan yana cikin fili idan aka kwatanta da lokacin da baya nan.

    Yawancin rashin buga wa City wasanni sun faru ne a cikin kakanni biyu da suka gabata. Lokacin da City ta lashe kofin Premier League huɗu a jere — abin da ba a taɓa yi ba — Rodri bai yi wa ƙungiyar wasa bakwai kacal ba, kuma uku daga ciki saboda dakatarwa ne.

    A farkon kakar 2024-25, raunin da ya samu makonni biyar kafin ya lashe kyautar Ballon d'Or ya sa ya yi jinya fiye da wata bakwai; Liverpool FC ce ta lashe kofin a kakar.

    Kakar wasan da yake yi yanzu ma ya ci karo da cikas saboda jinya, amma abin ƙarfafa gwiwa ga magoya bayan City shi ne alkaluma suna nuna cewa ƙungiyar da Guardiola ke jan ragama tana koyon yadda za ta yi nasara ko da babu ɗan wasan mai shekaru 29.

    Daga cikin wasanni 11 da bai buga ba tsakanin ƙarshen Satumba da Ranar Sabuwar Shekara, City ta yi nasara a wasanni tara daga ciki.

    Rodri

    Asalin hoton, Getty Images

  9. Live

    Asalin hoton, Getty Images

  10. Thierry Henry ya ce Arsenal ba ta kai karfin PSG ba

    Thierry Henry ya bayyana cewa ya yi imanin Arsenal ba ta kai matakin da ake bukata ba idan aka kwatanta da abokin karawarta Paris Saint-Germain gabanin wasan ƙarshe a Gasar Zakarun Turai.

    Henry, wanda ya jagoranci Arsenal zuwa wasan ƙarshe a 2006, inda suka sha kashi a hannun Barcelona, ya ce yana fatan ƙungiyar da Mikel Arteta ke jan ragama za ta doke PSG ta lashe kofin a karon farko a tarihi.

    Ya ce: “Ba mu kai matakin su ba tukuna, don haka dole ne sai mun bi wasa a hankali babu gaggawa.”

    Arsenal ta kawo wannan matakinne, bayan da ta yi nasara a kan Atletico Madrid da cin 2-1 gida da waje, yayin da PSG ta fitar da Bayern Munich da cin 6-5.

    Henry ya kuma yaba wa juriya da tsarin tsaron baya da raga daga Arsenal, yana mai cewa PSG suna da wahalar a zura musu ƙwallo, kuma duk da ba sa ƙirƙirar dama da yawa, suna iya amfani da damar da suka samu sosai.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  11. Ko Sifaniya za ta je gasar kofin duniya da Carvajal?

    Kocin Sifaniya, Luis de la Fuente, ya ce bai cire Dani Carvajal daga cikin ƴan wasan da zai je da su Gasar Cin Kofin Duniya ba, amma ya jaddada cewa dole ne mai tsaron bayan ya zama cikin koshin, kafin a yanke hukunci.

    Carvajal, kyaftin ɗin Real Madrid, ya samu rauni a ƙafar dama yayin atisaye a makon da ya gabata.

    Carvajal mai shekara 34 yana gab da shiga makonnin ƙarshe na kwantiraginsa da Real Madrid, kuma ya fuskanci rashin buga wannan da yawa a kakar na, tun bayan da aka sayo Trent Alexander-Arnold.

    Sifaniya za ta fara wasanninta na rukuni da Cape Verde ranar 15 ga watan Yuni, sannan ta kara da Saudi Arabia da kuma Uruguay.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  12. Netherlands za ta kammala shirin zuwa Amurka da wasan sada zumunta a watan Yuni

    Netherlands za ta kammala shirinta na shiga Gasar Cin Kofin Duniya da wasan sada zumunci da Uzbekistan a New York ranar 8 ga watan Yuni, kamar yadda hukumar ƙwallon ƙafa kasar ta sanar ranar Alhamis.

    Za a buga wasan a Icahn Stadium da ƙarfe 2:45 na rana agogon Amurka.

    Tuni Netherlands ta shirya wani wasan sada zumunci da Algeria ranar 3 ga watan Yuni a Feijenoord Stadium, sannan za ta je Amurka washegari domin yin sansanin a New York daga 5 zuwa 8 ga watan Yuni.

    A ranar 9 ga watan Yuni, tawagar za ta wuce sansan da za ta yi a Kansas City, kamar yadda hukumar ta ƙara bayyanawa.

    Netherlands za ta fara wasanninta na rukuni da Japan a Dallas ranar 14 ga watan Yuni, kafin ta kara da Sweden a Houston ranar 20 ga watan Yuni, sannan ta fafata da Tunisia a Kansas City ranar 25 ga watan Yuni.

