Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 19/10/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran bubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 19/10/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Rabi'atu Kabir Runka

  1. Matawalle ya dawo da ƴanmajalisar Zamfara 8 da suka bar APC

    Ƴanmajalisar dokokin jihar Zamfara takwas da suka fice daga APC a kwanakin bayan sun sake komawa jam'iyyar bayan ganawarsu da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

    Tsohon gwamnan Zamfara kuma Ministan Tsaro na Ƙasa, Bello Matawalle ne ya jagoranci tawagar ’yan majalisar zuwa ganawar, kamar yadda sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya wallafa a shafukansa na sada zumunta.

    A yayin ganawar, ƴan majalisar sun sake tabbatar da goyon bayansu ga Shugaba Tinubu tare da alƙawarin ci gaba da kasancewa a cikin APC, abin da suka ce na nuna ƙudirinsu na ganin jam’iyyar ta ci gaba.

    A kwanakin baya ne wata sabuwar rigima ta ɓalle, inda lamarin ya kai ga cewa wasu ƴan majalisar dokokin jihar takwas suka sanar da sauya sheka daga jam'iyyar.

    Yan majalisar sun bayyana matakin nasu ne a zaman majalisar dokokin jihar da aka gudanar a birnin Gusau, inda aka karanta wasiƙun murabus ɗinsu a hukumance.

    Wannan ba shi ne karon farko da ake fama da taƙaddamar siyasa a jihar.

    A zaɓen shekara ta 2019 wani rikicin siyasa mai muni ya turnuƙe jam'iyya mai mulki, lamarin da ya sa kotu ta rushe dukkanin zaɓaɓɓun ƴansiyasa a jihar bayan zaɓe, tare da miƙa dukkanin muƙaman ga jam'iyyar adawa.

  2. Tsohon gwamnan jihar Delta ya rasu

    Tsohon gwamnan jihar Delta, Emmanuel Uduaghan ya rasu yana da shekara 71.

    Uduaghan, wanda ya yi gwamnan jihar daga 2007 zuwa 2015, ya rasu ne yau Litinin, kamar yadda iyalansa suka bayyana.

    Toju Anire Uduaghan ne ya sanar da rasuwar tsohon gwamnan cikin wata sanarwa da ya fitar a madadin sauran iyalai.

    Iyalan sun ce rasuwar tasa rashi ne babba saboda mutum ne da ya hidimtawa al'umma a Delta da ma Najeriya.

    "Cikin alhini muke sanar da rasuwar mahaifinmu, ɗan'uwanmu, kuma kawunmu, Dakta Chief Emmanuel Eweta Uduaghan, tsohon gwamnan jihar Delta, wanda ya rasu ranar Litinin 19 ga Oktoban 2026," kamar yadda sanarwar ta bayyana.

    Iyalan mamacin sun ce mutuwar Uduaghan ta bar babban giɓi a rayuwarsu inda kuma suka bayyana shi a matsayin mutumin da tasirinsa ya zarce iya danginsa na kusa.

    Kafin zama gwamna, Uduaghan ya taɓa riƙe muƙamin kwamishinan lafiya na jihar Delta daga 1999 zuwa 2003.

    Daga baya kuma ya kasance sakataren gwamnatin jihar Delta daga 2003 zuwa 2007 inda daga nan kuma ya zama gwamna a 2007.

    Ya yi wa'adi biyu a matsayin gwamna kafin ya bar ofis a 2015.

  3. Amurka ta gargaɗi ƴanƙasarta mazauna Gabas ta Tsakiya

    Ofisoshin jakadancin Amurka da ke ƙasashen Gabas ta Tsakiya da dama sun yi kira ga ƴan ƙasar su ƙara taka-tsantsan, suna mai nuni da abin da suka bayyana a matsayin "rincaɓewar yanayin tsaro" da kuma cikas ga tafiye-tafiye.

    Sanarwar tsaron da aka fitar daga ofisoshin jakadancin Amurka da ke ƙasashen yankin Tekun Fasha, da Isra'ila da Iraki da Labanon da Jordan, ta ce:

    "Amurkawan da ke Gabas ta Tsakiya a halin yanzu su ƙara taka-tsantsan saboda rikicewar yanayin tsaro a yankin."

    "A yi la'akari da yiwuwar soke jirage, rufe sararin samaniya ga zirga-zirgar jiragen sama, da kuma samun tangarɗa ga tafiye-tafiye."

    Gargaɗin ya ce akwai yiwuwar rikicin ya yi saurin bazuwa zuwa wasu sassan yankin.

    Haka kuma an shawarci 'yan ƙasar Amurka su riƙa bibiyar bayanan jirage tare da tanadar wasu hanyoyin tafiya na madadi idan wani yanayin gaggawa ya taso.

    Sanarwar ta kuma yi nuni da hare-haren da mayaƙan Houthi na Yemen suka kai kan Saudiyya.

    Filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa na Riyadh na ci gaba da kasancewa a rufe bayan da mutane 18 suka mutu sakamakon hare-haren da Houthi suka kai.

    An sake jaddada wa 'yan ƙasar Amurka muhimmancin ci gaba da sa ido kan bayanan zirga-zirgar jirage da kuma shirya wasu tsare-tsaren madadin idan wata matsala ta taso.

    A gefe guda, a jiya mayaƙan Houthi sun yi barazanar cewa za su kammala abin da suka fara nan ba da jimawa ba, lamarin da ya fuskanci kakkausar martani da barazanar ramuwar gayya daga Iran.

  4. Faransa ta ba magaddai ikon sanya dokar hana fita

    Ministan Tsaron Faransa, Sébastien Lecornu,ya ce firaministan kasar ya bai wa shugabannin ƙananan hukumomi ikon ƙaƙaba dokar hana fita na wani lokaci a wasu sassan ƙasar domin kare rayuka da dukiyoyi.

    ya ce ministan shari'a zai yi bayani daga baya kan matakan da gwamnati ke ɗauka domin hana sake barkewar tashin hankali.

    Ya ce wani gagarumin samame na bincike zai fara a yau a birnin Paris, inda masu bincike 200 za su nazarci bidiyon rikice-rikicen da suka faru a ƙarshen mako.

    Lecornu ya ce ana sa ran wannan bincike zai taimaka wajen gano waɗanda suka haddasa tashin hankalin da kuma ɗaukar matakan doka a kansu.

    Ya kuma ce firaministan kasar ya bai wa shugabannin ƙananan hukumomi ikon kakaba dokar hana fita na wani lokaci a wasu sassan ƙasar domin kare rayuka da dukiyoyi.

  5. Harin ƴan Houthi ya kashe gomman mutane a Yemen

    Akalla mutum 18 ne suka mutu a wani hari da mayaƙan Houthi suka kai wani sansanin horas da sojoji a yankin Shabwa na Yemen, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters wanda ya ambato majiyoyin gwamnati da na lafiya.

    Mayaƙan Houthi sun daɗe suna kai hare-hare kan dakarun da ke goyon bayan gwamnatin Yemen da ƙasashen ƙawancen sojoji ƙarƙashin jagorancin Saudiyya.

    Rahotanni sun ce mayaƙan Houthi sun harba makamai masu linzami guda biyar kan fadar Al-Mashiq, wadda suka bayyana a matsayin cibiyar ayyukan ƙawancen da Saudiyya ke jagoranta.

    Rahotannin baya-bayan nan, sun ce mutum biyar sun mutu sannan wasu da dama sun jikkata a harin da aka kai fadar Al-Mashiq, wadda ita ce hedkwatar gwamnatin Yemen da kasashen duniya ke amincewa da ita.

  6. Mota ta banke ƴar majalisar Australia a harabar ofishinta

    Firaministan Australia, Anthony Albanese, ya ce an kai hari kan wata yar majalisa bayan wata mota ta buge ta a wajen ofishinta.

    Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a Wangaratta da ke jihar Victoria, inda Helen Haines take kusa da ofishinta lokacin da motar ta buge ta.

    A wata sanarwa da iyalanta suka fitar, sun ce Helen tana samun kulawar likitoci. Sun kuma gode wa mutanen da suka taimaka da gaggawa, da ma'aikatan lafiya da suka kula da ita, da kuma 'yan sanda saboda matakin da suka ɗauka.

    'Yan sanda sun ce wata farar mota kirar Toyota LandCruiser ce ta bugi Haines, mai shekara 65, a wajen wani ofishi da ke titin Murphy da misalin ƙarfe 3:35 na rana.

    Sun ce bayan direban ya fito daga motar, an kama shi a wurin kafin a mika shi ga 'yan sanda.

    An kai Haines asibiti tana cikin mawuyacin hali. 'Yan sanda sun kuma ce sun gano wata wuƙa a cikin motar kuma sun ƙwace ta. A yanzu haka suna binciken domin gano ko an kai harin da gangan ne ko kuma tsautsayi.

  7. Dalilan da ke janyo yi wa yara mata auren wuri a Najeriya

    A baya-bayan nan uwargidan shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga iyaye da shugabanni da al'umma gaba ɗaya su haɗa kai wajen kawo ƙarshen auren wuri tare da tabbatar da kare haƙƙoƙin ƴaƴa mata.

    Mun tattaro wasu bayanai daga Lauya Huwaila Muhammed, mai rajin kare haƙƙin mata, kan dalilan da suka sa matsalar ke ƙara yawa a arewacin Najeriya.

  8. Abubuwa masu ban mamaki game da rayuwar Saddam Hussein

    Shugabannin da ake kallon su a matsayin masu mulkin kama-karya kan kasance da wasu halaye na daban, kamar son kaɗaici da kuma amfani da cikakken iko.

    Daga cikin fitattun shugabannin kama-karya a duniya akwai Hitler, Stalin, Mussolini, Franco da Muammar Gaddafi.

    Kusan kowane ɗaya daga cikinsu yana da wasu halaye ko ɗabi'u na musamman da suka bambanta da na sauran mutane.

    Saddam Hussein ma bai kasance daban ba.

    Ga abubuwa biyar da za a iya tunawa game da tsohon shugaban Iraq, Saddam Hussein.

    Lambar yabo daga UNESCO

    Saddam Hussein ya kasance mataimakin shugaban jam'iyyar Baath tsakanin 1968 da 1979.

    A wannan lokaci ya kawo sauye-sauye masu yawa a tsarin ilimi na Iraq.

    Alƙawarin tallafa wa marasa galihu a Amurka

    Kafin hare-haren 11 ga Satumbar 2001, alkiblar manufofin ketare na Amurka ba ta sauya ba.

    Ya bukaci a rubuta Alƙur'ani da jininsa

    A Musulunci, ba a yarda a yi amfani da jini a harkokin ibada ba, kuma ana ɗaukarsa a matsayin abin da aka haramta.

    Rayuwa cikin maraici da burin zama lauya

    Saddam Hussein ya tashi ne ƙarƙashin kulawar mahaifiyarsa kaɗai bayan mahaifinsa ya ɓace ba tare da wani bayani ba.

  9. Su wane ne ke samar wa ƴansiyasa kuɗin yaƙin neman zaɓe a Najeriya?

    A daidai lokacin da aka fara yaƙin neman zaɓen na shekarar 2027 a hukumance, hankali ya fara komawa ne kan irin rawar da kowace jam'iyya za ta taka wajen jan hankalin masu kada ƙuri'a.

    Sai dai wani bangaren da ba'a cika mayar da hankali ba shi ne hanyoyin da jam’iyyun siyasa da ’yan takararsu ke bi wajen samun kudaden yakin neman zabe da kuma yadda suke bayar da su.

    Maganar kuɗin kamfe ta sake tasowa ne bayan Dokar Zaɓe ta 2026 ta ƙara yawan kuɗin da doka ta amince wa ƴan takara su kashe a zaɓe.

    Masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa dai suna ganin irin kudaden da ke kashewa a yakin neman zabe na kara bude kofar cin hanci da rashawa da kuma karkatar da dukiyar gwamnati.

    Hukumar zaɓe ta ƙasar (INEC) tana da sashen da ke sanya ido kan yadda jam'iyyu da ƴan takara ke kashe kuɗi. Hukumar ta kan buƙaci jam'iyyu su gabatar da bayanan kuɗaɗen da suka shigo da kuma yadda aka kashe su bayan an kammala zaɓe.

  10. Babban jamiʼin Rasha zai kai ziyara Iran kan batun yaƙinta da Amurka

    Ministan harkokin wajen Rasha, Sergey Lavrov, zai kai ziyara Tehran a yau a karon farko tun bayan rikicin da ya shafi Amurka da Isra’ila da Iran. Gidan Talabijin din Iran ya sanar da cewa Lavrov zai kuma gana da shugaban Iran, Massoud Pezeshkian, a yayin ziyarar.

    Rasha na kokarin taka rawa mafi girma a matsayin mai shiga tsakani yayin da takun saka tsakanin Iran da Amurka ke ƙara tsananta.

    Mista Lavrov, wanda ake sa ran zai gana da ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce Moscow na ƙoƙarin kawo ƙarshen yaki tsakanin ɓangarorin.

    Lavrov ya halarci taron Tattaunawar Dabaru tsakanin Rasha da Majalisar Hadin Kan Kasashen Gulf (GCC) da aka gudanar a Bahrain, inda ya yi kira da a gudanar da tattaunawa kai tsaye tsakanin kasashen Gulf da makwabtan su, ciki har da Iraki da Jordan.

    Ziyarar Lavrov zuwa Iran na zuwa ne bayan da shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya bayyana a wata ganawa da Massoud Pezeshkian cewa Moscow a shirye take ta shiga tsakani domin sasanta rikicin.

    Ya ce ana iya gudanar da irin wadannan tattaunawa tare da yiwuwar shigar Kungiyar Hadin Kan Musulunci (OIC) da kuma Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

  11. Tattalin arzikin China ya haɓaka

    Tattalin arzikin China ya haɓaka, inda ya ƙaru da kashi hudu da rabi cikin ɗari a rubu'i na uku na wannan shekarar.

    Farfaɗowar ta samo asali ne sakamakon karuwar bukatar da ake da ita ta na'urorin kwamfuta da sauran kayan aikin da ake amfani da su wajen gina cibiyoyin tattara bayanai na fasahar (AI).

    Masu sharhi sun ce kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen waje na rufe giɓin da ake samu daga raguwar kuɗaɗen da ake kashewa a cikin gida.

    Wakiliyar BBC ta ce a cikin gida, mutanen China ba sa son kashe kuɗi yayin da Gwamnatocin ƙananan hukumomi ke fama da manyan basussuka, kuma rashin aikin yi ke kara yawa tsakanin matasa.

  12. Macron ya fara ziyarar ƙasashen gulf kan batun makamashi

    Shugaba Emmanuel Macron ya fara wata ziyara a ƙasar Kuwait yayin da gwamnatin Faransa ke ci gaba da ƙoƙarin shawo kan matsalar mummunar zanga-zanag da faru a ƙarshen makon nan.

    Har jiya Lahadi ba a tabbatar da cewa shugaban Faransa zai yi wannan tafiya ba, duk sai dai ya yi wasu kalamai da yammacin jiya Lahadi da suka nuna alamun zai yi tafiyar.

    Ya ce, "Na ɗauki matakai da dama a matakin ƙasa da ƙasa domin tabbatar da cewa muna da man fetur da iskar gas, kuma zan ci gaba da yin hakan ta hanyar ziyartar ƙasashen yankin Gulf domin tabbatar da wadatar kayan makamashinmu."

    Macron zai shafe kwanaki uku a yankin Gulf, bayan ya isa Kuwait da safiyar yau. Daga nan zai ziyarci Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), Bahrain da Qatar kafin ya koma Faransa a ranar Laraba.

  13. Jirgin Austria ya yi saukar gaggawa bayan tashinsa daga Isra'ila

    Rahotannin kafafen yaɗa labaran Isra'ila sun ce wani jirgin saman kamfanin Austrian Airlines ya yi saukar gaggawa a Sofia, babban birnin ƙasar Bulgaria, kimanin sa'a guda bayan tashinsa daga Tel Aviv zuwa Vienna.

    Jaridar Times of Israel ta ruwaito a daren Lahadi (16 ga Oktoba) cewa jirgin ya aika da saƙon neman ɗauki na gaggawa bayan an samu fargaba kan yiwuwar wata barazanar tsaro a lokacin tashin.

    A cewar rahotannin, ganin wani abu da ake zargi a cikin jirgin ne ya haifar da damuwar tsaro.

    Fasinjojin da ke cikin jirgin sun shaida wa kafafen yaɗa labaran Isra'ila cewa an ayyana yanayin gaggawa ne bayan an karɓi wani rahoto daga wanda ba a san ko wanene ba, wanda ya yi ikirarin cewa akwai bam a cikin jirgin.

  14. MDD za ta rage yawan tallafin abincin a Gaza

    Shirin samar da Abinci na Duniya ya ce ƙarancin kudade na tilasta masa rage tallafin da ya ke bai wa mutane a Gaza.

    Adadin mutanen da shirin na Majalisar Dinkin Duniya ke taimakawa a yankin Falasdinawa zai ragu da kusan mutane dubu dari biyar.

    Rage tallafin ya zo ne yayin da hunturu ke karatowa kuma yawancin iyalai - wadanda ke zaune a cikin tantuna na wucin gadi - har yanzu suna fama da rashin isasshen abinci duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka riga aka cimma.

  15. Sallama

    Masu shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wanna rana ta Litinin, mande tushen aiki ko da Nasara na tsaronki kamar yadda Hausa ke yi mata kirari.

    Rabi'atu Kabir Runka ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.