Ƙasashen da aka fitar da su daga Gasar Kofin Duniya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 8

Zuwa yanzu an fara fitar da tawagar wasanni ƙasashe daga Gasar Kofin Duniya ta 2026 da ke gudana a Amurka da Mexico da Kanada.

Ƙasashe 48 ne ke fafatawa a gasar, inda kowa ke neman tikitin zuwa zagayen gaba na kifa ɗaya ƙwala ta hanyar samun maki a wasannin rukuni.

Ga jerin ƙasashen da aka cire bayan da aka kammala wasannin matakin rukuni a gasar.

Tunisia

An cire Tunisia daga gasar ne bayan da Japan ta doke ta da ci 4-0 a wasan da suka buga a Monterrey ranar Lahadi.

Tun da farko Tunisia ta sha kashi da ci 5-1 a hannun Sweden a wasan farko na rukuni na F.

Tun a wasansu na farko ne dai aka kori kocin su Sabri Lamouchi, inda aka naɗa Hervé Renard da tunanin za su ga sauyi.

Sai dai da alama daga nan za su yi bankwana da gasar Kofin Duniya na 2026.

Sakamakon rashin samun ko maki ɗaya a wasanninta biyu na farko ya tabbatar da cewa ba za ta iya kaiwa zagayen ƴan 32 ba, duk da cewa akwai wasa guda ya rage mata a matakin rukuni.

Haiti

A rukuni na C kuwa, zakarun duniya sau biyar Brazil sun lallasa Haiti da ci 3-0 a birnin Philadelphia.

Wannan sakamako ya tabbatar da ficewar Haiti daga gasar bayan da ta kasa samun ko maki ɗaya a wasanni biyu.

A wasansu na farko dai Scotland ce ta ci su 1-0.

Ƙasar ce take ƙarshen teburin rukuni da bambancin ƙwallaye, lamarin da ya sa wasanta na ƙarshe da Morocco a ranar 24 ga Yuni zai zama wasan cike gurbi ne kawai.

Turkiya

A rukuni na D kuma, Türkiye ta yi rashin nasara da ci 1-0 a hannun Paraguay a wasan da aka buga a filin wasa na San Francisco Bay Area Stadium.

Shan kashi sau biyu a jere ba tare da samun maki ba, lamarin da ya tabbatar da ficewar ƙasar daga gasar tun kafin ta buga wasanta na ƙarshe a rukuni.

Turkiya ta sha kashi a hannun Australia da ci 2-0 a wasansu na farko.

Wasan da ya rage mata na ƙarshe shi ne wanda za ta fafata da Amurka.

Jordan

A Rukunin J Algeria ta doke Jordan da ci 2-1 a wasansu da aka fafata a filin wasan San Francisco Bay inda suka fitar da ita daga gasar cin kofin duniya.

A baya bayan nan ta sha kashi a hannun Austria da ci 3-1 a wasan farko na gasar, kuma wannan sakamakon ya sa sun kasance a kasan rukunin inda ba su da maki ko ɗaya bayan wasanni biyu, wanda hakan ke nufin ba za su iya tsallakewa zuwa zagaye na gaba ba.

Yanzu a wasan ta na gaba za ta kara ne da Argentina mai riƙe da kambun gasar, wanda ita ke jan ragamar rukunin kuma ta riga ta tsallaka zuwa zagaye na gaba a gasar.

Panama

A rukunin L an yi waje da Panama daga gasar bayan da Croatia ta ci gaba da yunƙurinta na tsallakawa zuwa zagaye na ƴan 32 inda ta doke ta da ci 1-0 a ranar Talata a filin wasan birnin Toronto.

Wannan rashin nasara shi ne karo na biyu a jere da Panama ta sha kashi a matakin rukuni na wannan gasar kuma ya tabbatar da cewa ba za ta iya tsallakewa zuwa zagayen gaba ba bayan ta sha kashi da ci ɗaya mai ban haushi a hannun Ghana a wasanta na farko a rukunin.

