Ana zargin jagoran ƴan adawar Zambia da cin amanar ƙasa
Ƴansandan Zambia sun gurfanar da magudun jam'iyyar adawa na babban zaben shugaban kasa da aka gudanar a wannan watan, wanda ake takaddama a kansa, bisa zargin cin amanar kasa.
An tuhumi Brian Mundubile tare da abokin takararsa, Makebi Zulu, da wasu mutum goma sha shida.
An kama mutum biyu ne a ranar Alhamis bayan da Shugaba Hakainde Hichilema ya matsa wa Majalisar Dinkin Duniya da ke Lusaka lamba kan ta mika su ga hukumomin kasar.
Sun nemi mafaka ne a ofishin Majalisar Dinkin Duniya bayan da jami'an tsaro suka kashe wani tsohon minista tare da kama wasu 'yan siyasa a wani samame.
Mista Mundubile ya yi watsi da zargin gwamnati cewa jam'iyyarsa na shirin tayar da bore domin kifar da gwamnati.
Laifin cin amanar kasa a Zambia na iya haifar da hukuncin daurin rai da rai.