Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 11/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Asabar 11 ga watan Yulin 2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. Mojtaba Khamenei ya sha alwashin ɗaukar fansar kisan mahaifinsa

    Sabon jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei, ya sha alwashin ɗaukar fansar kisan mahaifinsa Ali Khamenei, wanda ya mutu a hare-haren Isra'ila da Amurka a ranar farko ta yaƙin.

    A wani saƙo da aka wallafa da sunansa domin gode wa waɗanda suka halarci jana'izar mahaifinsa, Mojtaba Khamenei ya ce za su ɗauki fansar jininsa da kuma na sauran waɗanda suka mutu a harin da Amurka da Isra'ila suka kai wanda ya bayyana a matsayin kisan gilla.

    Ya kuma jaddada cewa ɗaukar wannan fansa buri ne na al'ummar Iran, yana mai cewa dole ne a tabbatar an aiwatar da ita ba tare da gazawa ba.

    Tun bayan da aka ce ya maye gurbin mahaifinsa a matsayin jagoran Iran, Mojtaba Khamenei bai bayyana a bainar jama'a ba, kuma har yanzu ba a ji saƙon murya ko na bidiyo daga gare shi ba, sai dai rubuce-rubucen da ake wallafawa da sunansa.

  2. Yunwa ta kashe mutane 16 a Uganda sakamakon fari

    Gwamnatin Uganda ta ce aƙalla mutum16 sun mutu sakamakon yunwa a yankin Karamoja da ke arewa maso gabashin ƙasar, bayan dogon fari da ya lalata amfanin gona.

    Firaministar Uganda, Robinah Nabbanja, ta ce dubban iyalai sun rasa abinci bayan rashin ruwan sama tun daga watan Afrilu, lokacin da ake fara shuka amfanin gona.

    Manoma sun ce gonakin masara, dawa da waken soya sun lalace saboda ƙarancin ruwa, lamarin da ya rusa fatan samun girbi mai yawa a bana.

    Gwamnatin ta fara raba kayan agajin gaggawa, yayin da masana ke danganta matsalar da sauyin yanayi, sare itatuwa, yawan kiwo ba tare da kulawa ba da kuma ƙwarin da ke lalata amfanin gona. Sun yi kira da a ƙara zuba jari a ban ruwa da kuma iri masu jure fari.

  3. Ba mu nemi tattaunawa da Amurka ba – Iran

    Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baghaei, ya ce Tehran ba ta nemi wata tattaunawa da Amurka ba, sai dai ta amince da buƙatar wani mai shiga tsakani daga yankin domin tattauna sabbin abubuwan da ke faruwa.

    Baghaei ya bayyana cewa wakilin ya kai ziyara birnin Mashhad, inda Iran ta bayyana matsayinta ga ƙasar Qatar da ke taka rawa wajen shiga tsakani.

    Ya kuma zargi Amurka da karya wasu sassa na yarjejeniyar da aka cimma kwanan nan.

    A cewarsa, cikin kwanaki 21 zuwa 22 kacal bayan rattaɓa hannu kan yarjejeniyar, Amurka ta saɓa wa wasu tanade-tanadenta, ciki har da wasu abubuwan da suka faru a ranakun Laraba da Alhamis da kuma soke lasisin sayar da man fetur na Iran.

    Baghaei ya ƙara da cewa sabbin takunkuman da Amurka ta ƙaƙaba wa Iran sun saɓa wa sashe na tara na yarjejeniyar, yana mai jaddada cewa Tehran na ganin waɗannan matakan a matsayin karya alƙawuran da aka ɗauka.

  4. Farashin fetur ya ƙaru a Amurka sakamakon yaƙin Iran

    Farashin man fetur a Amurka ya sake tashi bayan makonni da dama yana sauka, sakamakon ƙarin tashin hankalin da ke tsakanin Amurka da Iran da kuma hauhawar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce matsakaicin farashin galan ɗaya na fetur ya ƙaru da cent shida a wannan mako, inda ya kai dala $3.88, wanda shi ne ƙaruwa mafi girma cikin mako guda tun tsakiyar watan Mayu.

    Hare-haren da aka kai kan wasu tankokin dakon mai a mashigar Hormuz da kuma musayar hare-hare tsakanin Amurka da Iran sun taimaka wajen haɓaka farashin ɗanyen mai na Brent da kusan kashi 5.5 cikin ɗari a wannan mako.

