Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a ranar Alhamis 17/09/2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Tinubu da Shettima
  • Mahajjata
  • Taron UNGA
  • Mayakan Houthi
  • Wani da ya tsira daga hannun NSCDC ya bayyana mummunan halin da suka shiga a lokacin da suke tsare.
  • Abin da ya janyo mutuwar matasa 37 a Neja - Bago
  • Aisha Aliyu Ja'afar
  • Tsadar farashin mai
  • Yadda sheikh Lukuwa
  • Hoto
  • Cyber Truck
  • Adeyemi Adeniyi
  • Abdourahamane Tchiani
  • Atiku Abubakar
  • NFF

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba da Usman Minjibir

  1. MDD ta zargi Amurka da aikata laifukan yaƙi a wasu hare-haren Iran

    wani gini

    Wani kwamitin bincike na Majalisar Dinkin Duniya kan Iran ya ce akwai hujjoji masu ƙarfi da ke zargin cewa Amurka ta aikata laifukan yaƙi a hare-hare biyu da ta kai a watan Fabrairu, waɗanda suka yi sanadin mutuwar fiye da mutane 170.

    Rahoton ya ce hare-haren makaman roka kan wata makaranta a garin Minab da kuma wani filin wasanni a Lamerd sun kasance da gangan ba tare da bambance fararen hula da wuraren soji ba, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da lalata kayayyakin more rayuwa na fararen hula.

    A baya dai Amurka ta musanta kai hari a Lamerd, sannan ta ce tana gudanar da bincike kan abin da ya faru a Minab.

    Rahoton ya kuma zargi hukumomin Iran da aikata laifukan cin zarafin bil'adama a ƙoƙarin murƙushe zanga-zangar adawa da gwamnati da aka yi a farkon wannan shekara.

  2. China ta buƙaci Iran ta yi wa mayaƙan Houthi magana su dakatar da yaƙi

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya ambato wasu majiyoyi uku daga Iran, na cewa Saudiyya ta buƙaci China ta yi tattaunawa da Iran a bayan fage, tare da roƙonta ta yi amfani da tasirinta kan mayaƙan Houthi na Yemen domin rage ayyukansu.

    Wannan buƙata ta zo ne bayan da mayaƙan Houthi suka samu gagarumin ci gaba a Yemen a makon da ya gabata, inda suka ƙwace wasu yankunan bakin teku da ke kusa da mashigar ruwa ta Bab al-Mandab.

    A bainar jama'a, China ta yi kiran kwantar da hankula da gudanar da tattaunawa da kuma tabbatar da tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa.

    Sai dai majiyoyin sun ce saƙon da Beijing ta aika a asirce ya fi faɗi da zurfi fiye da matsayinta da ta bayyana a fili.

    A cewar majiyoyin, Beijing na son Iran ta yi amfani da tasirinta kan Houthi domin hana rikicin ya bazu zuwa muhimman hanyoyin jigilar makamashi, waɗanda tattalin arzikin China, mai matsayi na biyu mafi girma a duniya, ke matuƙar dogaro da su.

    Majiyoyin, waɗanda suka yi magana da Reuters bisa sharadin rashin bayyana sunayensu, sun ce Iran ta mayar da martani da cewa: "Zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin na dogaro ne da kawo ƙarshen yaƙin da ake yi da Amurka."

  3. MDD ta yi gargaɗi sam un raguwar ruwan sha a faɗin duniya

    Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa adadin ruwan sha da ake da shi a doron ƙasa na raguwa matuƙa.

    Wani rahoto da aka fitar ranar Alhamis ya ce koguna da tabkuna na bushewa, yayin da kankarar duwatsu ke ci gaba da narkewa.

    Rahoton shekara-shekara na Majalisar Dinkin Duniya kan albarkatun ruwa ya kuma bayyana cewa sauyin yanayi na haddasa canjin mai tsanani da rashin tabbas, lamarin da ake sa ran zai janyo ƙarin ambaliyar ruwa da fari.

    Rahoton ya ce nahiyoyin Asiya da Afirka ne za su fi fuskantar mummunan tasiri, domin kusan kashi tamanin cikin dari na bala’o’in da suka shafi ruwa a baya-bayan nan sun faru ne a wadannan yankuna.