    Uzbekistan kuwa ta samu tikitin shiga Gasar Cin Kofin Duniya karon farko a tarihinta, kuma tana rukuni tare da Colombia da Portugal da kuma Jamhuriyar Congo.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  13. Algeriya na fuskantar karancin mai tsaron raga daf da fara gasar kofin duniya

    Algeria na fuskantar babban matsalar masu tsaron raga, gabanin Gasar Cin Kofin Duniya, kuma tana fatan magance wannan matsala ta hanyar dawo da wani tsohon ɗan wasa daga ritaya.

    Oussama Benbot, wanda ya yi ritaya daga tawagar, bayan da bai samu buga wasa ba a Gasar Cin Kofin Afirka (AFCON) a Morocco a ƙarshen shekara, na iya zama mafita ga wannan matsala.

    Wannan ya biyo bayan raunin da ya rutsa da wasu masu tsaron ragarta da dama: Melvin Mastil da Luca Zidane duk jinya, yayin da Anthony Mandrea ba zai buga gasar ba.

    Benbot mai shekara 31 ya taka rawar gani sosai a ƙungiyar USM Alger, inda ya taimaka musu kaiwa wasan ƙarshe a CAF Confederation Cup, inda za su karɓi bakuncin Zamalek SC a wasan zagayen farko ranar Asabar.

    Rahotanni daga kafofin yada labarai na Algeria sun nuna cewa a baya kocin ƙasar, Vladimir Petkovic ya yi fushi da Benbot saboda rashin jin daɗinsa kan rashin samun dama a tawagar ƙasa.

    Amma matsalar da tawagar ke fuskanta a yanzu ta sa aka sake kiransa cikin shirin kasar da za a sanar daga baya a wannan wata.

    Luca Zidane, ɗan shahararren ɗan wasan Faransa Zinedine Zidane, ya kasance zaɓin farko a AFCON amma ya yi wasan da ba su gamsar ba, sannan ya samu mummunan rauni a muƙamuƙi da ƙugu a wasa da Granada.

    Mastil ya yi tiyatar hernia, yayin da Mandrea ya ji raunin kafada a horo, abin da zai sa shi rasa gasar da za a yi a Kanada, Mexico da Amurka.

    Mandrea ya kasance zaɓi na farko na Algeria tsawon shekaru biyar, amma bayan saukar kulob ɗinsa Caen zuwa mataki na uku a Faransa, Petkovic ya bayyana cewa ba zai dinga kiran ‘yan wasa daga matakin ƙasa sosai ba.

    Zidane mai shekara 27, wanda ya wakilci Faransa a matakin matasa, ya sauya ƙasar da yake wakilta zuwa Algeria a watan Satumba domin zama madadin Alexis Guendouz.

    Amma Guendouz shi ma ya ji rauni kafin AFCON, kuma bayan dawowarsa bai sake samun matsayin farko ba a MC Alger.

    Rashin tabbaci ya kai ga kiran ɗan shekara 19 Kilian Belazzoug duk da cewa bai taɓa buga wasa a kulob ɗinsa Stade Rennais ba, kuma bai taka leda a wasannin gwaji biyu da ya je ba.

    Algeria na cikin rukunin J a gasar, tare da Argentina, Austria da Jordan — rukunin da zai zama mai wahala sosai, musamman idan matsalar mai tsaron raga ta ci gaba.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  14. Tchouameni ya ji wa Valverde rauni a faɗan da suka yi a Real Madrid

    Rahotanni daga wasu majiyoyi a Real Madrid sun ce rikicin cikin gida da ya dade yana tafasa ya ƙara tsananta ranar Alhamis, bayan da Federico Valverde da Aurelien Tchouameni suka yi fada a ɗakin canza kaya, lamarin da ya sa aka kai Valverde asibiti saboda wani mummunan yanke a kai.

    An ce rikicin ya faru ne a cibiyar horaswar Valdebebas washegarin wata takaddama da ta riga ta faru tsakanin ƴan wasan biyu.

    Mai magana da yawun Real Madrid ya shaida wa Reuters cewa ƙungiyar ba za ta yi sharhi kan abubuwan da ke faruwa a ɗakin canza kaya ba, amma har yanzu suna nazarin yadda za su magance lamarin.

    Majiyoyin sun ce an buɗe binciken ladabtarwa kan duka ƴan wasan, kuma hakan na iya kaiwa ga tara ko dakatarwa.

    Tsananin lamarin ya sa aka gudanar da taron gaggawa tare da manyan jami’an Real Madrid, inda aka ce babu wani ɗan wasa da ya bar filin horaswa sama da awa guda.

    An gudanar da taron ne domin ƙoƙarin hana rikicin ƙara tsananta, yayin da ƙungiyar ke cikin mawuyacin hali.

