Sojoji sun ce sun kashe ƴan ta'adda 12 a arewa maso gabas

Asalin hoton, NDHQ
Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation Haɗin-Kai sun hallaka wasu ƴan ta'adda 12 a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar haɗin gwiwa ta Joint Task Force, Laftanar- Kanar Sani Uba ya fitar, inda ya ce sun kuma samu nasarar ƙwato makamai da dama a samamen da suka kai Buba Dalo.
Makaman da aka ƙwato sun haɗa da bindigar AK-47 guda huɗu, bindigogin harba jirage masu saukar ungulu da kuma gurneti.
Kanal Buba ya ce wani samame na daban da sojoji suka kai sansanin ƴan Boko Haram a Gamo, ya ƙara hallaka ƴan ta da ƙayar-bayar shida, tare da lalata kayakinsu.
Sojojin sun kuma samu nasarar daƙile wani hari da mayaƙan ISWAP suka yi niyyar kai wa garin Sabon Gari a karamar hukumar Damboa a ranar Alhamis.
Sai dai, wasu sojoji da kuma ƴan sa-kai na Civilian JTF sun rasa rayukansu yayin daƙile harin.


