  4. An kama 'mutumin' da ya samar da abin shan 'Monkey Tail' a Ondo

    Rundunar ƴansandan jihar Ondo ta ce ta cafke wani mutum da ake zargi yana da hannu wajen samar da wani abin shan gargajiya mai guba na 'Monkey Tail' da ake zargin yana ɗauke da sinadarin methanol da ke kisa da haifar da makanta da shafar muhimman gaɓoɓin jiki.

    Ana zargin abin shan ne ya yi sanadin mutuwar mutum 49.

    Mutumin da ake zargi mai suna Oloruntoba Babatunde, wanda aka fi sani da "Meko" yana taimakawa hukumomi wajen bincike, kamar yadda ƴansandan suka shaida.

    A cewar rundunar, an miƙa samfurin abin shan da aka ƙwato a hannunsa domin gano ko suna da alaƙa da mutuwar mutane 49.

    Rundunar ta ƙara da cewa ta kama ƙarin wasu da ake zargi su 14, cikin su har da waɗanda ake zargi masu sayarwa da kuma shan kayan ne. An kama su ne a samamen da aka kai a Ore da Odigbo bayan samun rahoton mutuwar ba zata da mutanen suka yi ta sanadin shan abubuwan.

    Ƴan sanda sun ce za a gurfanar da waɗanda ake zargi gaban kotu yayin da kuma hukumomi ke ƙoƙarin shawo kan abin da ke zama ɗaya daga cikin manyan matsalolin lafiyar al'umma a baya-bayan nan da ke buƙatar ɗaukin gaggawa.

  5. Ba za mu buɗe mashigar Hormuz ba har sai ''an sauke'' Trump da Netanyahu

    Mohammad Baqer Zolqadr, mai bai wa Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran shawara kan harkokin siyasa, ya ce Iran ba za ta sake buɗe mashigar ruwan Hormuz ba har sai an sauke Shugaban Amurka Donald Trump da kuma Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu daga mulki.

    A jawabinsa, wanda ya yi ishara da kusan kwanaki 200 na rikicin da ake fama da shi, Zolqadr ya ce Iran za ta ci gaba da tinkarar Amurka da Isra'ila.

    Ya kuma bayyana rufe mashigar Hormuz a matsayin "mataki na farko na ɗaukar fansa da al'ummar Iran za su yi."

    Zolqadr ya kuma yi magana kan mutanen da suka rasa rayukansu a hare-haren da aka kai Minab da Lamerd, da kuma wasu sojojin Iran da suka mutu, inda ya ce ƙasar na da niyyar "ramuwa" a kansu.

    Waɗannan kalamai na zuwa ne a lokacin da mashigar Hormuz ta kasance ɗaya daga cikin manyan wuraren da ake takun-saka tsakanin Iran da Amurka a watannin baya-bayan nan.

  6. Labarai da dumi-dumi, Mun lalata jirgin Amurka maras matuƙi a sararin samaniyar Qeshm - Iran

    Jirgi maras matuƙi

    Dakarun Juyin Juya Halin Iran (IRGC) sun ce sun lalata wani jirgin sama maras matuƙi ƙirar MQ-9 mallakin rundunar sojin Amurka a sararin samaniyar tsibirin Qeshm.

    Sashen hulɗa da jama'a na IRGC ya ce da misalin karfe 10:12 na safiyar yau agogon ƙasar, sun harbo jirgin ne ta amfani da abin da suka kira "sabon tsarin kariyar sararin samaniya na zamani" na rundunar.

    Sanarwar ta kuma ce wannan ne jirgin sama maras matuƙi na Amurka na nau'in MQ-9 na 53 da dakarun Iran suka ce sun lalata.

  7. EU ta sanar da ƙudirin taƙaita wa yara amfani da shafukan sada zumunta

    ...

    Ƙungiyar Tarayyar Turai ta sanar da ƙudiri taƙaita wa ƴan ƙasa da shekara 16 yin amfani da shafukan sada zumunta a faɗin ƙasashe mambobinta, a wani yunƙuri na inganta lafiyarsu da kuma kare su daga matsalolin intanet.

