Burkina Faso ta dawo da hukuncin kisa kan manyan laifuka

Asalin hoton, Reuters
Ƙasar Burkina Faso ta sake dawo da hukuncin kisa kan laifuka da suka haɗa da cin amanar ƙasa da ta’addanci da leƙen asiri, matakin da ya haifar da fargabar cewa gwamnatin sojin ƙasar na iya amfani da dokar wajen murƙushe masu sukar ta.
Majalisar dokokin ƙasar, wadda ba a zaɓe ta ta hanyar dimokuraɗiyya ba, ta amince baki ɗaya da sabon kundin hukunta laifuka a wannan makon, wanda ya sake dawo da hukuncin kisa kan wasu laifuka, ciki har da kashe iyaye da kuma shigo da kayayyakin da wa’adin amfaninsu ya ƙare ko waɗanda aka haramta.
Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin sojin ƙasar, ƙarƙashin jagorancin Kyaftin Ibrahim Traoré, ke fuskantar suka kan takaita ‘yancin jama’a da kuma yadda take tafiyar da yaƙi da matsalar ta’addanci da ta daɗe tana addabar ƙasar.
Ministan shari’a, Edasso Rodrigue Bayala, ya bayyana cewa wajibi ne a ɗauki matakin domin yaƙi da ta’addanci. Ya yi iƙirarin cewa masu aikata ta’addanci na cin gajiyar sassaucin tsohuwar dokar wajen ɗaukar mayaƙa, domin waɗanda aka kama da laifi za su fuskanci daurin rai da rai maimakon hukuncin kisa.
Sai dai ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Human Rights Watch (HRW) ta yi gargaɗin cewa matakin na iya mayar da hukuncin kisa wata hanya ta yin shiru da masu sukar gwamnati, a wani yanayi na ƙara matsa wa masu bayyana ra’ayoyin da ba su dace da na gwamnati ba.


































