Rufewa
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 28 ga watan Janairun 2026.
Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed, Aisha Babangida da Ahmad Bawage
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Ecuador ta yi alla-wadai da abin da ta bayyana a matsayin yunƙurin wani jami'in hukumar shige da fice na Amurka (ICE) na shiga ƙaramin ofishin jakadancin ƙasarta da ke Minneapolis.
Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Ecuador ta fitar ta ce jami'an ofishin jakadancin sun hana jami'in na ICE shiga ofishin, inda aka ce sun yi aiki ne "don tabbatar da kariya ga ƴan Ecuador da ke cikin ofishin jakadancin a lokacin".
Ecuador, wadda shugabanta abokin Trump ne, ta shigar da ƙara a hukumance.
A cikin wani faifan bidiyo da kafafen yaɗa labarai na Ecuador suka wallafa, wanda BBC ba ta tantance shi ba, ana iya ganin wani jami'in ofishin jakadanci ya garzaya zuwa kofar shiga yana cewa da jami'in na ICE "wannan ƙaramin ofishin jakadancin ne, ba a ba ku izinin shiga nan ba".
Shi kuma jami'in na ICE ya gaya wa jami'in cewa "idan ka taba ni, zan kama ka".
BBC ta tuntubi ma'aikatar tsaron cikin gida don jin ta bakinta, amma ya zuwa yanzu ba ta ce komai kan wannan batu ba.

Asalin hoton, Getty Images
Firaministan Birtaniya Sir Kier Starmer ya ce ana ci gaba da tattaunawa da Amurka kan yarjejeniyar miƙa tsibirin Chagos ga Mauritius, a daidai lokacin da ake fargabar cewa Amurka za ta janye goyon bayanta ga yarjejeniyar.
A ƙarƙashin yarjejeniyar, wadda Amurka ta goyi bayan a bara, Birtaniya za ta miƙa ikon mallakar tsibiran zuwa Mauritius tare da bayar da hayar wani sansanin soja na haɗin gwiwa tsakanin Birtaniya da Amurka a tsibirin mafi girma, Diego Garcia.
Ministoci sun dage cewa yarjejeniyar ya zama dole don kare sansanin daga "masu miyagun muradu", amma a makon da ya gabata Shugaba Trump ya bayyana yarjejeniyar a matsayin "wani babban wauta".
Jam'iyyar Conservatives mai adawa a Birtaniya dai na zargin gwamnatin ƙasar da yi wa tsaron ƙasa zagon ƙasa saboda alaƙar Mauritius da China.

Asalin hoton, Senator Kashim Shettima/X
Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Kashim Shettima, ya yi kira ga ƴan Najeriya da su rungumi haɗin-kai da kuma zaman lafiya, saboda haɗin-kai shi ne ginshikin cigaban ƙasa.
Shettima ya bayyana haka ne yau Laraba a Jos, babban birnin jihar Plateau, lokacin da ya kai wa shugaban majalisar sarakunan jihar, Jacob Gyang Buba ziyara.
A cewar mataimakin shugaban ƙasar, ɗimbin kabilu da ake da su a Najeriya ne ya sa dole a ƙarfafa haɗin-kai maimakon rarrabuwar kawuna.
"Dukkan mu akwai ta inda muke alaƙa da juna. Bai kamata a ce wani abu ya raba kan mu ba. Ba za a samu cigaba ba in dai babu zaman lafiya," in ji Shettima.
Mataimakin shugaban ƙasar wanda kuma ya je Plateau don bikin tarbar gwamnan jihar, Caleb Muftwang wanda ya koma jam'iyyar APC, ya yaba wa sarakunan gargajiya a jihar saboda koƙarinsu wajen tabbatar da kyakkyawan zaman lafiya a tsakanin al'umma.
Ya ce sarakunan gargajiyar na da rawar taka wa wajen daɓɓaka dorewar zaman lafiya a al'ummomi.