    A ƙarƙashin tsarin, yara ƴan ƙasa da shekara 13 zuwa 15 za su samu damar amfani da shafukan na tsawon sa'a ɗaya a kowace rana ta hanyar amfani da shafin da aka tanada musamman domin yara wanda kuma yake ƙarƙashin sa idon iyaye da masu kula da su.

    Shugabar Hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen ta ce matakin zai bai wa iyaye damar sa ido kan yaransu musamman ta fuskar amfani da shafukan sada zumunta.

    Dokar ta bai wa yara ƴan shekara 15 zuwa sama su buɗe shafukansu na sada zumunta da kansu.

    Tuni wasu ƙasasahen EU suka sanar da nasu shirye-shiryen na taƙaita wa yara amfani da shafukan sada zumunta, cikinsu har da Faransa da Sifaniya.

  8. Hare-haren Amurka a Iran na iya zama laifukan yaƙi – Ƙwararrun MDD

    Masu bincike a Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce akwai hujjoji masu gamsarwa da za su sa a yadda cewa Amurka ta aikata laifukan yaƙi kan farar hula a Iran, ƙasar da ita ma suka ce ta ci zarafin bil’adama.

    A rahotonsu na baya-bayan nan da ake shirin gabatarwa ga Hukumar kare haƙƙin bil adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya a ranar Litinin, masu binciken sun buƙaci ƙasashe 47 da ke majalisar da su ƙara ƙaimi don ganin an kawo ƙarshen yaƙin tare da hukunta masu laifukan yaƙi, a kuma bai wa farar hula mafaka.

    Fiye da mutum 150, har da ɗalibai 120 aka kashe a wani hari da aka kai makarantar Shajareh Tayyibeh da ke Minab, kamar yadda jami’an Iran suka bayyana.

    Rahoton na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce Amurka ta dogara kan bayanai da ke cewa wani babban kwamandan Iran yana wajen sai dai ba a iya tantance bayanin ba.

    Iran ta musanta zarge-zargen da ek mata na take haƙƙoƙin bil adama kuma suma jami’an Amurka, a baya, sun ce hare-haren sojin da suke kai wa suna yin su ne bisa tanadin doka.

  9. An sake gano gawar mace ta tara a kisan cin zarafi a Afirka ta Kudu

    ....

    Ƴan sanda a Afrika ta Kudu sun tabbatar da sake gano gawar mace ta tara a wani yanki na East Rand inda aka gano gawawwakin wasu mata guda takwas cikin watanni biyu.

    An gano matar ne cikin mummunan yanayi - an yanke mata maƙogwaro kuma wasu ɓangaren jikinta ba a suturce ba.

    Ana ta yaɗa jita-jita inda ake alaƙanta kashe-kashen na baya-bayan nan da ake yi a yankin, da wani mai kisan ɗauki ɗaiɗai sai dai ƴan sanda ba su tabbatar da hakan ba.

    Zuwa yanzu, iyalan mutum uku ne kawai cikin matan da aka kashe suka iya gane ƴan'uwan nasu.

    Ƙaruwar kashe-kashen kusa da Kempton Park da yankuna masu maƙwabtaka ya fusata jama'a tare da sanya fargaba.

    Hakan kuma na ƙara haifar da tambayoyi game da girman matsalar cin zarafin mata a Afirka ta Kudu.

    An kuma buƙaci mata da su daina tafiya su kaɗai sannan su guji zama a wuraren da babu jama'a.

  10. Houthi ta ƙaddamar da sabbin hare-hare kan Saudiyya

    Mayaƙan Houthi a Yemen sun sanar da ƙaddamar da wasu sabbin hare-hare kan Saudiyya.

    Kafar Talabijin ta Al-Masirah ta sanar da kai sabbin hare-haren zuwa Saudiyya waɗanda suka shafi wasu turakun sadarwa uku da ke Lardin Taez, lamarin kuma da ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya.

    A baya-bayan nan ne Saudiyya ta zargi mayaƙan Houthi da kai hari Makkah, birni mafi tsarki a addinin musulunci.

    Mayaƙan Houthi dai sun zafafa hare-hare a Saudiyya tun bayan da suka ƙwace wasu yankunan gaɓar Tekun Maliya da Mashigar ruwa ta Bab al-Mandeb daga hannun dakarun da ke samun goyon bayan Saudiyya.

    A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya, sama da mutum 100,000 aka ɗaiɗaita yayin da yaƙi ke ƙara ƙamari a Saudiyya.

  11. Mutum 49 sun mutu bayan shan 'gurɓataccen abin sha na gargajiya' a Ondo

    Adadin mutanen da suka mutu sakamakon shan wani abu da ake zargin gurɓataccen abin sha ne a jihar Ondo ya ƙaru zuwa 49 inda waɗanda abin ya shafa suka kai kusan 170, kamar yadda hukumomin lafiya suka tabbatar.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mutum 30 a yankunan Araromi-Obu da Odigbo da ke ƙaramar hukumar Odigbo sun mutu ne sakamakon san haɗin na 'Monkey Tail'.

    Shugaban ƙaramar hukumar ta Odigbo, Taiwo Adegoroye, da farko ya ce mutum 14 ne suka mutu a Araromi-Obu sai wasu 16 a Odigbo.

    Sai dai binciken da aka gudanar ya nuna cewa adadin mutanen ya ƙaru har ma yawan waɗanda suka mutu sanadin hakan ya kai 49 zuwa jiya Laraba.

    A cewar Daily Trust, Kwamishinan Lafiya a jihar ta Ondo, Dakta Banji Ajaka, ya ce matsalar ta yaɗu zuwa ƙaramar hukumar Irele inda mutum 19 suka mutu.

  12. Yaƙin Iran ya kusa zuwa ƙarshe - Trump

    ...

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya jaddada cewa Iran na son a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

    Trump ya bayyana haka ne a wani gangami da ya yi a North Carolina na zaɓen tsakiyar zango da za a yi cikin watan Nuwamba.

    Yayin gangamin Trump ya yi ta nanata cewa Iran na neman a ƙulla yarjejeniya, sai dai tattaunawar Amurka da Iran a watannin baya-bayan nan ba su haifar da wata yarjejeniya mai ɗorewa ba.

    Duka ƙasashen biyu sun sha kai wa junansu hare-hare saɓanin matsayar a suka ɗauka.

    A cewar Trump, "ina fatan mun kusa ganin ƙarshen yaƙin. Suna son a cimma yarjejeniya, amma za mu ga yadda za ta kaya."

    Nuna damuwa da masu zaɓe ke yi kan ƙaruwar farashi da haraje-haraje da kuma tsadar mai sakamakon yaƙin da kuma rufe Mashigar Hormuz, ya zama ƙalubale ga ƴantakarar Republicans da dama gabanin zaɓen na watan Nuwamba, wani abu da ake ganin ya ƙarfafa wa Trump gwiwa ta alal aƙalli ya tattauna da Iran don kawo ƙarshen yaƙin.

  13. An ƙara kuɗin ruwa a Amurka karon farko cikin shekara uku

    ..

    Shugaban Amurka Donald Trump ya soki hukumar babban bankin kasar kan ƙara yawan kuɗin ruwa a karon farko cikin shekaru uku, matakin da ya kira na bita da kullin siyasa.

    Mista Trump ya sha yin kira da a rage yawan kuɗin ruwa, amma masu tsara manufofi a Babban Bankin sun nuna cewa akwai yiwuwar a sake ƙara kuɗin domin daƙile hauhawar farashin kayayyaki.

    Wakiliyar BBC ta ce da alama ba wannan ne kaɗai sauyin da za a samu a kan kuɗaɗen ruwa a wannan shekarar ba, kasancewar hukumar bankin ta nuna cewa tana sa ran yin wani ƙarin kafin ƙarshen shekara.

  14. Amurka ta sake hana Mahmoud Abbas bizar shiga ƙasar

    Mahmoud Abbas

    Jami'an Falasdinawa sun bayyana cewa Amurka ta sake hana shugaban Hukumar Falasdinawa Mahmoud Abbas bizar shiga kasar.

    Wannan shi ne karo na biyu a jere da za a bukaci Mista Abbas ya yi jawabi ga Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya ta hanyar bidiyo.

    Wakilin BBC ya ce Gwamnatin Trump ta zargi kungiyoyi irinsu PA da PLO - wadanda su ne ƙungiyoyi masu wakiltar Falasɗinawa da aka amince da su a duniya da abin da ta kira kambama ta'addanci.

