APC ta musanta zargin shirin kashe Atiku
Jami'yyar APC mai mulki a Najeriya ta musanta zargin cewa akwai wani shiri na kashe tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Action Democratic Congress (ADC) a zaɓen shekarar 2027, Atiku Abubakar.
Mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen jamiyyar APC, Dele Alake, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar, yayin da yake mayar da martani kan wani zargi da wani ɗan jam'iyyar ADC, Timi Frank, ya yi.
Jam'iyyar APC ta musanta kai-tsaye cewa Shugaba Bola Tinubu ko Fadar Shugaban Ƙasa ko kuma APC'n na da hannu a duk wani shirin cutar da Atiku Abubakar ko wani jigon jam’iyyun adawa.
Sanarwar ta kuma musanta rahotannin da ke cewa an janye jami’an tsaron da ke kare tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar, inda ya tabbatar da cewa Atiku na ci gaba da samun cikakkiyar kariya daga rundunar ’yan sandan Najeriya da kuma Hukumar Tsaro ta DSS.
Dele Alake ya kuma ce zargin kisan ba komai bane illa 'ƙulle-ƙullen siyasa irin ta jamiyyun adawa', inda ya ce an yi hakan ne domin a zafafa siyasar ƙasar da kuma jawo hankalin ƙasashen duniya ta hanyar amfani da kafafen sada zumunta.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa a kwanan nan ne ma Shugaba Tinubu ya umarci hukumomin tsaro da su ƙarfafa matakan tsaron da ake bai wa dukkan ’yan takarar shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa da gwamnoni da mataimakin gwamna gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Mai magana da yawun kwamitin ya kuma jaddada cewa duk wata barazana ga rayuwar ɗan ƙasar abu ne mai haɗari da ke buƙatar a ɗauki mataki ba tare da la’akari da siyasa ba, tare da kira ga Frank da ya gabatar da duk wata hujja da yake da ita ga hukumomin tsaro domin gudanar da bincike cikin gaggawa.