Panama har yanzu tana neman makin ta na farko, bayan buga wasanni biyar a tarihin gasar cin kofin duniya.

A ranar Juma'a ne za ta kara da Ingila a wasan ta na ƙarshe a gasar bana.

Czechia

An yi waje da Czechia daga gasar ne bayan ta sha kashi a hannun mai masaukin baƙi Mexico da ci 3-0 a wasanta na ƙarshe na rukunin A a Estadio Ciudad de Mexico.

Czechia ta gaza taɓuka wani abin kirki a matakin rukuni na gasar, inda ta ƙare a matsayi na ƙarshe a rukuninta da maki ɗaya kacal inda ta yi kunnen doki a wasa guda, abin da ke nufin ta kasa samun gurbi a zagaye na 32.

Mexico ce ta ja ragamar rukunin da maki tara yayin da Afrika ta hudu ta bi ta a baya da maki huɗu sai kuma Koriya ta kudu da ke da maki uku ta ke matsayi na uku.

Qatar

An cire Qatar daga gasar ne bayan ta yi rashin nasara a wasanta na ƙarshe da Bosnia-Herzegovina, inda aka doke ta da ci 3 -1 a wasan da aka buga a filin wasan Seatle.

Yayin da Qatar ta yi waje bayan ta ƙare a matsayi na ƙarshe a rukunin B a zuwan ta na biyu gasar cin kofin duniya, Bosnia-Herzegovina - idan aka tabbatar da ita a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashe takwas mafi ƙoƙari a matsayi na uku a cikin rukunoni - za su iya karawa da Amurka mai masaukin baƙi a ranar Alhamis, 1 ga Yuli ko Jamus a ranar Litinin, 29 ga Yuni a zagayen ƴan 32.

Curacao

Curacao, wadda ita ce ƙasa ce mafi ƙanƙanta ta ɓangaren yawan al'umma da ta taɓa taka leda a gasar cin kofin duniya ta maza, an fitar da ita daga gasar bayan da ta yi rashin nasara a wasanta na ƙarshe a rukunin E inda ta sha kashi 2-0 a hannun Ivory Coast wadda ta ƙetara zuwa zagaye na biyu na gasar a karon farko a cikin tarihinta.

Hakan na nufin Ivory Coast ta zo ta biyu a rukunin da maki shida, inda ta lashe wasanni biyu a gasar cin kofin duniya a karon farko.

Ivory Coast za ta kara da ta biyu daga rukunin I - wadda za ta zama ko Faransa ko kuma Norway - a Arlington, Texas a ranar 30 ga watan Yuni a zagaye na biyu.

Curacao ta ƙare a ƙasan rukunin E da maki ɗaya daga wasanni uku sakamakon haka ta kama hanyar tafiya gida.

Iran

Iran ta kasa kai labari a gasar bana ne bayan da ta yi canjaras a duka wasanninta uku na rukunin G.

Bayan ta yi canjaras a wasanni biyu na farko da ta kara da New Zealand da Belgium, Iran ta san da cewa sai ta yi nasara a wasanta na ƙarshe da Masar a Seattle kafin ta iya tsallakawa zuwa zagaye na gaba.

Wasan ya ƙare ci 1-1sakamakon da ke nufin sai da Iran ta jira aka kammala duka wasannin rukuni kafin ta san makomarta a gasar.

Algeria da Australia shi ne wasa mafi mahimmanci a gare ta, kuma da aka tashi ci 2-2 hakan ya sa Iran ta kasa kai labarai a matsayin ɗaya daga cikin tawagogi 8 mafi ƙwazo da suka zo na uku a rukuninsu

Koriya ta Kudu

Koriya ta kudu ta fice daga gasar ne bayan ta yi rashin nasara a wasa biyu cikin guda uku da ta fafata a rukunin A.

Wssanta na ƙarshe da ya tabbatar da ficewarta a gasar shi ne rashin nasara da ta yi da ci 1-0 a hannun Afrika ta kudu.