    Haka kuma ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta hana wasu jami'an Falasdinawa da dama, wadanda ke shirin raka Mista Abbas, samun bizar shiga kasar.

  15. Aisha Buhari ta kai wa Atiku ziyara

    ....

    Mai ɗakin tsohon shugaban Najeriya, Aisha Buhari ta kai wa tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ziyara.

    Atiku Abubakar, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar ADC a zaɓen 2027, ya bayyana hakan a shafinsa na Fesbuk inda ya bayyana jin daɗinsa da ziyarar da ta kai masa tare da tawagarta.

    Sai dai babu ƙarin bayani game da dalilan ziyarar tata.

    Atiku ya kuma ce ziyarar wata tunatarwa ce cewa akwai buƙatar masu neman ganin an samu sauyi a Najeriya su mayar da hankali kan inganta walwala da kuma makomar ƴan ƙasar.

    A cewarsa, ƴan Najeriya suna fuskantar ƙaruwar matsi sakamakon tashin farashin kayayyaki har da kayan masarufi da sufuri da ilimi har ma da harkar lafiya.

    Tsohon mataimakin shugaban Najeriyar ya bayyana cewa ƴan Najeriya sun cancanci tattalin arzikin da zai samar da damarmaki da kuma bai wa jama'a damar yin rayuwa mai ƴanci da ke cike da kyakkyawan fata.

  16. NLC ta nemi gwamnati ta sassautawa ƴan Najeriya kan tsadar mai

    ..

    Ƙungiyar ƙwadago a Najeriya, NLC ta buƙaci gwamnati da ta gaggauta bijiro da matakan sassautawa al'umma da ma ƴan kasuwa sakamakon ƙarin farashin man fetur.

    Shugaban NLC, Joe Ajaero ya ce ya kamata gwamnati ta duba yiwuwar samar da albashin da ya dace ga ma'aikata wanda zai yi daidai da yanayin da ake ciki sannan ta riƙa sayar da ɗanyen mai ga matatun cikin gida ta hanyar amfani da naira, ta kuma faɗaɗa ma'ajiyar man fetur ta ƙasa don buƙatun gaggawa.

    Jaridar Punch ta ruwaito cewa a wasu jihohin, mai ya tashi zuwa kusa N1,500 ka kowace lita.

    Ajaero ya ƙara da cewa akwai buƙatar gwamnati ta riƙa bayar da tallafi a lokutan da ake da buƙata ganin yadda Najeriya ta kasance mai yawan albarkatun ƙasa.

    NLC ta kuma ce gwamnati ta ci gajiyar tashin da ɗanyen mai yake yi a duniya ina kuma ya yi zargin cewa ana sayar da ɗanyen mai ne kan kamar dala 35 zuwa dala 40 kowace ganga, wanda hakan ya zarce yadda aka ɗora kuɗin man a kasafin kuɗin Najeriya.

  17. Trump na barazanar yanke alaƙar kasuwanci da EU kan Canada

    Trump

    Shugaba Donald Trump ya yi barazanar yanke harkar kasuwanci da Tarayyar Turai idan ta bi shawarar mayar da Canada mamba ta musamman a karon farko a tarihin ƙungiyar.

    Da yake bayyana shirin a matsayin abin dariya, Mista Trump ya ce zai ɗauke shi a matsayin mataki na cin mutunci wanda zai iya haifar da ƙarin haraji kan Tarayyar ta Turai.

    Shugabar Hukumar Tarayyar, Ursula von der Leyen, ta shaida wa Majalisar Tarayyar Turai a baya cewa tana son yin aiki kan "buɗe ƙofa" ga Canada.

    A makon da ya gabata Firaministan Canada Mark Carney ya yi magana game da neman ƙulla "ƙawance na musamman" da Tarayyar Turai, a daidai lokacin da dangantaka ke ƙara tsami tsakanin kasarsa da Amurka.

  18. Barka da Safiya

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Alhamis.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa.

    Ku kasance da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya.

    Akwai shafukanmu na sada zumunta da za ku iya karanta arin labarai da kuma kallon bidiyo.