    Wannan rikici ya biyo bayan wani saɓani a farkon makon nan inda mai tsaron baya, Alvaro Carreras ya amince cewa ya yi wata zazzafar gardama da abokin wasansa, amma ya ce “abu ne na lokaci, kuma an warware,” bayan nan kafofin Sifaniya sun ruwaito wata takaddama tsakaninsa da ɗan wasan Jamus, Antonio Rudiger.

    Kakar wasan Real Madrid ta bana ta ci karo da cikas ta fannoni da dama. An kori koci Xabi Alonso a tsakiyar kakar, sannan wanda ya maye gurbinsa Alvaro Arbeloa ya kasa samun mafita kan durƙushewar ƙungiyar, wadda za ta kare kakar nan ba tare da lashe kofi ba karo na biyu a jere.

    Bayan ficewa daga Gasar Zakarun Turai a hannun Bayern Munich a matakin kwata fainal, Real Madrid yanzu tana bayan Barcelona da tazarar maki 11 a La Liga, yayin da saura wasanni huɗu suka rage a kammala kakar nan.

    Ƙungiyoyin biyu za su haɗu a Camp Nou ranar Lahadi a wasan El Clasico wanda zai iya tabbatar wa Barcelona lashe kofin liga da zarar ta yi nasara a Camp Nou.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  15. Carrick ya fi mayar da hankali kan ci gaban Man United fiye da batun damka masa aikin koci

    Michael Carrick ya ce ya fi mayar da hankali kan kammala kakar wasa a kan ganiya fiye da damuwa kan makomar aikinsa a Manchester United.

    Ƙungiyar ta yi amfani da tsohon ɗan wasanta, tsohon kyaftin da ta bashi aikin kocin rikon kwarya bayan korar Ruben Amorim a watan Janairu cikin yanayi mai cike da rikici, wanda ya taimaka wa Red Devils ta hau zuwa matsayi na uku a Premier League.

    Nasarar da suka yi 3-2 a kan abokiyar hamayyarsu Liverpool a ranar Lahadi ta tabbatar musu da tikitin shiga Gasar Zakarun Turai da saura wasanni uku, wanda hakan ya ƙara mayar da hankali kan muhimman shawarwarin da za a ɗauka a bazara.

    Ana ta tattaunawa kan saye da sayar da ƴan wasa, da kuma wanda zai zama sabon kociyan ungiyar, yayin da Carrick ke ganin shi ne wanda ke kan gaba don ci gaba da aikin bayan karewar kwantiraginsa a ƙarshen kakar nan.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  16. Ƙungiyar magoya baya ta ce kuɗin jirgin ƙasa zuwa filin wasa a Gasar Cin Kofin Duniya bai dace ba

    Wata ƙungiyar magoya bayan Ingila ta ce har yanzu kuɗin jirgin ƙasa daga tsakiyar New York zuwa filin wasa a Gasar Cin Kofin Duniya yana da tsada sosai, duk da rahotannin cewa an rage farashin.

    Jaridar The Athletic ta ruwaito ranar Alhamis cewa kamfanin sufuri na NJ Transit ya rage kuɗin daga Penn Station a New York zuwa MetLife Stadium daga dala 150 ta Amurka (£110) zuwa dala 105 (£77), bayan masu tallafi da wasu kamfanoni masu zaman kansu da suka taimaka wajen rage kuɗin.

    Sashen Fans’ Embassy na Football Supporters’ Association, wanda ke kula da magoya bayan da ke tafiye-tafiye, ya ce wannan ragin bai yi ba.

    A al’ada, kuɗin wannan jirgin bai wuce kusan dala 13 (£9.50) ba. Sashen hulɗa da jama’a na NJ Transit bai mayar da martani nan take ba lokacin da aka nemi sharhi ranar Alhamis.

    Gwamnan jihar New Jersey, Mikie Sherrill, ta jaddada a watan da ya gabata cewa masu biyan haraji a jiharta ba za su ɗauki nauyin dala miliyan 48 (£35.3m) na sufuri a lokacin Gasar Cin Kofin Duniya ba, tana mai cewa “FIFA ce ya kamata ta biya.”

    “A Amurka ana yarda a sake sayar da tikiti, saboda haka idan ka sayar da tikiti da rahusa sosai, mutane za su sake sayar da su da tsada sosai. A gaskiya, kashi 25 cikin 100 na tikitin matakin rukuni ana iya saya da ƙasa da dala 300.

