KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 01/09/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 01 ga watan Satumbar 2026.

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Atiku Abubakar
  • NFF
  • Badriyyah Tijjani Kalarawi
  • Ranar Hausa: BBC
  • Danjuma Goje
  • Zainab
  • BBC
  • ABU
  • xxx
  • xxx
  • Khalifa Dokaji
  • Sheikh Jingir
  • Kano
  • Seriki Abbas
  • xxx

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Abdullahi Diginza

  1. Ina aka samo kalmar Takutaha kuma me ya sa ake biki a ranar?

    ....

    Asalin hoton, Abba Hamza

    Wannan maƙala ce da aka rubuta kuma aka wallafa a ranar 12 ga watan Satumban 2025. Yanzu kuma an sake wallafa ta saboda dacewar ranar.

    A wasu biranen ƙasar Hausa, musamman jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, da zarar ranar Maulidin Annabi Muhammad ta zo, ta wuce, hankali yana komawa ne kan bikin Takutaha.

    Ana dai gudanar da bikin Takutaha ne a ranar bakwai daga ranar Maulidi, wato ranar da Hausawa a al'ada suke yin bikin sunan wanda aka haifa.

    A ranar bakwai da haihuwa ne dai aka saba da bikin raɗa suna da yanka da taron bikin na suna idan an samu ƙaruwa.

    Bikin na Takutaha dai yana ɗaukar hankali sosai ne, inda mutane da dama suke bukukuwan shagali da dama, akwai dafe-dafe da yanka, sannan ake hawa domin murnar ranar.

    Sai dai akwai bukukuwan al'ada da dama da ake aiwatarwa a ranar, sannan kuma akwai abubuwa da suke da alaƙa da ibada.

  2. An sami Duane "Keffe D" Davis da laifin kashe Tupac Shakur bayan kusan shekaru 30

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata kotu a Las Vegas, jihar Nevada ta Amurka, ta samu tsohon shugaban ƙungiyar 'yan daba Duane "Keffe D" Davis da laifin kashe shahararren mawaƙin rap Tupac Shakur, wanda aka harbe a shekarar 1996.

    Alƙalan kotun sun yanke hukuncin ne bayan shari’ar da ta ɗauki makonni ana sauraron shaidu da hujjoji.

    An same Davis mai shekara 63 da laifin kisan kai na matakin farko tare da amfani da makami.

    Masu gabatar da ƙara sun ce shi ne ya shirya harin da aka kai wa Tupac bayan wata arangama da ta haɗa mawakin da dan uwansa Orlando Anderson a daren da aka kashe shi.

    Tupac Shakur, ɗaya daga cikin fitattun mawaƙan hip-hop a duniya, ya samu raunuka ne yayin harbin da aka yi masa daga cikin wata mota a Las Vegas a ranar 7 ga Satumban 1996.

    Ya rasu kwanaki shida bayan harin yana da shekara 25 kacal, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce da hasashe tsawon shekaru da dama ba tare da an kama wani ba.

    An sake farfaɗo da binciken kisan ne bayan Davis ya bayyana wasu bayanai a cikin tarihin rayuwarsa da aka wallafa a shekarar 2019.

    Bayan hukuncin kotun, an bayyana cewa zai iya fuskantar ɗaurin rai da rai, yayin da ya ce zai ɗaukaka ƙara kan hukuncin.

  3. EFCC ta kori ma'aikata sama da 40 kan tafka cin hanci

    ...

    Asalin hoton, EFCC/X

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta ce ta kori ma'aikatanta sama da 40 cikin shekaru biyu da rabi da suka gabata saboda hannusu a cin hanci da sauran laifukan kuɗi.

    Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya ce fiye da mutum biyar daga cikin waɗanda aka kora na fuskantar shari'a a kotu, yayin da ake shirya gurfanar da wasu.

    Ya kuma bayyana cewa hukumar ta ƙaddamar da sabbin matakan tabbatar da gaskiya da riƙon amana a cikin ma'aikatanta, yana mai cewa EFCC ba za ta iya yaƙar cin hanci yadda ya kamata ba idan nata jami'an suna aikata irin wannan laifi.

    Haka kuma ya ce hukumar ta ƙwace sama da naira tiriliyan 1.23 da wasu manyan kuɗaɗen ƙasashen waje tsakanin Oktoban 2023 da Yunin 2026.

  4. Tinubu ya yaba da ceto 'yan bautar ƙasa da aka sace a Kogi

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya jinjinawa jami'an tsaro bayan ceto mutum 21 da aka sace a jihar Kogi, ciki har da mambobin bautar ƙasa 15.

    Shugaban ya ce haɗin gwiwar sojoji, 'yansanda, jami'an DSS da kuma masu sa-kai ne suka gudanar da aikin ceton, inda aka kuɓutar da waɗanda aka sacen daga maɓoyar masu garkuwa da mutane a dajin Ofu.

