Wani sabon rahoto na kuri'ar jin ra'ayin jama'a da kamfanonin dillancin labaran Reuters da Ipsos suka gudanar ya nuna cewa farin jinin Shugaban Amurka Donald Trump ya ragu matuƙa zuwa kashi 33 cikin ɗari, mafi ƙanƙanta da ya taɓa samu tun bayan komawarsa mulki.
Kuri'ar ta kuma nuna cewa yaƙin Iran na daga cikin manyan abubuwan da ke damun Amurkawa, inda kashi 80 cikin ɗari suka ce suna fargabar yiwuwar yaƙin Amurka da Iran ya daɗe.
Sai dai kashi 33 cikin 100 ne kawai suka amince da yadda Trump ke tafiyar da mulki, yayin da kashi 64 cikin 100 suka bayyana rashin gamsuwarsu da salon jagorancinsa.
Adadin amincewar da ake yi wa Trump ya ragu da kashi 35 cikin 100 da aka samu a farkon wannan wata, kuma ya yi daidai da mafi ƙarancin matakin farin jinin da ya samu a wa'adinsa na farko a watan Disambar 2017.
Tun bayan da Trump ya ba da umarnin kai hari kan Iran tare da Isra'ila, farin jininsa ya ci gaba da raguwa sosai a bana.
Yaƙin da Amurka da Isra'ila suka yi da Iran ya kuma haddasa rufe mashigar Hormuz, wanda ke da muhimmanci ga kasuwancin kusan kashi ɗaya cikin biyar na ɗanyen mai a duniya, lamarin da ya sa farashin man fetur ya tashi a Amurka.