KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 24/10/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 24/10/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed

  1. Amurka ta ayyana cibiyoyin al'adun Sin a matsayin barazana ga tsaron ƙasar

    Amurka

    Ma'aikatar Tsaron Amurka ta ayyana cibiyoyin koyar da harshe da al'adun kasar Sin a matsayin barazana ga tsaron ƙasar.

    Cikin wani faifan bidiyo da aka wallafa a kafafen sada zumunta, Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya kwatanta cibiyoyin da a matsayin masu yada farfaganda.

    Ya ce irin waɗannan cibiyoyi da dama sun ɓulla a jami'o'in Amurka da sunaye daban-daban, yana mai zarginsu da ƙoƙarin satar fasahohi da bayanan ilimi, tare da abin da ya bayyana a matsayin ƙoƙarin yin tasiri a tunanin ɗaliban Amurka.

    Mista Hegseth ya ce ma'aikatarsa ta rushe irin waɗannan cibiyoyi da dama. Har yanzu ofishin jakadancin China da ke Washington bai fitar da wata sanarwa kan batun ba.

  2. Taƙaddama kan yaƙin Iran na jan hankali a shirin zaɓen Isra'ila

    Isra'ila

    Yaƙin neman zaɓe a Isra'ila ya shiga wani gagarumin mataki, inda ake fafatawa mai zafi tsakanin manyan ƴan takara biyu: Firaminista mai ci Benjamin Netanyahu da kuma shugaban jam'iyyar adawa ta Yashar, Gadi Eisenkot.

    Sauran ƴan siyasa ma na ta ƙoƙarin samun ƙarin kuri'u da kuma tasiri wajen kafa gwamnati ta gaba.

    Yanayin siyasar ya yi zafi matuƙa har wani ɗan jarida na cikin gida ya kwatanta gasar da "wanka da jini". Wato, kowane ɓangaren siyasa ya fito fili yana ƙalubalantar ɗayan a wannan fafatawa.

    Sai dai abin lura shi ne, kusan dukkan ƴan takarar suna da abokin gaba guda ɗaya, wato Iran. Ɗaya daga cikin manyan tambayoyin da ake yi wa dukkan masu neman shugabanci a wannan zaɓe ita ce: me za ku yi game da Iran?

    Amsar da mafi yawansu ke bayarwa kusan iri ɗaya ce: "Za mu ci gaba da fuskantar Iran, amma ta hanyar da muka yi imani ta fi dacewa."

    Sai dai duk da wannan matsaya ta bai ɗaya, hanyoyin da kowane bangare ke son bi wajen mu'amala da Iran suna cike da bambance-bambance da kuma muhawara mai yawa. Wasu na goyon bayan ƙarin matsin lamba ta soja, yayin da wasu ke ganin ya kamata a haɗa hakan da dabarun diflomasiyya da na siyasa.

  3. Saudiyya ta ce ta kakkaɓo makamai masu linzami da Houthi ta harba

    Ƙawancen ƙasashen Larabawa da Saudiyya ke jagoranta ya sanar da cewa ya lalata makamai masu linzami masu cin dogon zango guda biyu da mayaƙan Houthi suka harba zuwa biranen Taif da Yanbu a ranar Asabar, yayin da rikici ke ci gaba tsakanin ɓangarorin biyu.

    Hukumar Kare Fararen Hula ta Saudiyya ta fitar da gargadi a ranar Asabar, tana sanar da yiwuwar barazana a biranen Taif da Yanbu, da kuma Makka da Jidda.

    Sai dai kusan mintuna 10 bayan haka, hukumar ta fitar da wata sanarwa tana cewa an shawo kan barazanar, kuma lamarin ya koma daidai.

  4. Zaɓen shugaban ƙasar Brazil na ƙara ɗaukar zafi

    Sebastião Moreira EPA

    A muhawarar talabijin ta ƙarshe gabanin zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasar Brazil da za a gudanar a ƙarshen wannan makon, shugaban ƙasar Luiz Inácio Lula da Silva da babban abokin hamayyarsa mai ra'ayin ƴan mazan jiya, Sanata Flávio Bolsonaro, sun yi musayar yawu kan manufofinsu.

    Lula, wanda tsohon jagora ne mai sassaucin ra'ayi, ya kare nasarorin gwamnatinsa musamman kan harkokin tattalin arziki.

    Shi kuwa Flávio Bolsonaro, ɗan tsohon shugaban ƙasar Jair Bolsonaro da ake tsare da shi, ke yakin neman zaɓe kan batutuwan tsaro da tabbatar da doka da oda.

    Zaɓen na wannan karon ya sake haifar da rarrabuwar kawunan siyasa da aka jima ba a a gani ba a cikin shekaru huɗu da suka gabata, wato lokacin da Lula ya yi nasara, lamarin da ya haifar da suka daga magoya bayan Bolsonaro.

  5. Birtaniya za ta kasafta fam miliyan 220 domin ƙarfafa tsaron AI

    Birtaniya

    Gwamnatin Birtaniya ta sanar da cewa za ta ware kusan dala miliyan 300, kwatankwacin fam miliyan 220, domin ƙarfafa tsaron ƙirƙirarriyar basira ta AI, a cikin kasafin kuɗinta na shekara da za a gabatar a ranar Laraba mai zuwa.

    Kimanin rabin kuɗin za a yi amfani da su wajen kafa dakin gwaje-gwaje na farko a duniya da zai mayar da hankali kan tsaron halittu ta amfani da AI, domin ƙarfafa kariya daga yiwuwar barazanar da ke da alaƙa da ƙwayoyin halitta.

