Fatan Iran na kaiwa zagaye na biyu a Gasar Cin Kofin Duniya karo na farko a tarihi ya ƙare ranar Asabar, bayan da Austria ta farke ƙwallon da Algeria ya zura mata a raga daf a tashi suka tashi 3-3 a karawar cikin rukuni, wanda ya sa Iran ta kasa shiga cikin tawaga takwas mafi samun maki mai kyau.
Tawagar da Amir Ghalenoei ke jan ragama ta kammala wasanninta na rukuni na bakwai a ranar Juma’a da canjaras 1-1 da Masar, lamarin da ya sa ta jira sakamakon karawar Algeria da Austria, domin ganin ko maki uku za su isa su ba ta damar kaiwa zagayen ƴan 32.
Tuni Iran ta fuskanci babbar koma baya lokacin da aka soke kwallon da zura a kan Masar, saboda batun satar gida.
Hakan ya sa suka dogara da sakamakon sauran wasannin rukuni da fatan samu dama. A ranar ta Asabar, ya zama kamar Iran za ta tsallaka zagayen gaba a gasar kofin duniya, lokacin da Algeria ta zura kwallo a ƙarin lokaci ta kai ga cin Austria 3-2.
Sai dai Austriah ta samu damar farke kwallo daf a tashi da karawar ta koma 3-3, hakan ya bai wa tawagar biyu kai wa zagayen ƴan 32, yayin da Iran ta yi ban kwana da wasannin.
Iran ta bar gasar ba tare da rashin nasara ba, bayan kunnen doki da Belgium da New Zealand da kuma Masar a fafatawar da ta ci karo da ƙalubale saboda matsaloli da ya shafi sabani tsakaninta da Amurka.
Rashin tabbas kan batun visa da rikicin da ke tsakanin Iran da Amurka ya tilastawa kasar yin zirga-zirga daga sansaninsu da ke Mexico (ɗaya daga masu karɓar baƙuncin gasar) zuwa wasanninta uku na rukuni da aka buga a Amurka.