Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, 19/04/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, 19/04/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Muhammad Buhari Fagge

  1. Har yanzu tsugune ba ta ƙare ba a yaƙin Iran - Netanyahu

    Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce "har yanzu tsugune ba ta ƙare ba" a yaƙin da suke yi da Iran.

    Ya bayyana hakan ne a yayin da suke tattaunawa da manema labarai bayan karɓar baƙuncin shugaban ƙasar Argentina Javier Milei a Birnin Ƙudus.

    "Muna cikin wani lokacin mai cike da ƙalubale da kuma jiran sakamako. Muna yaƙi tare da Amurka kan Iran," a cewarsa.

    "Mun cimma nasara da dama ya zuwa yanzu a yaƙin. Kuma har yanzu tsugune ba ta ƙare ba, kuma a kowanne lokaci za a iya samun sabbin labarai kan yaƙin".

  2. Fafaroma ya jagoranci taron addu'o'i a Angola

    Fafaroma Leo ya yi kira ga ƴan ƙasar Angola su kawo ƙarshen rarrabuwa kai tsakananinsu don samar da ingantaccen zaman lafiya a ƙasar.

    Ya yi wannan jawabi ne yayin taron addu'oi a cocin Muxima wani yanki mai muhimmanci da a baya aka yi amfani da shi a wajen cinikin bayi.

    Fafaroman ya bayyana Angola a matsayin kyakkyawar ƙasa wadda rikici ya yi wa illa.

    Ya jaddada buƙatar kaunar juna maimakon yaƙi.

    Cocin na ɗauke da hoton Mary wadda aka fi sani Mama Muxima.

  3. Me ya yi saura ga Arsenal?

    Yayin da ya rage wasanni biyar a kammala Primier Ingila, makin uku ne ya rage tsakanin Arsenal da ke jan ragamar teburin da kuma Manchester City da ke matsayi na biyu.

    Amma ga City wasa shida ne ya rage mata, wadda take da kwantan wasa tsakaninta da Crystal Palace.

    Da zarar ta ci wasan zai zama makinsu ɗaya da Arsenal, kowa yanaa da maki 70, kuma kwallo ɗaya ce kawai ke tsakanin kungiyoyin dake rige-rigen lashe gasar.

    Wannan ne karo na uku da Arsenal ke jan ragamar gasar na tsawon lokaci sai a daf da kammala gasar kuma ta sakko daga matsayi na ɗaya mai biye mata a baya ta lashe.

    Arsenal wadda ita kaɗai ce kungiyar da ta rage a gasar zakarun Turai daga Ingila za ta fafata wasanta na gaba ne da ƙungiyar Atlethico Madrid ta Sifaniya.

    Ko mene ne ya rage wa Arsenal?

    Masu sharhi na ganin wannan gasar ma za ta kuɓucewa wa Arsenal, saboda la'akari da ƙoƙarin ƙungiyoyin biyu Arsenal bai zama dole ta iya cin kwallaye da yawa da City take iya ci ba.

    Yanzu abin jira a gani mene ne zai faru daga nan zuwa ƙarshen gasar ta bana.

    Idan kowa ya ci wasan da ya rage masa ba tare da matsala ba, kwallo tsakaninsu ce za ta raba su.

  4. Babu gaskiya kan batun sake tattaunawa da Amurka a Pakistan - Iran

    Kamfanin dillancin labarai ba Iran ya ce bayanan da suke cewa za'a sake wata sabuwar tattaunawa karo na biyu da Amurka a Pakistan "ba gaskiya ba ne".

    Ta zargi Amurka da turo buƙatu masu yawa, wanda yake rudar da ita Amurkan sannan kuma tana sassauya buƙatun nata akai-akai.

    Wannan da kuma toshe tashoshin ruwanmu ne ya haifar da koma baya a tattaunawar da aka so a ci gaba.

    "Da wannan babu wani fatan samun tattaunawa da za ta kai ga mafita a nan gaba," kamar yadda ta bayyana a Telegram, sai dai ba ta ambato wani babban jami'i da ya fadi hakan ba, ko kuma wata cibiya.

    Wannan yazo ne bayan wani saƙo daga wasu kafafe da ke da alaƙa da IRGC, wadda ta musanta yiwuwar kasancear Iran cikin batun a nan gaba.

    Har yanzu babu tabbaci ko jami'an Iran za su kasance cikin tattaunawar, kuma babu wani jami'i da zai ce ga matsayar Iran cikin lamarin.

  5. Tinubu bai min alƙawarin komai ba - Malam Shekarau

    Tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim ya ce babu wani kuɗi ko alƙawari da shugaba Tinubu ya yi masa gabanin komawarsa jam'iyyar APC mai mulki.

    Shekarau ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da BBC Hausa, jim kaɗan bayan sanarwarsa ta koma jam'iyyar APC.