    Tinubu ya ce jami'an tsaro na ci gaba da farautar masu garkuwar, yana mai jaddada cewa duk wanda ke da hannu a lamarin zai fuskanci hukunci bisa doka.

    Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya.

  5. Za mu koma aiwatar da yarjejeniya idan har Amurka ta cika alƙawuranta - Iran

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya ce ƙasarsa za ta koma aiwatar da yarjejeniyar Islamabad nan take idan Amurka ta koma cika alƙawuran da ta ɗauka a ƙarƙashin yarjejeniyar.

    Yayin da yake jawabi a taron Ƙungiyar Haɗin Kan Shanghai, Pezeshkian ya ce Iran a shirye take ta mayar da martani iri ɗaya idan Washington ta mutunta yarjejeniyar.

    A wani ɓangaren kuma, rundunar sojin Iran ta sake gargaɗin ƙasashen yankin cewa za ta kai farmaki ga duk wata ƙasa da aka yi amfani da yankinta wajen kai mata hari.

    Rahotanni sun kuma ce an kai hari kan wani tankar ɗanyen mai a mashigar Hormuz, yayin da Sakataren Sojin Amurka Daniel Driscoll ya yi murabus bayan samun saɓani da Sakataren Tsaro Pete Hegseth.

  6. NAPTIP ta ceto sama da yara 180 da ake safararsu ta hanyar ƙungiyoyin fara hula na bogi

    ...

    Asalin hoton, NAPTIP/X

    Hukumar hana fataucin mutane ta Najeriya (NAPTIP) ta ce ta ceto yara sama da 180 da aka yi safararsu daga jihohin Kaduna, Anambra, Benue, Nasarawa da wasu wurare a ƙasar.

    Hukumar ta bayyana cewa wasu ƙungiyoyin masu fataucin yara na yaudarar iyaye ta hanyar bayyana kansu a matsayin ma'aikatan ƙungiyoyin farar hula masu tallafa wa yara da ilimi, sannan su tafi da yaran da sunan ba su ilimi da tallafi.

    A baya-bayan nan, an ceto wasu yara uku da aka kwaso daga Kajuru a jihar Kaduna a wani gini da ke Onitsha ta jihar Anambra, yayin da aka kuma gano wani yaro a hannun wata ma'aikaciyar lafiya.

    NAPTIP ta ce wasu daga cikin yaran da aka ceto an kai su gidajen marayu inda aka rika sayar da su ga mutane da sunan ɗaukar yara reno.

    Hukumar ta ce tana ci gaba da farautar masu hannu a wannan laifi domin gurfanar da su a gaban kuliya.

  7. Sojojin Yemen sun kai wa Houthi hari tare da lalata jiragen ruwansu marasa matuƙi

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Yemen sun ce sun kai hare-haren jiragen sama marasa matuƙa kan sansanonin mayaƙan Houthi a yankuna da dama, tare da kai farmaki kan maɓoyarsu da ke yankin Baqim a arewacin lardin Saada.

    A lokaci guda kuma, rundunar ruwan Yemen ta sanar da cewa ta lalata kwale-kwale huɗu marasa matuƙa na ƴan Houthi kusa da tsibiran Hanish da Dhaqr da ke Tekun Bahar Maliya.

  8. Amurka da waɗanda suka taimaka mata a harin Larak za su ɗanɗana kuɗarsu - Iran

    ....

    Asalin hoton, IRNA

    Iran ta yi gargaɗin cewa duk wata ƙasa ko ɓangaren da ya taimaka wajen kitsa ko ya goyi baya ko ya shiga cikin shirin harin da Amurka ta kai tsibirin Larak zai ɗanɗana kuɗarsa kuma za su ɗauki alhakin sakamakon da zai biyo baya.

    Iran ta ƙara da cewa za su kuma fuskanci martani mai tsanani kan abin da suka aikata.

    A wata wasiƙa da jakadan Iran a Majalisar Ɗinkin Duniya ya aike wa Sakatare Janar na MDD da Kwamitin Sulhu, ƙasar ta yi Allah wadai da harin tare da kira ga Amurka da ta daina abin da ta kira take haƙƙin ƙundin tsarin MDD da kuma matakan da ke barazana ga zirga-zirgar jiragen ruwa a Tekun Fasha da mashigar Hormuz.

    Haka kuma, rundunar sojin Iran ta yi gargaɗin cewa za ta mayar da martani kan duk wata ƙasa da aka yi amfani da yankinta wajen kai hare-hare kan Iran.

  9. Assalamu alaikum

    Shafin Kai Tsaye na BBC Hausa na marhaba da ɗumbin masu bibiyar mu a wannan rana ta Talata.

    Kamar kullum wannan shafi zai kawo muku labarai kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ce za ta kasance tare da ku a don haka sai ku ci gaba da kasancewa da mu.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.