A wasanta na farko a rukunin Koriya ta yi nasara kan Czechia da ci 2-1 kafin ta sha kashi a hannu Mexixo mai masaukin baƙi da ci 1-0, hakan ya sa ta ƙare a matsayi na uku da maki uku a cikin rukunin.

Scotland

Scotland ta kasance a rukunin C inda ta fafata da Brazil da Morocco da kuma Haiti.

Ta ƙare ne a mataki na uku a rukunin bayan ta yi nasara a wasa ɗaya inda ta doke Haiti da ci 1-0. Amma ta yi rashin nasara a sauran wasanninta biyu inda ta sha kashi a hannun Morocco da ci 1-0 sai kuma Brazil ta lallasa ta da ci 3-0.

Wannan dai shi ne karo na tara da ƙasar ta samu gurbin wasa a gasar cin kofin duniya, amma ba ta taɓa ƙetarawa zuwa zagaye na biyu ba a tarihinta.

Uruguay

Uruguay ta tsinci kanta ne a rukunin H inda ta kece raini da Spain da Cape verde da kuma Saudiyya.

Ta fice daga gasar ne bayan ta kasa lashe ko wasa ɗaya a rukunin, inda ta yi kunen doki 1-1 da Saudiyya ta kuma sake yin canjaras 2-2 da Cape verde sai kuma ta sha kashi a hannun Spain da ci 1-0, sakamakon da ya sa ta ƙare a mataki na uku a rukunin da maki biyu kacal.

Uzbekistan

Uzbekistan ce ƙasa ɗaya tilo da aka yi waje da ita a rukunin K, wanda ya kunshi Colombia da Portugal da kuma DR Congo.

Ƙasar dai ba ta yi nasara ko ɗaya a gasa ba inda ta sha kashi a duka wasanninta uku. An zura mata jimillar ƙwallo 11 ita kuma ta ci biyu kacal, lamarin da ya sa ta ƙare a matsayi na ƙarshe a rukunin.

Wannan dai shi ne karo na farko da ƙasar ke halartar gasar cin kofin duniya.

Saudi Arabia

Saudiyya ta fice daga gasar ne bayan ta ƙare a matsayi na ƙarshe a rukunin inda ta samu maki biyu kacal daga wasanni uku da ta buga.

Wannan shi ne karo na bakwai da ƙasar ke halartar gasar cin kofin duniya. Ta fvara halartar gasar ne a shekarar 1994, gasar da Amurka ta karɓi baƙunci kuma ta kai har zagaye na ƴan 16 a gasar.

Saudiyya ce dai ƙasar da za ta karɓi baƙuncin gasara 2024, inda ta ke sa ran taɓuka abin kirki a gaban tarin magoya bayanta.

New Zealand

New Zealand ta kasance ne a ruklunin G, inda ta fafata da Belgium da Masar da kuma Iran.

Ita ce dai kurar baya a rukunin inda ta ƙara da maki ɗaya kacal bayan canjaras ɗin da ta yi da ci 2-2 da Iran a wasanta na farko.

Baga baya ta sha kashi a hannun Masar da ci 3-1 kafin Belgium ta lallasa ta da ci 5-1 a wasanta na ƙarshe a gasar.

Wannan dai shi ne karo na uku da ƙasar ke halartar gasar kuma ba ta taɓa samun damar fitowa daga rukuni ba.

Iraƙi

Iraƙi ta fice daga gasar bana ne a ƙarshen zagayen rukuni bayan da ta ƙare a matsayi na ƙarshe a rukunin I inda ba ta samu maki ko ɗaya ba sakamakon rashin nasara da ta yi a duka wasanninta na rukunin inda ta sha kashi a hannunNorway (4-1), da Faransa (3-0), da kuma Senegal (5-).

Kafin ta halarci gasar bana sau ɗaya kacal Iraƙi ta taɓa samun gurbi a gasar, inda ta halarci gasar 1986 wanda aka yi a ƙasar Mexico.

Yanzu dai za ta yi fatan cewa ba za ta sake jira sai bayan wasu shekara 40 kafin ta sake samun damar halartar gasar ba.