Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce Washington na iya sake ɗaukar matakin soja kan Iran, kusan watanni takwas bayan fara yaƙin Amurka da Isra’ila da Iran, a daidai lokacin da hauhawar farashin mai ke ƙara tayar da hankali gabanin zaɓen tsakiyar wa’adin majalisar dokokin Amurka.
A wani gangamin yaƙin neman zaɓe da ya yi a jihar Florida ranar Juma’a, 23 ga Oktoba, Trump ya ce:
“Mai yiyuwa ne mu sake gudanar da wani ƙaramin farmaki, ko kuma su amince da yarjejeniya.”
Ya ƙara da cewa: “Da ace suna da basira, da kawai za su ce, ‘Mu shiga tattaunawa ta gaskiya.’ Amma ina shakka za su yi hakan, domin wataƙila ba su da wannan hikimar.”
“Operation Epic Fury” shi ne sunan da sojojin Amurka ke amfani da shi wajen kiran yaƙin da suke yi da Iran.
A cikin jawabin nasa, Trump ya sake kare matakin da gwamnatinsa ta ɗauka na ficewa daga yarjejeniyar nukiliya ta JCPOA a lokacin wa’adinsa na farko. Ya yi iƙirarin cewa Amurka ta lalata ƙarfin Iran na tace sinadarin uranium ta hanyar farmakin “Operation Midnight Hammer”, sannan ta ci gaba da yi mata ƙarin illa ta hanyar “Operation Epic Fury.”
Har ila yau, ya ce Amurka ta yi wa Iran mummunar illa, yana mai ikirarin cewa tattalin arzikin ƙasar na cikin mawuyacin hali fiye da kowane lokaci.
Tun da farko a ranar Juma’a, shugaban na Amurka ya ce ƙasarsa na da ikon kawo ƙarshen yaƙin da Iran cikin sauri, amma ya yi tambaya kan ko ya dace Washington ta nemi kawo ƙarshen rikicin cikin gaggawa ko kuma ta bari ya lafa a hankali.
Trump, wanda ya sha bayyana manufofi da lokuta daban-daban kan yadda za a kawo ƙarshen yaƙin, ya sanar a farkon watan Oktoba cewa Amurka ba za ta sake kai wani hari kan Iran ba kafin zaɓen tsakiyar wa’adin majalisar dokoki da za a gudanar a ranar 3 ga Nuwamba.