    Shekarau ya ce ya koma APC ne da burin samar da na shi taimakon ga Najeriya da kuma jam'iyyar, inda ya ce yana fatan ganin abubuwan ci gaba a ko ina a ƙasar.

    Ko da aka tambaye shi game dalilin da ya sa bai koma jam'iyyar ADC mai adawa ba, Shekarau sai ya ce "ba na bin yayi ko kuma inda muradin masu neman mulki ya haɗa su, ina nufin duk wanda ka ga ni a haɗakar ta 'yan takara ce," in ba a kai ga gaci ba kowa watsewa zai yi.

    "Na ji mutane na cewa kuɗi aka ba ni tun lokacin da muka haɗu da Tinubu, amma ba haka abin yake ba, babu wanda ya ba ni kuɗi ba kuma wanda ya yi min alƙawarin komai a jam'iyya," in ji Malam Shekarau.

    Ya ce babu matakin da yake ɗauka shi kaɗai har sai ya tattauna da hadimai da sauran mabiyansa.

    Shekarau ya koma APC ne daga jam'iyyar PDP mai hamayya wadda rikicin shugabanci na cikin gida ya kasarra.

  6. JD ne zai jagoranci wakilan Amurka a tattaunawa da Iran a Pakistan

    Wani jami'i a fadar White House ya shaida wa BBC cewa mataimakin shugaban Amurka, JD Vance ne zai jagoranci tawagar wakilan ƙasar da ta ƙunshi mashawartan Shugaba Trump biyu, Steve Witkoff da Jared Kushner zuwa tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin Iran da za a yi a Islamabad.

    A makon da ya gabata ma dai Mista Vance ne ya jagoranci tawagar wakilan na Amurka a zaman da bai yi nasara ba da aka yi a birnin na Islamabad.

    Kawo yanzu babu tabbas ko Iran za ta shiga tattaunawar, da ma waɗanda ke cikin tawagarta idan za ta je tattaunawar.

  7. Turkiyya za ta kafa sansanin horon soji a Najeriya

    Najeriya da Turkiyya sun amince da kafa babbar cibiyar horon soji a Najeriya, a wani ɓangare na haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen biyu.

    An cimma yarjejeniyar ce lokacin wata tattaunawar diplomasiyya tsakanin ministocin tsaron ƙasashen biyu a a gefen taron diplomasiyya na 2026.

    A ƙarƙashin yarjejeniyar dakarun tsaron Najeriya za su riƙa samun horo a fannoni daban-daban na yaƙi da matsalar tsaro kamar ta'addanci da tattatara bayanan sirri da amfani da jirage marasa matuƙa da cire abubuwan fashewa da aka dasa, da kuma atisayen ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD.

    Najeriya ta jima tana neman haɗin kai da taimakon manyan ƙasashen waje wajen yaƙi da ayyukan ƙungiyoyin ƴanbindiga masu ɗauke da makamai a ƙasar.

    A watan Fabrairu ne Amurka ta tura dakaru 200 zuwa Najeriya, domin ayyukan horas da sojojin Najeriya da taimaka musu da bayanan sirri.

  8. Isra'ila ta ce za ta ƙara tura ƙarin sojoji Lebanon

    Ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz, ya ce an bai wa rundunar sojin ƙasar, IDF umarnin abin da ya kira amfani da duka ƙarfinta a Lebanon idan aka sake kai wa sojojin ƙasar hari.

    A ranar Asabar aka kashe sojan ƙasar ɗaya a Lebanon duk da fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta.

    Mista Katz ya ce duk da yarjejeniyar, Isra'ila za ta ƙara tura sojojin ƙasa da na sama zuwa ƙasar.

    Wakilin BBC da ke Birnin Ƙudus ya ce yarjejeniyar na tangal-tangal bayan kisan sojan na Isra'ila da sojan kiyaye zaman lafiya na MDD, ɗan ƙasar Faransa.

    A ranar Talata, Shugaban Farana, Emmanuel Macron zai gana da firaministan Lebanon Nawaf Salam a birnin Paris game da batun tsagaita wutar.

  9. Shekarau ya koma APC bayan ficewa daga PDP

    Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya koma jam'iyyar APC bayan ficewarsa daga PDP.

    Shekarau ya koma APC ne tare da Sanata Bello Hayatu Gwarzo, wanda shi ma jigo ne a jam'iyyar PDP a Kano.

    Mallam Shekarau ya bayyana matakin nasa ne ranar Asabar a gidansa da ke unguwar Mundubawa a birnin Kano.

    Tsohon gwamnan ya ce ya ɗauki matakin ne bayan tuntuɓar masu ruwa da tsaki a siyasar jihar.

    A baya-bayan ne dai Shekarau ya gana da Shugaba Tinubu a fadarsa da ke Abuja.

