WHO ta nuna damuwa kan bazuwar cutar Ebola a Congo

Asalin hoton, Jospin Mwisha / AFP via Getty Images
Hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta ce a duk lokacin da ta faɗaɗa bincikenta a kan ɓarkewar cutar Ebola a gabashin jamhuriyar Dumukuradiyyar Congo, sai ta gano shedar cewa lalle cutar ta bazu.
Wakilin BBC ya ce, wani kuma abin damuwa shi ne, a yanzu ta bazu zuwa yankin da ke da yawan jama'a sosai.
Hukumomin ƙasar ta Kongo sun ce a yanzu mutanen da cutar ta hallaka sun kai sama da 130 - kuma ana samun ƙaruwar mutanen da suka kamu da cutar.
To amma kuma gwamnatin ƙasar ta ce akwai jami'ai da ke aiki ba dare ba rana domin gano waɗanda ake ganin sun kamu ko sun yi mu'amala da waɗanda suka kamu.
Hukumar ta lafiya ta buƙaci jama'a da kada su firgita.
WHO, ɗin ta ce tana ƙoƙarin ganin ta daƙile bazuwar cutar ne ta hanyar taƙaita zirga-zirgar jama'a, da kuma faɗakar da mutane kan janaizar waɗanda suka rasu, ta hanyar da ta dace don gudun yaɗa cutar.