Asalin hoton, Getty Images
Ƙarin shugabanni biyu a Nahiyar Turai sun yi kira ga nahiyar ta ƙara ƙarfafa sojin ta, saboda ta rage dogaro da Amurka kan tsaro.
Firaministan Denmark Mette Frederiksen ta ce burin da aka sanya na ƙara kuɗaɗen da ake kashewa a fannin tsaro nan da 2035 na tafiyar hawainiya, inda ta ce a daidai wannan lokacin ne ake buƙatar inganta fannin tsaro.
Ita ma babbar jami'ar diflomasiyya ta ƙungiyar Tarayyar Turai Kaja Kallas ta shaida wa taron da aka yi kan tsaro a Brussels cewa alaƙarsu da Amurka ta raunana sosai.
Ta ce babu wata kasa da za ta dogara da kasashen waje kuma ta ci gaba da wanzuwa.

Asalin hoton, Getty Images
Aƙalla ƴansanda uku ne aka kashe sannan biyu suka jikkata a wani harin kwantan-ɓauna da ƴanbindiga suka kai jihar Katsina.
Lamarin ya faru ne ranar Talata, 27 ga watan Janairu, lokacin da ƴansanda ke aikin sintirin da suka suba yi a ƙauyen Guga da ke karamar hukumar Bakori na jihar ta Katsina.
Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa an kai harin da lokacin da jami'an ƴansanda suka je yankin domin daƙile wani hari da ɓata-gari suka yi niyyar kai wa, inda daga nan suka fara harbi kan mai uwa da wabi.
Kakakin ƴansandan jihar DSP Abubakar sadiq, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa, inda ya ce tuni aka garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti domin samun kulawa.
Ya ƙara da cewa an fara gudanar da bincike domin kama waɗanda suka kai harin, don hukunta su.

Asalin hoton, LasVegasAirportLive
An fara gudanar da bincike kan yadda ɗaya daga cikin tayar jirgin British Airways ta ɓalle ta faɗi ƙasa, jim kaɗan bayan tashi daga filin jirgin sama na Las Vegas.
An ɗauki yadda lamarin ya faru kai-tsaye, inda aka yi ta yaɗa bidiyon a kafofin sada zumunta.
Jirgin na Airbus A350 ya samu damar ci gaba da tafiya, kuma ya sauka ba tare da wata matsala ba a birnin Landan sa'o'i tara bayan faruwar lamarin.
Wata sanarwa da kamfanin jirgin ya fitar, ya ce yana mayar da hankali sosai kan kariya da kuma tsaro a dukkan ayyukansa - ya kuma ce zai bai wa hukumomi haɗin-kai a binciken su.

Asalin hoton, EPA
Shugaban Isra'ila Isaac Herzog ya ce sannu a hankali kasar za ta farfado daga tashin hankalin da ta fuskanta. Herzog na magana ne a wurin jana'izar mutumin da ya rage cikin wadanda suka mutu da Hamas ta yi garkuwa da su, bayan an dawo da gawarsa daga Gaza.
Ya kuma kara da bai wa iyalan Ran Gvili hakuri kan babban rashin da suka yi, da abin da ya kira mummunan tashin hakalin da suka fuskanta na jiran dawo da gawarsa zuwa gida.
A jawabin da ya yi, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya yi barazanar makiyan Isra'ila za su dandana kuɗarsu sosai.
Gvili dai ɗansanda ne da ya rasa ran shi lokacin bata-kashi da mayakan Hamas lokacin da suka kaddamar da farmaki a Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoban 2023.

Asalin hoton, Getty Images
An tabbatar da Dame Sarah Mullaly a matsayin shugabar cocin Ingila ta 106, a wani taron addu'a da aka yi a majami'ar St Paul da ke birnin Landan.
Ita ce mace ta farko da aka bai wa jagorar cocin Ingila. Ita ce kuma za ta jagoranci mabiya ɗarikar Anglican a fadin duniya, wanda ke da mabiya fiye da miliyan tamanin.
Sarah Mullaly kenan yayin da take shan rantsuwar kama aiki, inda ta yi alƙawarin kasancewa mai riƙon amana, da kuma biyayya ga mai martaba sarki Charles na uku.
Sai dai naɗin nata ya janyo ce-ce-kuce, musamman a wasu ƙasashen Afrika, inda mabiya ɗarikar Anglican na yankin ba su amince da mata a matsayin Limamai ba.

Asalin hoton, Reuters / Getty Images
Shugaba Trump ya ce lokaci na ƙurewa gwamnati Iran na hawa teburin tattaunawa. A cewar sa idan gwamnatin ta gaza hakan, ya yi gargaɗin cewa hari na gaba da zai kai mata, zai fi wanda da aka kai cibiyoyin nukiliyarta a watan Yunin bara muni.
Mista Trump ya ce wasu manyan jiragen ruwan yaƙi na tunkarar Iran, inda ya ce a shirye suke su kammala aikinsu cikin gaggawa, kamar yadda dakarun Amurka suka kai hari Venezuela.
Tun da farko dai ministan harkokin wajen Iran ya ce bai yi wata tattaunawa da Amurka ba a kwanakin baya bayan nan, kuma bai buƙaci a yi wata tattaunawa ba.
Sai dai Abbas Araqchi ya ce masu shiga tsakani da dama, waɗanda bai bayyana sunayensu ba, na neman shawarwari da kuma ganawa a Tehran.

Asalin hoton, NPF
Rundunar ƴansandan jihar Zamfara ta sanar da kama wani mutum bisa zargin mallakar abubuwan fashewa ba bisa ƙa’ida ba, a wani samame da aka kai a ranar 27 ga Janairu, 2027.
Samamen ya gudana ne da misalin ƙarfe 4:15 na yamma, bayan samun sahihin bayanan sirri da suka jagoranci jami’an tsaro zuwa kai farmaki cikin nasara.
A cewar sanarwar da rundunar ta fitar, "jami’anta na Task Force kan hana haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, ƙarƙashin jagorancin ASP Aminu Aliyu ne suka kama wanda ake zargin mai suna Mustapha Mohammad mai shekaru 38."
An kama shi ne yayin da yake tuƙin motar da binciken farko ya nuna cewa motar na ɗauke da abubuwan da ake zargin kayan fashewa ne 954 waɗanda aka ɓoye su a cikin buhunan robobi.
Rahotannin binciken sun nuna cewa ana zargin kayan an shirya amfani da su ne wajen ƙera ababen fashewa (IEDs) da ’yan bindiga ke amfani da su.
Rundunar ta ce "a halin yanzu wanda ake zargin yana tsare a hannun ’yan sanda, yayin da kayan da aka kama an adana su tare da miƙa su ga masu ƙwance abubuwan fashewa na rundunar domin ƙarin bincike da tantancewa.
Sanarwar ta ƙara da cewa bincike na ci gaba da gudana domin gano tushen kayan da inda aka nufa da su, da kuma gano sauran mutanen da ka iya kasancewa cikin wannan laifi.

Asalin hoton, Getty Images
Ɓarkewar zanga-zanga da kashe wasu daga cikin masu gangami, ya ƙara haifar da zaman ɗarɗar tsakanin Iran da Amurka, da fargabar ƙaddamar da hare-haren Amurka a ƙasar.
Fargabar ta ƙaru, musamman a makon nan, lokacin da Shugaba Trump ya ce ''wani makeken jirgin ruwan yaƙin ƙasarsa ya nufi Iran.'' Kodayake ya ce ba lallai a yi amfani da shi ba.
Kan wannan dalili ne sashen harshen Pashto na BBC ya bi diddigi tare da sanya idanu kan jirgin da motsinsa a yankin Gabas ta Tsakiya na tsawon makonni.
Jirgin mai suna ''USS Abraham Lincoln'' ya kasance ɗaya daga cikin jiragen ruwan Amurka da ya ɗauki hankali a ƴan makonnin nan.
Jirgi ne - mai amfani da makamashin nukiliya da ke ɗaukar jiragen sama - mallakin rundunar sojin ruwan Amurka, kuma ana kallon shi a matsayin ɗaya daga cikin manyan jiragen dakon kaya na zamani.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya ce ƙasarsa a shriye take ta taimakawa Najeriya wajen yaki da ta’addanci, yayin da ƙasar ke neman taimakon ƙasashen duniya don magance matsalolin tsaro da suka haɗa da ƙaruwar satar mutane a baya-bayan nan.
Erdogan ya yi wannan bayani ne a taron manema labarai tare da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, a birnin Ankara, inda ya ce "Turkiyya a shirye take ta raba ƙwarewar da take da ita a fannin tsaro da yaki da ta’addanci domin taimakawa Najeriya."
Tinubu ya bayyana cewa taimakon zai haɗa da "horon soji da na tattara bayanan sirri, da kuma ayyukan yaƙi da ta’addanci".
Shugabannin biyu sun tattauna kan bunƙasa haɗin gwiwar tattalin arziki, inda shugaba Erdogan ya ce Turkiyya za ta ƙulla kasuwancin dala biliyan 5 da Najeriya.
Bugu da ƙari, ƙasashen biyu sun sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi takwas a fannonin tsaro da ilimi da ci gaban al'umma da haɗin gwiwar ƙungiyoyi da sauransu.
A shekarar 2024, Najeriya ta sayi jiragen yaƙi marasa matuƙa 43 daga Turkiyya kuma ta tura sojoji 46 domin samun horo.
Ƴan Habasha da ke zaune a gundumar Mandera, dake arewa maso gabashin Kenya, sun bayyana cewa an gargaɗe su da cewa za a kashe su idan ba su bar wurin ba kafin ranar 5 ga Fabrairu, 2026.
Wasu daga cikin ƴan ci-ranin da ke zama a wurin sun bayyana wa BBC cewa halin da suke ciki na iya zama haɗari ga rayukansu.
Wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa sun ce suna fuskantar barazanar kai hari, kuma suna cikin tsananin tashin hankali da rashin tsaro a yankin.
Jakadancin Ethiopia a Kenya ya tabbatar da cewa yana bin lamarin sosai, kuma yana tuntubar hukumomin Kenya domin tabbatar da cewa ‘yan kasar suna samun kariya.
Masu sharhi kan harkokin tsaro sun ce wannan lamari na iya ƙara tsananta rikicin da ke tsakanin al’ummomi a iyakokin Kenya da Ethiopia, musamman a yankunan da ake fama da rashin tsaro da tashe-tashen hankula.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban mulki sojin Sudan, Lt Janar Abdel Fattah al-Burhan ya gana da sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad al-Thani a Doha, inda shugabannin biyu suka tattauna kan dangantakar ƙasashen biyu da kuma ƙoƙarin duniya na kawo zaman lafiya a Sudan, kamar yadda jaridar gwamnatin ƙasar Suna ta ruwaito.
"Ganawar ta duba ci gaban dangantakar ƙasashen biyu a fannoni daban-daban da kuma abubuwan da ke faruwa a Sudan da ƙoƙarin duniya na tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali da zaman lafiya a Sudan." in ji Suna.
Haka kuma, an ruwaito cewa Janar Burhan ya yaba da goyon bayan da Qatar ke bai wa Sudan, sannan ya tabbatar da kudurin Khartoum na ƙarfafa haɗin gwiwa bisa dogon tarihi na dangantakar ƙasashen biyu.
Ziyarar Burhan zuwa Qatar na cikin rangadin kasashen waje da ya fara ƙarshen shekarar da ta gabata, wanda ya haɗa da ziyara a Masar, Saudiya, da Turkiyya.
Haka kuma rangadin yana da nufin samun kayan yaƙi ga sojojin Sudan yayin da suke ci gaba da fafatawa da dakarun RSF a manyan sassan yankunan Kordofan da Darfur.