  10. Gobara ta kashe mutum 20 a Indiya

    Ƴansandan a jihar Tamil Nadu da ke kudancin Indiya sun ce wata mummunar gobara - da ta tashi a wani kamfanin ƙera abubuwan tartsatsin wuta da ake amfani da su a wuraren bukukuwa- ta kashe aƙalla mutum 20.

    Bayanai sun ce gobarar ta raunata mutum shida.

    Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce an riƙa jin ƙarar abubuwan fashewa daga tazara mai nisa.

    Kawo yanzu ba a san abin da ya haddasa gobarar ba.

    Gobarar masana'antu ba sabon abu ba ne a Indiya, wanda ake alaƙantawa da rashin bin dokokin kariya ko rashin amfani da su.

  11. An gano wani bom da aka dasa tun yaƙin duniya na biyu a Faransa

    Kimanin jami'an ƴansanda 800 ne suka killace wani wuri a arewa maso yammacin birnin Paris yayin da ƙwararru ke ƙoƙarin kunce wani bom da aka gano an dasa shi a wurin tun lokacin yaƙin duniya na biyu.

    Dubban mazauna yankin aka kwashe daga wurin daga tazarar mita 450.

    An gano bom ɗin ne a yankin Colombes kwana tara da suka gabata, amma ƙwararru suka kasa cire shi a yunƙurinsu na farko saboda makunnarsa ta lalace.

    Shirin da ake yi yanzu shi ne tayar da shi a zurfin mita biyu.

  12. Labarai da dumi-dumi, Tawagar wakilan Amurka ta nufi Pakistan don tattaunawa da Iran

    Mun samu sabbin bayanai daga Shugaban Amurka, Donald Trump game da batun tattaunawar tsagaita wuta da Iran.

    "Wakilaina za su tafi birnin Islamabad na Pakistan - Za su isa can gobe da maraice, domin tattauanawa'', kamar yadda ya rubuta a shafinsa na sada zumunta.

    ''Muna son cimma yarjejeniya mai kyau kuma mai inganci, kuma ina fata Iran za ta amince da hakan, domin idan ba ta amince ba, Amurka za ta kai hari kan kowace cibiyar lantarkin da duka gadojin Iran,'' kamar yadda ya wallafa.

    Ya yi gargaɗin cewa ''babu wata lallaɓa da za a yi mana'', idan aka gaza cimma matsaya.

    Shugaban na Amurka ya ce zai ruguza duka gadoji da tasoshin lantarki cikin ''hanzari, kuma cikin sauƙi''.

  13. Mun duƙufa wajen ƙera makamai cikin hanzari a lokacin tsagaita wuta- Iran

    Kamfanonin dillancin labaran Iran masu alaƙa rundunonin soji da hukumomin tsaron ƙasar sun wallafa wani bidiyo da ke nuna yadda ake ci gaba da ƙera makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa a ƙasar da abubuwan harba makaman.

    A cikin bidiyon an ga kwamadan IRGC mai kula da dakarun saman ƙasar, Majid Mousavi na ziyartar ɗaya daga cikin cibiyoyin - wanda ke ƙarƙashin ƙasa.

    Baya ga bidiyon kamfanonin labaran sun kuma wallafa wani saƙo daga Majid Mousavi da ke cewa ''saɓanin Iran maƙiya ba su iya sake ƙera makamai a lokacin tsagaita wuta''

    ''A lokacin tsagaita wuta yawan ƙera makamanmu masu linzami da jirage marasa matuƙa ya ma fi sauri a kan yadda muke ƙerawa kafin fara yaƙin. Mun sani maƙiya ba za su iya ƙera wa kansu makamai ba...''.

    ''Sun yi asarar wannan lokaci, sun kuma yi rashin nasara a yaƙin, sun gaza a Hormuz, sun gaza a Lebanon sannan kuma a duka yankin ma gaba ɗaya'', in ji shi.

  14. 'Islamabad na shirin karɓar baƙuncin tattaunawar Amurka da Iran karo na biyu'

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayar da rahoton tsaurara matakan tsaro a Islamabad, babban birnin Pakistan.

    Yayin da jami'an Amurka da na Iran ke shirin ci gaba da tattauna batutuwan da suka sha bamban don kawo ƙarshen yaƙin Iran.

    Kawo yanzu dai ba a bayyana wuri da lokacin da za a gudanarwa da tattaunawar ba.

    Mashigar Hormuz - wadda ke cikin batutuwan da ɓangarorin biyu suka yi saɓani - ta kasance a rufe, saboda ci gaba da datse tasoshin ruwan Iran da Amurka ke yi.

    Iran ta ce jiragen ruwa za su wuce ta mashigar ne kawai bisa amincewar dakarun IRGC.

    Duka ɓangarorin biyu dai sun ɗauki tsauraran matsayi game da batun.