    Rahotanni sun ce zirga-zirgar man fetur ta mashigar Hormuz har yanzu ba ta koma yadda take kafin rikicin ba.

  5. Yau wa'adin Amurka ga Iran kan mashigar Hormuz zai ƙare

    Yau ne ake sa ran wa’adin da Amurka ta bai wa Iran zuwa ƙarshen ranar yau Asabar zai ƙare, inda ta buƙaci Tehran ta ba da tabbacin cewa mashigar Hormuz za ta ci gaba da kasancewa a buɗe kuma ba za a kai hare-hare kan jiragen kasuwanci ba.

    Jami’an Amurka sun ce Iran ta shaida musu a sirrance cewa wasu masu tsattsauran ra’ayi da ba sa aiki ƙarƙashin cikakken ikon gwamnati ne ke da hannu a hare-haren da aka kai kan wasu jiragen ruwa, da nufin kawo cikas ga tattaunawar da ake yi.

    A daidai lokacin da ake fargabar ƙarin tashin hankali a yankin, Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, ya kai ziyara ƙasar Oman domin tattauna rikicin da ya shafi mashigar Hormuz.

    Haka kuma, wata tawagar masu shiga tsakani daga Qatar ta gana da jami’an Iran a Tehran, a wani yunƙuri na hana rugujewar fahimtar juna tsakanin Iran da Amurka da kuma rage zafafan takun-saƙar da ke ƙara ƙamari a yankin.

    Mashigar Hormuz na daga cikin manyan hanyoyin jigilar man fetur a duniya, kuma duk wani rikici a yankin na iya yin tasiri ga kasuwancin duniya da kuma farashin mai.

  6. Yadda aka kuɓutar da ɗalibai da malamai 44 da aka sace a Oyo - Sojoji

    Rundunar Sojin Najeriya ta ce an kuɓutar da ɗalibai da malamai 44 da aka sace a ƙaramar hukumar Oriire ta jihar Oyo bayan wani samamen haɗin gwiwa da ya ɗauki fiye da wata guda, wanda aka gudanar tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro da na leƙen asiri daban-daban.

    Mai magana da yawun rundunar sojin ƙasa, Danjuma Jonah Danjuma, ya ce aikin ya mayar da hankali kan gano waɗanda suka shirya garkuwar da kuma lalata hanyoyin tallafi da maɓoyarsu da ke cikin dajin Old Oyo National Park.

    Ya ƙara da cewa kama wasu da ake zargi ya tarwatsa ƙungiyar, lamarin da ya kai ga sakin waɗanda aka sace ba tare da wani sharadi ba.

    Tun da farko, mai bai wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya sanar da sakin ɗaliban da malaman tare da wallafa hotunansu a shafinsa na X.

    An sace ɗalibai 39 da malamai bakwai a wani hari da aka kai ranar 15 ga Mayun 2026, kuma rundunar sojin ta ce ana kula da lafiyar waɗanda aka ceto kafin a haɗa su da iyalansu.

  7. Idan Iran ta yi yunƙurin kashe ni, za ta fuskanci hare-hare mafi muni - Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa Iran gargaɗi cewa za ta fuskanci hare-hare mafi muni idan ta yi yunƙurin kashe shi, yana mai cewa sojojin Amurka sun shirya tsaf domin mayar da martani cikin ƙarfi.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Truth Social, Trump ya ce:

    “Makaman roka dubu ɗaya a shirye suke su afka wa Iran idan ta aiwatar da duk wata barazana ta kashe ni, nan take za a harba ƙarin dubban makamai masu linzami.”

    Trump ya kuma ce ya bayar da umarnin da suka dace, yana mai cewa sojojin Amurka sun shirya su “lalata dukkan yankunan Iran gaba ɗaya” na tsawon shekara guda.

    Wannan barazanar na zuwa ne bayan wasu rahotanni sun bayyana cewa jami’an leƙen asirin Isra’ila sun gano wani sabon shiri da ake zargin Iran na yi na kashe Trump.

    Haka kuma, an ga wasu hotuna da kalamai masu nuna adawa da Trump a yayin jana’izar Jagoran Addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

    Sai dai jami’an Iran sun sha musanta zarge-zargen cewa suna da wani shiri na kashe Donald Trump.

  8. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa,barkanmu da wannan safiya ta ranar Laraba.

    Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokacin.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.