Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi na kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa dangane da yaƙin Iran da kuma sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na 20/04/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman MINJIBIR

  1. Kotun ƙoli ta ɗage zaman sauraron shari'ar rikicin masarautar Kano

    Kotun ƙoli ta dage sauraron shari'ar rikicin masarautar Kano da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa tsakanin Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero da Sarki Muhammad Sanusi kan wane ne halastaccen Sarkin na Kano.

    A wani zaman da ta yi a Abuja, kotun ta ƙoli ta ɗage zaman sauraron shari'ar zuwa ranar 19 ga watan Afrilun 2027.

    A watan Mayun 2024 ne dai Gwamna Abba Kabiru Yusf ya rushe tsarin masarautar Kano na lokacin wanda ke da Sarakuna biyar ciki har da Sarki Aminu na Kano, bayan sauya dokokin da suka kafa masarautun na jiha.

    Tun lokacin ne Sarki Aminu Bayero ke ƙalubalantar sauye-sauyen inda suka je kotuna daban-daban kafin zuwa kotun ƙolin da ta ɗage zaman har na tsawon shekaru biyu.

  2. Da me Turkiyya za ta taimaka wa Najeriya ta fuskar tsaro?

    A ƙarshen makon da ya gabata ne Najeriya da Turkiyya suka amince da ƙulla yarjejeniyar tsaro tsakaninsu da nufin ƙarfafa rundunar sojin Najeriya a yaƙin da take yi da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.

    Cikin wata sanarwa da kakakin ma'aikatar tsaron Najeriya, Queeneth Iheoma-Hart ta fitar a ranar Lahadi ta ce yarjejeniyar ta ƙunshi cewa Turkiyya za ta kafa babbar cibiyar horon soji a Najeriya, a wani ɓangare na haɗin gwiwar tsaron tsakanin ƙasashen biyu.

    An cimma yarjejeniyar ce lokacin wata tattaunawar diplomasiyya tsakanin ministocin tsaron ƙasashen biyu a gefen taron diplomasiyya na 2026.

    Turkiyya na da ƙwarewar ƙera makaman yaƙi na zamani, musamman jirage marasa matuƙa.

  3. Benjamin Netanyahu ya ce za a hukunta sojan da ya rushe mutum-mutumin Yesu

    Firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya yi alawadai da sojan ƙasar wanda aka samu da laifin wulaƙanta mutum-mutumin Yesu Almasihu.

    Wani hoto ne dai ya rinƙa karakaina da ke nuna sojan na Isra'ila yana rushe mutum-mutumin da guduma.

    A wata sanarwa da aka wallafa a shafinsa na X, Benjamin Netanyahu ya ce ilahirin al'ummar Isra'ila sun kaɗu da jin faruwar al'amarin.

    Ya ce hukumomin soji suna gudanar da bincike dangane da al'amarin kuma za su ɗauki dukkannin matakin da ya kamata domin hukunta sojan.

  4. Ba mu yanke zuwa tattaunawa a Pakistan ba - Iran

    Har kawo yanzu ƙasar Iran ta ce ba ta kammala yanke shawara ba dangane da ko za ta aika wakilai zuwa tattaunawar da za a yi da Amurka a Pakistan ba.

    Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin gida ta Iran ɗin, Esmail Baghei ya shaida cewa "ya zuwa yanzu...ba mu da wani shiri na zango na biyu na tattaunawa."

    ShugabaTrump dai ya ce zai aika tawagar Amurka zuwa Pakista inda kuma mataimakin shugaban ƙasar, JD Vance zai jagoranta.

    Bayanai sun nuna cewa tuni tawagar ta Amurka ta kama hanya zuwa Pakistan domin halartar tattaunawar.

  5. Amurka ba ta shirya wa hulɗar jakadanci ba - Iran

    We can bring you more now from Iran's foreign ministry on whether it will attend the second round of peace talks with the US in Pakistan.

    Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghaei ya ce "A daidai lokacin da Amurka ke ikrarin son cimma huldar jakadanci da kuma shirinta na shiga tattaunawa da Iran, Amurka tana aiwatar da wasu halaye da suke ƙaryata ta, in shi.

    Ya ƙara da cewa Iran ba ta amincewa da wa'adi da wata ƙsa za ta ba ta idan dai har hakan ya keta muradun ƙasar tasu, kamar yadda Reauters ta faɗa, inda kuma ta ƙara da cewa cire batun nukiliya ba ma abin da za a iya tattaunawa ba ne.

    Batun dai abin da ya kamata a yi da sinadarin nukiliya na Iran na ɗaya daga cikin batutuwan da aka kasa amincewa da su yayin zaman tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu a Pakistan wanda aka ƙare dutse a hannun riga ranar 12 ga watan Afrilu.

  6. Askarawan Zamfara sun kama mota ɗauke da ababan fashewa

    Rundunar tsaro ta Asakarawan Zamfara ta ce ta kama wata mota da direbanta da ke ɗauke da wasu abubuwan fashewa da take zargin za a kai wa yanbindiga.

    Rundunar Askarawan ta ce ta kuma samu kuɗi sama da naira miliyan 13 a motar da ta kama a ƙauyen Bindin da ke ƙaramar hukumar Maru.

    Jihar Zamfara dai na fama da matsalar tsaro ta ƴanbindiga wadda ta ƙi ci ta ƙi cinyewa, inda rahotanni masu karo da juna ke nuna rasuwar dubban mutane da kuma ɗaiɗaita miliyoyi.

  7. Al'umma jihar Diffa a Nijar na fama da matsalar wutar lantarki

    Al'ummar jjiar Diffa ta jamhuriyar Nijar na kokawa da matsalar ɗaukewar wuta lantarki, lamarin da ya haifar da babbar koma baya ga al’amuran yau da kullum na jama’a.

    Tuni dai al’umma da ƙungiyoyin kare haƙƙin masu saye suka fara nuna damuwarsu tare da kira ga hukumomi su shawo kan wannan matsalar.

    Jamhuriyar Nijar dai na samun kaso kusan 60 na wutarta daga Najeriya mai maƙwabtaka tun bayan da alaka tsakanin ƙasashen guda biyu ta samu tangarɗa bayan juyin mulkin 2023 da ya hambarar da shugaba Mohamed Bazoum.

    Kafin tsamin dangantakarar tsakanin ƙasashen guda biyu dai kusan za a iya cewa jamhuriyar na samun wutarta kaso 100 daga Najeriya.

  8. China ta yi kiran sake zaman tattaunawa tsakanin Amurka da Iran

    Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen China ya yi kira ga sake zaman tattaunawa tsakanin Amurka da Iran sakamakon ƙwace jirgin dakon ƙasar Iran da Amurka ta yi mai suna Touska.

    Guo Jiakun ya shaida wa manema labarai cewa China ta bayyana damuwa kan "ƙwace da ƙarfi" na jirgin ruwan da sojojin ruwan Amurka suka yi, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito.

    A baya dai ma'aikatar harkokin wajen ta China ta bayyana toshe tashoshin ruwan Iran da "rashin sanin ya kamata".

    An ƙiyasta cewa China na sayen kusan kaso 90 na man Iran inda masu sharhi ke cewa toshe tashoshin na Iran da Amurka ta yi zai ƙara matsin lamba ga China domin ita ma ta matsa wa Iran lamba ta shiga tattaunawa da Amurka.

  9. Wane irin haɗari manhajar Claude Mythos ke da shi?

    A ƴan makonnin nan, duniyar manhajar AI ta cika da hayaniya bayan iƙirarin da babban kamfanin fasaha na Anthropic ya yi kan sabuwar manhajar Claude Mythos.

    Kamfanin yace ya samo wannan manhajar da za ta zarce ɗan adam a wasu sassa irin na kutse da kuma tsaron intanet, wannan ya janyo ce-ce-ku-ce tsakanin masu ruwa da tsaki, 'yan majalisa da kuma cibiyoyin kudade kan haɗarin da da za ta iya haifarwa a al'amuran intanet.

    An baiwa kamfanonin fasaha damar amfani da ita Mythos ta ƙarƙashin wani shiri da ake kira da Project Glasswing, wanda aka tsara domin baiwa Mythos damar juriya da kanta.

    Amma sauran abubuwan da kamfanin Anthropic ya zayyana cewa manhajar za ta iya ci waɗanda ba a taɓa gani ba ne a fanni AI ta yadda ba za a iya banbance aikinta ba da kuma na gaskiya ba.

  10. Shekarau ya ce buƙatar takara ce ta haɗa ƴan ADC wuri guda

    Tsohon gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekarau, ya ce son yin takara ne a gaban jiga-jigan da ke jagorantar tafiyar ADC, ba wai bukatar ciyar da kasar gaba ba.

    Yayin wata hira da sashen Hausa na BBC jim kadan bayan sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC a ranar Lahadi, tsohon gwamnan ya ce rashin yarda da akidun 'yan ADC din ne ya sa ya zabi rungumar tsohuwar jama'iyyarsa ta APC, wadda ke kan mulki a yanzu.

    A cewar Shekarau ''Na san da ADC tun wajen wata bakwai ko biyar da ake ta yin batunta, lokacin da su Atiku suka yi gangami har rubutu na yi na gaya musu cewa ni bana goyon bayan 'yan takara kadai su ce za su hadu wuri guda ba tare da jama'iyyunsu ba, idan ka kalle su dukkansu takara suke nema''

  11. Jam'iyyar tsohon shugaban Bulgeria, Rumen Radev na kan gaba a zaɓen majalisar dokoki

    Sakamakon farko na zaɓen yan majalisar dokokin Bulgaria, da aka gudanar ranar Lahadi ya nuna cewa jam’iyyar Progressive Bulgaria ta tsohon shugaban ƙasar Rumen Radev, na kan gaba da tazara mai yawa, kuma tana ma iya kafa gwamnati ita kaɗai.

    Mista Radev ya shugabanci Bulgaria daga shekarar 2017 har zuwa lokacin da ya sauka a watan Janairu.

    Ya yi kamfen ne kan kawar da cin hanci da rashawa. Ya soki mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, amma yana adawa da takunkumin da Tarayyar Turai ta kakabawa Moscow.

    Wani wakilin BBC ya ce masu jefa ƙuri’a sun ba Mista Radev damar kawo kwanciyar hankali bayan shafe shekaru na gwamnatocin gamin bambiza da suka rasa tabbas da kuma karfin gudanar da al'amura.

    Wannan shine zabe na takwas da aka yi cikin shekaru biyar kacal a kasar. dai.

  12. Firaiministan canada ya kudiri niyyar farfaɗo da alaƙarsa da Amurka

    Firaministan Canada, ya ce dangantakar tattalin arziƙi tsakanin ƙasarsa da Amurka ta yi tsami, kuma dole ne a tashi tsaye don farfaɗo da ita.

    A cikin wani jawabi ta bidiyo, Mark Carney ya ce harajin shigo da kaya da gwamnatin Turump ta ƙaƙaba sun yi matukar illa ga ma’aikata a masana’antun mota da na ƙarafa a ƙasar.

    Mark Caney, ya ce Canada na ƙoƙarin faɗaɗa hanyoyin saka jari da kuma ƙulla yarjejeniyoyin kasuwanci da sauran ƙasashen duniya.

    Dangantakar shugabannin biyu ta yi tsami tun bayan da Mista Carney ya zama firaminista a bara, kuma ƴan Canada da dama sun fusata da barazanar da Mista Trump ya yi ta mayar da ƙasarsu jiha ta 51 ta Amurka.

  13. Ƴansandan Louisiana sun ce mutumin da ya harbe yara 8 mahaifinsu ne

    ‘Yan sanda a jihar Louisiana a Amurka sun ce mutumin nan da ya harbe yara takwas ranar Lahadi shi ne mahaifin dukkansu ba wai daya daga cikin mutanen da aka harbe ba.

    An kuma raunata mata biyu a hare-haren da suka faru a birnin Shreve-port. Ƙaramin cikin wadanda aka kashe din shine dan shekara ɗaya kacal a duniya.

    Ƴan sanda sun kashe mahaifin da aka bayyana sunansa da Shamar Elkins, bayan sun bi sawunsa lokacin da ya yi ƙoƙarin tserewa a cikin wata mota da ya sata.

    Wannan shi ne hari mafi muni daga hare-haren bindiga dadi masu yawa da aka kai kasar cikin shekaru biyu.

  14. Pakistan na shirin karɓar baƙuncin Amurkawa da Iraniyawa domin tattaunawa

    Pakistan na shirin karɓar baƙuncin zagaye na biyu na tattaunawar zaman lafiya tsakanin Iran din da Amurka a wannan mako, sai dai har yanzu babu tabbaci ko Iran za ta halarta.

    Kafofin watsa labarai na gwamnati sun ce wakilan Tehran ba su da niyyar shiga tattaunawar, muddin Washington na ci gaba da toshe tashoshin jiragen ruwan ƙasar.

    Har yanzu dai manyan shugabannin Iran ba su ce ko kanzil ba, game da lamarin tukuna.

    Fadar White House ta ce tawagarta za ta kasance ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasar JD Vance.

    Shugaba Donald Trump ya yi barazanar lalata tashoshin wutar lantarki da gadojin Iran idan ba a cimma yarjejeniya ba.

  15. Iran ta sha alwashin ɗaukar fansar tare jirginta da Amurka ta yi

    Iran ta yi alƙawarin ɗaukar fansa bayan Amurka ta ƙwace wani jirgin dakon kayanta a Tekun gabas ta tsakiya.

    Sojojin Amurka sun ce sun budewa jirgin wuta, lamarin da ya lalata injinsa, bayan ya yi ƙoƙarin wucewa ta shingen da Amurkar ta kafa.

    Wakiliyar BBC ta ce shugaba Trump ya ce sojin ruwan Amurkar sun gargadi matuka jirgin da su dakata, amma suka yi kunnen kashi.

    Wani kakakin sojojin Iran ya bayyana kwace jirgin a matsayin fashin teku, kuma saba yarjejeniyar zaman lafiyar da ke aiki.

  16. Buɗewa

    Masu bibiyarmu barka da warhaka da fatan an yi wayi garin ranar Litinin lafiya wadda ake yi wa take da ko nasara na tsoron ki. Yau ma kamar kullum mun dawo muku da shafin namu na kai tsaye inda muke kawo muku muhimman labarai dangane da al'amuran yau da kullum.

    Da fatan za ku ci gaba da kasancewa da shafin da ma sauran shafukan sada zumunta na BBC Hausa.