    Shugaba Trump ya jaddada cewa Amurka za ta bari jiragen Iran su shiga ko fita daga tasoshin ruwanta ne kawai idan aka cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin, yayin da Iran ta zargi Amurka da rashin mutunta yarjejeniyar wucin gadi da aka cimma.

  15. Fafaroma Leo ya gudanar da ibada tare da dubban mabiya a Angola

    Fafaroma Leo na gudanar da taron Ibada tare da dubban Kiristoci da suka taru a wani wuri a Kilamba da ke wajen Luanda, babban birnin Angola.

    Masu ibadar - waɗanda ke sanye da farar riga da hula mai launin ruwan ɗorawa, manne da hotonsa - sun cika wurin ibadar.

    Jagoran ɗariƙar Katolikan zai kuma ziyarci Muxima, wani babban wurin ziyarar ibada a ƙasar da ke kudancin Afirka.

    A ranar Asabar ne Fafaroman ya ziyarci ƙasar - a wata ziyara da yake yi a ƙasashen Afirka huɗu - inda ya gana da shugaban ƙasar.

    Fafaroman ya buƙaci shugabannin siyasa kada su ji tsoron bayyana aƙidar addininsu, yana mai cewa Angola za ta ci gaba idan ta yi amfani da hanyoyi daban-daban na dukiyar da Ubangiji ya huwace mata.

  16. Alamu sun nuna cewa babu jirgin da ya wuce ta mashigar Hormuz

    Yayin da Iran ta sanar da sake rufe mashigar Hormuz, a matsayin martani ga matakin Amurka na ci gaba da rufe tasoshin ruwanta.

    Shafin da ke bibiyar ziraga-zirgar jiragen ruwa na Marine Traffic ya nuna cewa babu jirgin da ya tsallaka mashigar, duk da cewa akwai jiragen da dama a gaɓar mashigar, musamman gaɓar tekun Oman da na UAE.

    Shafin kula da sufurin jiragen ya nuna cewa jirage da dama ne suka matsa kusa a mashigar a jiya, to amma suka dakata bayan da Iran ta sanar da sake rufe ta.

    Jiragen ruwa da dama ne ciki har da na dakon kaya aka bayar da rahoton dakarun Iran sun kai musu hari a ranar Asabar.

  17. 'Tump na amfani da yaƙin Iran don karkatar da hankalin jama’a daga badaƙalar Epstein'

    Tsohuwar mataimakiyar shugaban Amurka, Kamala Harris, ta ce Shugaban Amurka, Donald Tump na amfani da yaƙin Iran ne domin karkatar da hankalin jama’a daga sakin bayanan bankadar mashahurin mai lalata da ƙananan yaran nan Jeffrey Epstein.

    Yayin da take jawabi a wani taron mata na jam'iyyar Democrat a jihar Michigan, tsohuwar ƴan takarar shugaban Amurka a jam'iyyar Democrats ɗin ta ce firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ne ya yi wa shugaba Trump ingiza mai kantu ruwa wajen sanya shi shiga yaƙin.

    Sai dai ba ta bayar da hujjar iƙirarin nata ba, amma ta ce Amurkawa ba sa son yaƙin.

    Kawo yanzu dai babu wani martani daga Shugaba Trump kai-tsaye ga zarge-zargen na Mrs Harris, amma ya ce Isra'ila ''babbar ƙawa'' ce a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

    • "Ko mutane su so Isra'ila ko su ƙi ta, ta tabbatar da cewa ita babbar ƙawa ce ga Amurka. Suna da ƙwazo da ƙarfi da biyayya da kuma fikira, kuma ba kamar saura ba, da suka nuna mana halinsu na ainihi a lokacin yaƙi da na matsi, Isra'ila na yaƙi da himma, kuma sun san yadda za su yi nasara!"

    A makon da ya gabata ne Mrs Harris ta ce tana nazarin yiwuwar sake tsayawa takara, bayan da ta sha kaye a yunƙurin da ta yi a baya a hannun Mista Trump.

  18. Iran ta yi gargaɗin taƙaita zirga-zirga a Hormuz

    Shugaban Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, ya ce dakarun Iran ne ke da cikakken iko da mashigar Hormuz.

    Mista Qalibaf ya yi gargaɗin ci gaba da takaita zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar matsawar Amurka ba ta janye shingen da ta yi wa jiragen ruwan Iran ba.

    A baya-bayan rundunar sojin Iran ɗin ta riƙa mayar da jiragen da suka yu yunƙurin wucewa ta mashigar.

    Shugaba Donald Trump ya ce Amurka za ta ci gaba da hana jiragen ruwa zuwa ko fitowa daga Iran har sai an cimma yarjejeniya da Tehran.

  19. Assalamu alaikum

    Masu bibiyarmu barkanmu da hutun ƙarshen ako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku irin wainar da ake toyawa.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.