Har yanzu gwamnati ba ta tuntuɓe mu ba - Iyalan Shugaban Miyetti-Allah

Asalin hoton, Amnesty International
Iyalan shugaban ƙungiyar Miyetti-Allah, Alhaji Ardo Risku da aka kashe a jihar Benue sun koka cewa har yanzu gwamnati ba ta tuntuɓe su ba tun bayan faruwar lamarin, duk da alƙawuran da ake yi na cewa za a ɗauki mataki kamar yadda babban ɗan marigayin, Muhammad Idris ya shaidawa BBC.
Wannan na zuwa ne bayan da rundunar ’yansandan jihar Benue ta tabbatar da kama mutum 10 da ake zargi da hannu a kisan shugaban da wasu mutum uku, wanda aka harbe su a ranar Juma’a yayin da yake kan hanyarsa ta komawa gida daga wani taro da ya shafi tsaron jihar.
Gwamnatin jihar Benue ta bayyana cewa ta yi allawadai da kisan tare da ƙaddamar da bincike, amma iyalan marigayin sun ce ba su ji wani sakamako kai tsaye daga gwamnati ba
Sun bayyana cewa har yanzu suna jiran a tuntu be su domin ganin an yi musu bayani kan matakan da ake dauka.
Babban ɗan ya ce a ranar da aka kashe shi, ya je ya gaishe shi da safe, inda ya shaida masa cewa DPO na karamar hukumar Ohimini ya kira shi domin wani taro. “Sai ya kira wasu mutum uku su tafi tare, suka hau babur suka nufi inda za a yi taron,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa sun samu labarin kisan ne bayan sallar Juma’a, lokacin da suka ga mutane sun taru ana cewa an ga wasu mutane a bakin hanya an harbe su.
“Mun kira wayoyinsu ba su shiga ba, daga nan muka tafi wurin muka tarar ’yansanda sun riga mu, muka dauki gawarwakin,” in ji shi, yana mai korafin cewa, “tun daga lokacin DPO bai kira mu ba, gwamnatin ma ba ta tuntuɓe mu ba,” tare da jaddada cewa wanda aka kashe ba Fulani kaɗai ba ne, shugaba ne da ya shafi jama’a baki ɗaya.





