Asalin hoton, Abdullahi Ganduje/X
Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa a shirye yake ya shirya da babban abokin siyasarsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Ganduje ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da BBC.
Ya ce, “Ina fatan nan gaba za mu daidaita da Kwankwaso, a tafi ga baki ɗaya domin harka ce ta siyasa. Da munyi siyasa tare da shi, mu ‘yan uwan juna ne."
Ganduje da Kwankwaso dai sun jima ba sa ga maciji da juna a harkokin siyasar jihar Kano, kuma ana ganin komawar da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf yayi zuwa jam’iyyar APC zai sake ruruta ƙiyayyar da ke tsakaninsu.
Ganduje ya ce abin da yanzu ya fi muhimmanci shi ne ci gaban al’ummar Kano da kuma nasarar jam’iyyar APC.
“Da anyi hamayya, yanzu ana tare. Wance shafi na hamayya an riga an rufe shi. Abin da aka sa a gaba shine ci gaban al’ummar Kano da samun nasara a wannan jam’iyya,” in ji shi.
Ya kara da cewa, “Idan Abba ya samu nasara, mun samu; in mun samu nasara, ya samu; idan ya faɗi, mun fadi; idan mun fadi, ya fadi. Duk wanda ya gane wannan, magana ce ta mu taimaka wannan gwamnati tayi nasara.”
Ganduje ya bayyana cewa kasancewarsa tsohon shugaban jam’iyyar APC na tsawon shekara biyu ya ba shi damar fahimtar tsarin jam’iyya da yadda ake tafiyar da al’amuranta.
“A kan batun ko za a ba Abba dama ya tsaya takara a jam'iyyar, na san abun da yaka a tsarin mulki da kuma abin da yake na al'ada na jam'iyyar. Al’ada ta jam’iyyar APC shine wanda yake gwamna, shi za a fara ba shi tayi idan yana sha’awa ya tsaya takara domin ya maimaita ko yayi tazarce, amma ba yana nufin duk sauran muƙame haka bane,” Ganduje ya ƙara da cewa.
Ganduje ya jaddada cewa hadin kai tsakanin shugabannin jam’iyya da ‘yan siyasa zai taimaka wajen samun nasara a jihar Kano.

Asalin hoton, X/NEMA
Najeriya ta karɓi ƴan gudun hijirar ƙasar 153 daga Jamhuriyar Nijar a wani yunkuri na tabbatar da dawowarsu cikin aminci da daraja.
Ofishin hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA reshen Kano ne ya karɓi waɗannan ƴan gudun hijira tare da haɗin gwiwar Hukumar ƴan gudun hijira ta ƙasa NRC da hukumar ba da agajin gaggawa ta SEMA, da rundunar tsaro ta NSCDC.
Ƴan gudun hijirar sun isa filin jirgin saman Malam Aminu Kano da misalin ƙarfe 12:50 na tsakar daren Talata ta jirgin Sky Mali Airline.
Bayan kammala rajista da hukumar shige da fice ta Najeriya NIS, an kai su makarantar horarwar hukumar domin gudanar da cikakken bincike da tantancesu tare da dukkan masu ruwa da tsaki.
An gudanar da tantancewar a ranar 27 ga Janairu, 2026, inda bayanan ƴan gudun hijirar suka nuna cewa akwai maza manya 46, mata manya 37, yara maza 38 da kuma yara mata 32.
Hadin gwiwar duk masu ruwa da tsaki ya tabbatar da cewa aikin tantancewa ya gudana cikin tsari, nasara, kuma ba tare da wani matsala mai hatsari ba.

Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Nyesom Wike, ya gargaɗi ma’aikatan birnin tarrayar da ke yajin aiki da cewa duk wanda ya bijirewa umarnin kotu ya ƙi komawa bakin aiki daga ranar Laraba, 28 ga Janairu, zai fuskanci ladabtarwa.
Wike ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake ganawa da manema labarai a ofishinsa da ke Abuja, jim kaɗan bayan kotun warware matsalolin ƴan ƙwadago da ke birnin ta umarci ma’aikatan da su dakatar da yajin aikin da suke yi.
Ya ce, “Daga gobe duk wanda bai koma aiki ba, za mu yi amfani da tsauraran matakai. Kuma daga gobe idan muka ga wani yana ƙoƙarin toshe ƙofa, za mu yi amfani da shi a matsayin misali. Dole ne doka ta yi aikinta.”
Ministan ya bayyana cewa gwamnatinsa ta riga ta gana da ƙungiyoyin ƙwadago, inda aka tattauna dukkan ƙorafe-ƙorafensu amma hakan bai haifar da ɗa mai ido ba.
“Ina nufin idan ma’aikata sun gabatar da buƙatu 14, gwamnati ta magance 10 daga ciki, to mene ne kuma matsalar?” in ji Wike.
Ma'aikatan dai sun shiga yajin aikin ne tun daga makon da ya gabata inda suka buƙaci gwamnatin tarayya ta kyautata yanayin aikinsui da alawu-alawus din su.
Yajin aikin ya jawo tsaiko da rufe ayyuka a manyan ofisoshin gwamnati da dama a Abuja.
Biyo bayan hakan ne Wike ya shigar da ƙara a gaban koun warware matsalolin ƴan ƙwadago dangane da yajin aikin inda ta umarci ma’aikatan da su dakatar da yajin aikin.

Asalin hoton, Anadolu via Getty Images
Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya bayyana cewa ƙasarsa na da burin ƙara yawan cinikayya da Najeriya zuwa dala biliyan 5, daga dala biliyan 2.
Shugaba Erdogan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a birnin Ankara, yayin taron manema labarai na haɗin gwiwa da Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, a ziyarar aiki da Tinubu ya kai ƙasar.
Erdogan ya ce tuni aka fara tattaunawa domin cimma wannan buri, inda ya bayyana cewa Turkiyya na fitar da jiragen sama da jirage masu saukar ungulu da injuna da ƙarafa da sinadarai zuwa Najeriya, yayin da Najeriya kuma ke fitar da ɗanyen mai da kayayyakin gona zuwa Turkiyya.
Ya ce "ƙasashen biyu sun tattauna batutuwa da suka shafi cinikayya da zuba jari da makamashi da ilimi da masana’antar tsaro, tare da nuna fatan haɗin gwiwa tsakanin kamfanin man fetur na Turkiyya da na Najeriya zai haifar da sakamako mai kyau."
Erdogan ya kuma yi alkawarin tallafa wa Najeriya a yaƙin da take yi da ta’addanci, musamman ganin yadda matsalar ta’addanci ke barazana ga yankin Sahel da nahiyar Afirka baki ɗaya.
Ya ce "Turkiyya a shirye take ta raba ƙwarewarta a fannin horon sojoji da tattara bayanan sirri."
A nasa jawabin, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gode wa Turkiyya bisa shirinta na haɗin gwiwa da Najeriya domin bunƙasa ‘yanci da zaman lafiya da wadata a duniya.
Ƙasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyi tara, ciki har da na tsaro da na cinikayya da ilimi da kafofin watsa labarai da harkokin mata da jinƙai, domin ƙarfafa dangantaka tsakanin Najeriya da Turkiyya.

Asalin hoton, Kwankwaso/X
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa kuma jagoran jam'iyyar NNPP a Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce yana da yaƙinin cewa sai gwamnan Kano Abba Kabir da muƙarrabansa sun yi da na sanin fita daga jam'iyyar NNPP da suka yi.
Sanata Kwankwaso ya ce fitar gwamna Abba daga jam'iyyar NNPP ta zo da mamaki ga mutane da dama, kuma shi da kansa jin abin yake kamar a mafarki.
''Da yawa mutane ina da labarin, gani suke ma kamar wani tsari ne, da ni da shi, ko da ni da su. Nima sau da yawa ba na yarda cewar abubuwab da suke faruwa haka su ke.'' in ji Kwankwaso.
A ranar Litinin 26 ga watan Janairun 2026 gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya komawa jam'iyyar APC a hukumance, bayan sanar da ficewar sa daga NNPP a ranar Juma'a 23 ga watan Janairun 2023, ƙasa da shekara uku bayan cin zaɓen gwamnan Kano a cikin ta.