Isra'ila ta ce ta kama wani babban jami'in Hamas a Gaza
Ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz, ya sanar da cewa dakarun ƙasarsa sun kama wani babban jami'in ƙungiyar Hamas a Gaza.
Sanarwar ta zo ne bayan rahotannin da suka bayyana cewa dakarun musamman na Isra'ila tare da wata ƙungiyar Falasɗinawa da Isra'ila ke marawa baya sun gudanar da ayyuka a birnin Gaza.
A cewar ma'aikatan agaji na yankin, hare-haren sama da Isra'ila ta kai sun kashe yara biyu da wata mata.
Sai dai rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai hare-hare ne kan wurare da dama domin kawar da barazana, kuma babu wani soja nata da ya jikkata.
Ministan bai bayyana sunan jami'in Hamas ɗin da aka kama ko yadda aka kama shi ba.
Ya kuma jaddada cewa ayyukan sojojin Isra'ila a yankin Netiv Hasara da ke kusa da arewacin Gaza na ci gaba ba tare da tsayawa ba.