    Sauran kuɗaɗen kuwa za su tafi ga Cibiyar Tsaron AI ta Birtaniya, wadda ke gwada manyan nau'ikan tsarin AI kafin a fitar da su don amfani.

    A baya-bayan nan an samu karuwar damuwa kan barazanar kutse ta intanet da kuma haɗurran da ci gaban fasahar AI cikin sauri ka iya haifarwa.

  6. Cutar Ebola da aka gano a Najeriya na kama da wadda ta ɓarke a Kenya

    Ebola

    Ministan Lafiya na Najeriya, Muhammad Ali Pate, ya ce binciken ƙwayoyin halittar wadda aka tabbatar tana ɗauke da cutar Ebola a Najeriya ya nuna cewa ƙwayar cutar tana da kamanceceniya sosai da nau’in cutar da aka gano a mutum na farko da ya kamu da ita a Kenya.

    Wannan shi ne karo na farko da aka samu wata hujjar kimiyya da ke nuna alaƙa tsakanin ɓarkewar cutar a ƙasashen biyu.

    Sai dai hukumomin Najeriya sun ce babu wata shaida da ke nuna cewa mutumin farko da ya kamu da Ebola a Kenya ya taɓa zuwa Najeriya ko kuma yana da wata alaƙa kai tsaye da wanda aka gano da cutar a Najeriya.

    Minista Pate ya ce hukumomi na ci gaba da gano da bibiyar duk waɗanda suka yi hulɗa da wanda ya kamu da cutar, inda ake killace su tare da yi musu gwaji. Ya ce wasu daga cikin sakamakon gwaje-gwajen sun fito babu cutar, yayin da ake jiran sakamakon wasu.

    Najeriya dai ta tabbatar da mutum guda kacal da ya kamu da Ebola, wanda rahotanni suka ce ya yi tafiya zuwa ƙasar Uganda kafin a gano yana ɗauke da cutar.

  7. Faransa na fuskantar wata sabuwar zanga-zangar tsadar rayuwa

    Faransa

    Faransa na fuskantar wata sabuwar zanga-zanga kan tsadar rayuwa da kuma taɓarɓarewar ilimi a makarantu, yayin da ake fargabar sake aukuwar tashe-tashen hankula da fashe fashen shaguna irin na karshen makon da ya gabata.

    Gwamnatin kasar ta ce za ta girke jami’an ƴansanda dubu 70 a fadin kasar, tare da alkawarin gaggauta daukar mataki idan aka samu wata alamar tarzoma.

    A birnin Paris, masu shaguna sun rufe ko kuma sun kare wuraren kasuwancinsu domin dakile yiwuwar barna. Garin Orleans, da ke kudancin Paris, na daga cikin wuraren da ake da matukar damuwa akansu.

    Jam’iyyar National Rally mai ra’ayin rikau, na gudanar da taronta na shekara-shekara a garin, inda ake sa ran shugabarta, Marine Le Pen, za ta sanar a hukumance aniyarta ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekara mai zuwa. break

  8. Wataƙila mu sake ƙaddamar da hari a Iran - Trump

    Amurka

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce Washington na iya sake ɗaukar matakin soja kan Iran, kusan watanni takwas bayan fara yaƙin Amurka da Isra’ila da Iran, a daidai lokacin da hauhawar farashin mai ke ƙara tayar da hankali gabanin zaɓen tsakiyar wa’adin majalisar dokokin Amurka.

    A wani gangamin yaƙin neman zaɓe da ya yi a jihar Florida ranar Juma’a, 23 ga Oktoba, Trump ya ce:

    “Mai yiyuwa ne mu sake gudanar da wani ƙaramin farmaki, ko kuma su amince da yarjejeniya.”

    Ya ƙara da cewa: “Da ace suna da basira, da kawai za su ce, ‘Mu shiga tattaunawa ta gaskiya.’ Amma ina shakka za su yi hakan, domin wataƙila ba su da wannan hikimar.”

    “Operation Epic Fury” shi ne sunan da sojojin Amurka ke amfani da shi wajen kiran yaƙin da suke yi da Iran.

    A cikin jawabin nasa, Trump ya sake kare matakin da gwamnatinsa ta ɗauka na ficewa daga yarjejeniyar nukiliya ta JCPOA a lokacin wa’adinsa na farko. Ya yi iƙirarin cewa Amurka ta lalata ƙarfin Iran na tace sinadarin uranium ta hanyar farmakin “Operation Midnight Hammer”, sannan ta ci gaba da yi mata ƙarin illa ta hanyar “Operation Epic Fury.”

    Har ila yau, ya ce Amurka ta yi wa Iran mummunar illa, yana mai ikirarin cewa tattalin arzikin ƙasar na cikin mawuyacin hali fiye da kowane lokaci.

    Tun da farko a ranar Juma’a, shugaban na Amurka ya ce ƙasarsa na da ikon kawo ƙarshen yaƙin da Iran cikin sauri, amma ya yi tambaya kan ko ya dace Washington ta nemi kawo ƙarshen rikicin cikin gaggawa ko kuma ta bari ya lafa a hankali.

    Trump, wanda ya sha bayyana manufofi da lokuta daban-daban kan yadda za a kawo ƙarshen yaƙin, ya sanar a farkon watan Oktoba cewa Amurka ba za ta sake kai wani hari kan Iran ba kafin zaɓen tsakiyar wa’adin majalisar dokoki da za a gudanar a ranar 3 ga Nuwamba.

  9. Farawa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar, inda za mu cigaba da kawo muku labarai da rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Kuna iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta