KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, 03/04/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, 03/04/2026

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

  1. Farashin kayan abinci ya tashi saboda yaƙin Iran -MDD

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce farashin kayan abinci ya yi tashin da ya daɗe bai yi ba tsawon watanni shida da suka wuce, kuma akwai yiwuwar zai ci gaba da tashi idan yaƙin da ake yi tsakanin Amurka da Isra'ila kan Iran ya ci gaba.

    Babban jami'in tattalin arziki na hukumar kula da abinci da noma na Majalisar ya ce hauhawar farashin mai ne babban abin da za a ɗora wa alhakin karuwar farashin abincin zuwa yanzu, amma ya yi gargaɗin cewa katse samar da taki da wasu muhimman kayayyakin noma na iya ƙara ta'azzara lamarin.

    Ƙasashe da dama sun baiwa ma'aikata umurnin yin aiki daga gida,kuma sun ƙara farashin man fetir, sakamakon yadda hana wucewa ta mashigar Hormuz ya hana su shigar da mai da iskar gas cikin ƙasashensu.

  2. NBC ba ta da hurumin cin tarar gidajen radiyo da talbijin a Najeriya - Kotu

    Hukumar NBC

    Asalin hoton, NBC

    Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da hukumar kula da gidajen radiyo ta Najeriya NBC ta shigar gabanta, tana neman kotun ta rusa hukuncin da babbar kotun tarayya ta yi na hana ta cin tarar wasu gidajen radiyo da talbijin a faɗin ƙasar.

    Yayin da yake gabatar da hukuncin, babban kotun Mai shari'a Oyebiola Oyewumi a madadin alkalan kotun uku ta amince da hukuncin babbar kotun tarayya, wanda ya hana hukumar NBC cin tarar gidajen labari 45 a ranar 1 ga watan Maris na 2019 saboda zarginsu da saɓa ƙa'idar dokar yaɗa labarai ta Najeriya.

    Kotun ɗaukaka ƙarar ta ce hukumar NBC ba ta hurumin cin tarar gidajen labarai a ƙasar.

    Mai Shari'a Oyewumi ta ci gaba da cewa a ƙarƙashin dokokin Najeriya ana cin tara ne ga waɗanda aka samu da laifin saɓa doka, kuma kotu ce kawai ke da hurumin yin hakan, ba mutumin da aka yi wa laifi ba.

    Tun da farko babbar kotun tarayyar ta ce matakin na NBC ya saɓa wa dokokin Najeriya.

  3. 'Ƴanbindiga sun sace fiye da mutum 150 a Zamfara'

    yanbindiga

    Asalin hoton, Daily Trust

    Al'ummar yankin Bukkuyum a jihar Zamfara sun ce ƴanbindiga sun yi sace fiye da mutum kusan 150 a wani hari da suka kai cikin dare.

    Mazauna yankunan sun ce ƙauyuka da dama ne ƴanbindigar suka tarwatsa, inda ɗaruruwan mutane suka yi gudun hijira.

    Hon Sulaiman Abubakar Gumi, ɗanmajalisar wakilai na tarayya mai wakilar Gumi da Bukkuyum ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin, inda ya ce mazauna ƙauyukan Kurfa Ɗanya da Kurfan Magaji sun kwana cikin tashin hankali.

    Ya ƙara da cewa kawo yanzu duka mutanen waɗannan garuruwa sun guda sun bar gidajensu, yayin da suke gudun jira a cikin garin Bukuyyum.

    Ya ci gaba da cewa dama yankin Bukuyyum da Gumi da Anka ya jima yana da fama da matsalar hare-haren ƴanbindiga masu sace mutane domin neman kuɗin fansa.

    Hon Abubakar ya yi kira ga gwamnatin ƙasar ta mayar da hankali domin magance matsalolin tsaron jihar Zamfara.

    ''Mun ga alamun gwamnati yanzu ta mayar da hankalinta a Borno, saboda barazanar dawowar Boko Haram, amma muna kira a gare ta cewa Zamfara na fama da matsalar tsaro'', in ji shi.

  4. Tinubu ya ce za a saka kyamarorin tsaro fiye da 5,000 a Filato

    Kyamarorin tsaro

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Najeriya ta ce za ta saka kyamarorin tsaro masu amfani da fasahar AI fiye da 5,000 domin taimaka wa jami'an tsaro yaƙi da matsalar tsaro a jihar Filato da ke tsakiyar ƙasar.

    Shugaba Tinubu ya bayyana matakin yayin da yake jawabi a lokacin ziyarar jaje da ya kai jihar ranar Alhamis.

    Ziyarar tasa na zuwa ne bayan da wasu mahara suka kai hari ƙauyen Angwan Rukuba da ke ƙaramar hukumar Jos ta Arewa tare da kashe mutane.

    Shugaba Tinubu ya ce minsitan sadarwar zamani da tattalin arziki, Bosun Tijjani ne zai kula da saka kyamarorin tare da hadin gwiwar gwamnatin Filato da jami'an tsaro.

    ''Za a fara saka kyamarorin ne daga birnin Jos sannan a faɗaɗa aikin zuwa sauran sassan jihar, kamar yadda aka saka jihohin Legas da Enugu'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

    Shugaban na Najeriya jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su, tare da alƙawarta farauto maharan.

    “Na yi muku alƙawarin cewa irin wannan al'amari ba zai sake faruwa ba,'' in ji shi.

    Shugaba Tinubu ya kuma umarci ministan tsaron ƙasar, Janar Christopher Musa (mai ritaya) da babban hafsa sojin ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu da kuma babban sifeton ƴansandan ƙasar, Olatunji Disu, su “tabbatar da kamo waɗanda suka aikata kashe-kashen” na waɗanda ba su ji ba su gani ba.

  5. An zaɓi shugaban mulkin sojin Myanmar matsayin shugaban ƙasar

    Majalisar dokokin ƙasar Myanmar ta zaɓi jagoran juyin mulkin ƙasar Janar Min Aung Hlaing a matsayin cikakken shugaban ƙasar.

    Majalisar na ƙarƙashin rinjayen magoya bayan sojoji bayan zaɓukan da aka yi kwanan nan, waɗanda ake zargin an tafka maguɗi.

    Janar Hlaing ne ya jagoranci kifar da gwamnatin Aung San Suu Kyi, shekaru biyar da suka gabata.

    Sabon shugaban ƙasaer mai shekara 69 na fatan gwamnatinsa za ta samar wa ƙasar kima, musmman ga ƙawayen ƙasar irin su China.

    Yaƙin basasar da ƙasar ta shafe shekaru tana fuskanta ya haifar da koma-baya ga tattalin arzikin ƙasar.

    Janar Min ya sauka daga muƙaminsa na shugaban rundunar soji domin karɓar wannan sabon matsayi, wanda yake fatan zai sa gwamnatinsa ta samu karbuwa a duniya.

    Sai dai ba a tunanin samun wani gagarumin sauyi.

  6. Iran ta ci gaba da kai hare-hare kan Isra'ila da yankin Gulf

    Hri

    Asalin hoton, ..

    Iran ta ci gaba da kai hare-hare kan Isra'ila da sauran ƙasashen yankin Gulf.

    A Kuwait babban kamfanin na ƙasar ya ce an kai wa matatar mai ta Mina al- Ahmadi hari da jirage marasa matuƙa, yayin da ma'aikatan agaji ke ƙoƙarin kashe gobarar da ta tashi bayan hare-haren.

    Can a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa hukumomin ƙasar sun bayar da rahoton kai hare-hare.

    A Isra'ila sojojin ƙasar sun ce na'urorin tsaron samniyarta na aikin kakkaɓo makaman linzami da Iran ta harba cikin ƙasar.

  7. Dimokraɗiyya ba ta dace da Burkina Faso ba - Traore

    Kyaftin Ibrahim Traore

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban mulkin sojin Burkina Faso ya shaida wa al’ummarsa su daina sa rai da dimokuraɗiyya.

    A wata hira da aka watsa a gidan talabijin na ƙasa, Kyaftin Ibrahim Traore ya ce ba shi da wani shiri na gudanar da zaɓe, duk da cewa ya yi alƙawarin mayar da mulki ga farar hula lokacin da ya karɓi iko shekaru huɗu da suka gabata.

    Sai dai a ranar Alhamis, ya bayyana a fili cewa dimokuraɗiyya ba ta dace da al’ummar Burkina Faso ba.

    Gwamnatinsa ta soja ta gaza shawo kan rikicin tashe-tashen hankulan masu iƙirarin jihadi da suka addabi ƙasar.

    Haka kuma, ƙungiyoyin kare hakkin ɗanadam na ci gaba da suka kan kamun ludayin gwamnatinsa ta fuskar ƴancin ɗan'adam.

  8. Kiristoci na bukuwan Ranar Easter

    Mahalarta taron addu'o'in Easter

    Asalin hoton, Getty Images

    Babban limamin Katolika na Latin a Birnin Ƙudus ya jagoranci wani taron ibada kwanaki bayan da ƴansandan Isra’ila suka hana shi shiga cocin da ake girmamawa a matsayin wurin da aka gicciye Yesu Almasihu.

    A daren Alhamis, Kardinal Pier-battista Pizza-balla ya wanke ƙafafun fastocinsa a wani ɓangare na al’adar ibadar Kirista.

    Ana sa ran zai jagoranci wasu ibadu a yau, ciki har da ranar Good Friday da kuma Easter Sunday, sai dai za a takaita yawan masu halarta saboda matsalolin tsaro da suka shafi yaƙin da ake yi da Iran.

    A sauran majami’u kuwa, za a bai wa mutane kusan hamsin damar halartar tarukan ibadar.

    Duk da haka, yawancin wuraren ibada a tsohon Birnin Ƙudus na ci gaba da kasancewa a rufe, ciki har da masallacin Al-Aqsa da kuma Western Wall.

  9. Za mu tsananta hare-hare kan Iran idan ba ta ba da kai ba - Trump

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar ƙara tsananta hare-hare kan Iran, matsawar shugabanninta ba su ba da kai ga buƙatunsa ba.

    Wannan gargaɗi na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan wasu ƙwararru a fannin dokokin duniya sun fitar da wata wasiƙa, inda suka yi gargaɗi kan manyan take dokoki da ake zargin Amurka, da Isra’ila da Iran da aikatawa.

    Ƙwararrun sun nuna damuwa kan kalaman barazanar da Mista Trump ke yi a tsawon yaƙin.

    Shugaban ya sake yin barazanar kai hari kan kayayyakin more rayuwa na Iran, kamar lalata gadoji da cibiyoyin wutar lantarki, abun da za a iya ɗauka a matsayin laifukan yaƙi.

    A ranar Alhamis, Amurka da Isra’ila sun kai hari kan wata gada da ake ginawa, da kuma wata daɗaɗɗiyar cibiya mai tarihi da ke samar da riga-kafin cututtuka.

  10. Assalam alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a da Hausawa ke yi wa kirari da Hajji babbar rana.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki, musamman yakin Iran da siyasar Najeriya.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafa.