Gwamnatin Najeriya ta ce ba ta da shirin ƙara kuɗin wutar lantarki

Asalin hoton, @JosephOTegbe/X
Gwamnatin Najeriya ta ce ba ta da wani shiri na ƙara kuɗin wuta lantarki a halin yanzu.
Wata sanarwa da Bayo Onanuga ya fitar ta ambato Ministan Lantarkin ƙasar Joseph Tegbe na cewa abin da gwamnatin ta fi bai wa muhimmanci shi ne inganta samar da wutar lantarki, amfani da mitoci da kuma tabbatar da cewa ƴan Najeriya suna biyan kuɗin wutar da suka yi amfani da ita.
Kalaman nasa sun zo ne bayan damuwar da ake ci gaba da nunawa kan tsadar kuɗin lantarki, musamman bayan sauye-sauyen farashi da aka yi a baya ga masu amfani da wutar Band A.
Sai dai ministan ya ce gwamnati ba ta da wata manufa ta ƙara kuɗin lantarki fiye da yadda yake a yanzu.
"Burinmu shi ne inganta wutar lantarki, tabbatar da kowa ya samu mita, sannan 'yan Najeriya su riƙa biyan kuɗin wutar da suka yi amfani da ita," in ji ministan.
Ya ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da nazarin ƙarin hanyoyin da za su kare masu amfani da lantarki a wuraren da ba a cika samu ba da sauran matakai..




