    FIFA ta buɗe wani sabon zango na sayar da tikitin Gasar Cin Kofin Duniya ranar Alhamis, bayan da ta buɗe wani tsarin “sayarwar minti na ƙarshe” ranar 1 ga watan Afrilu, wanda ta bayyana a matsayin mataki na huɗu kuma na ƙarshe na sayar da tikiti wanda zai ci gaba har zuwa ƙarshen gasar.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  17. Fabian Huerzeler ya tsawaita kwantiragi a Brighton

    Brighton and Hove Albion ta ɗauki matakin dakile yiwuwar wasu ƙungiyoyi su nemi kocinta Fabian Huerzeler, bayan da ta amince da tsawaita kwantiraginsa har zuwa watan Yunin 2029.

    Huerzeler mai shekara 33, wanda shi ne mafi ƙarancin shekaru a cikin masu horaswa a Premier League, ya koma Brighton daga St Pauli a 2024 kuma ya kammala kakarsa ta farko a matsayi na takwas mai ban sha’awa.

    Brighton na iya ƙara hawa saman teburi a wannan kakar domin tana matsayi na takwas da saura wasanni uku, maki biyu kacal a bayan Bournemouth da ke matsayi na shida, yayin da take fafutukar samun gurbin gasar zakarun Turai.

    Ci gaban Huerzeler a Brighton ya ƙara masa suna a matsayin ɗaya daga cikin matasan masu horaswa mafi hazaka a Turai, lamarin da ya janyo rade-radin cewa wasu ƙungiyoyi na iya neman sa a bazara mai zuwa.

    Brighton za ta karɓi bakuncin Wolverhampton Wanderers a wannan ƙarshen mako a Premier League yayin da take ƙoƙarin ƙarfafa fatanta na samun gurbin gasar zakarun Turai ta baɗi.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  18. Wasannin da ke gaban Paris St Geramin

    Paris St-Germain tana jan ragamar Ligue 1 da tazarar maki shida a saman tebur, kuma har yanzu tana da wasanni uku da suka rage.

    Wasannin PSG da suka rage a Ligue 1:

    • Lahadi, 10 ga Mayu: PSG da Brest
    • Laraba, 13 ga Mayu: Lens da PSG
    • Lahadi, 17 ga Mayu: Paris FC da PSG

    Ƙungiyar Luis Enrique za ta zama zakara idan ta doke Brest a Parc des Princes ranar Lahadi, sannan Lens da ke matsayi na biyu ta yi kunnen doki ko ta sha kashi a hannun Nantes.

    PSG na iya zama zakara ko da ta yi kunnen doki da Brest, amma sai idan Lens ta sha kashi a hannun Nantes.

    Idan hakan bai faru ba, to nasara a kan abokiyar fafatawar da Lens bayan kwanaki uku tsakani, za ta tabbatar musu da lashe kofin lig karo na biyar a jere.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  19. Wasannin da ke gaban Arsenal

    Kafin wasan ƙarshe a Gasar Zakarun Turai ranar Asabar, 30 ga Mayu, har yanzu akwai fafatawar lashe gasar Premier League ta Ingila ga Arsenal da kuma Faransa ga PSG.

    Wasannin Arsenal da suka rage a Premier League:

    • Lahadi, 10 ga Mayu: West Ham da Arsenal
    • Litinin, 18 ga Mayu: Arsenal da Burnley
    • Lahadi, 24 ga Mayu: Crystal Palace da Arsenal

    Dangane da yadda fafatawar take a teburin gasar, ƙungiyar Mikel Arteta na iya lashe Premier League ranar Laraba, 13 ga Mayu.

    Idan Arsenal ta doke West Ham ranar Lahadi, sannan Manchester City ta sha kashi a hannun Brentford kwana ɗaya tsakani, sannan City ta sake yin rashin nasara da Crystal Palace ‘yan kwanaki tsakani, Arsenal za ta lashe kofin da saura wasanni biyu a kakar.

    Sai dai kuma fafatawar na iya kaiwa har zuwa ƙarshe, inda za a iya tantance zakaran kwanaki shida kacal kafin wasan ƙarshe na Gasar Zakarun Turai.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  20. Kvaratskhelia yana kan ganiya

    Khvicha Kvaratskhelia na PSG ne ya bayar da ƙwallon da Ousmane Dembele ya ci da wuri a wasan daf da ƙarshe a Gasar Zakarun Turai da Bayern Munich ranar Laraba.

    Guillem Balague ya ce: “Akwai wani sihiri na musamman tare da shi” yayin shirin Match of the Day: Champions League.

    Kvaratskhelia ya ci ƙwallaye 10 tare da bayar da shida aka zura a raga a Gasar Zakarun Turai ta wannan kakar.

    Haka kuma ya zama ɗan wasa na farko da ya ci ƙwallo ko ya bayar aka zura a raga a wasa bakwai a jere a cikin kaka guda ta Gasar Zakarun Turai.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images