Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Gasar Kofin Duniya: Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai game da Gasar Kofin Duniya ta 2026 da aka kammala da sauran labaran wasannin BBC Hausa na ranakun 20 zuwa 26 ga watan Yuli, 2026

An kammala Gasar Kofin duniya ta 2026 Spain ta lashe komai

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Buhari Fagge

  1. Ina ganin ba sai an hukunta Leandro Paredes ba - Gavi

    Dan wasan tsakiya na Spain Gavi ya ce shi bai amince a dakatar da dan wasan Argetina ba Leandro Paredes saboda fito na fiton da ya yi a filin wasa ba, bayan kammala wasan ƙarshe na Gasar Duniya.

    Yan wasan Aregentina Parades da Molina da Almada da kuma mai taimakawa koci Roberto Ayala duka an gansu da hannu cikin rikicin lokacin da Spain ke murnar kammala gasar da ta ci 1-0.

    An ga Parades ya shaƙi wuyan Eric ɗan wasan Spain da kuma kayar da Gavi yana yunkurin taushe shi yayin da shi ma Almada ya taimaka masa.

    Parades bayan ya kayar da ɗan wasan na Barcelona ya nemi ya dake shi a fuska.

    Tuni Fifa ta kafa kwamitin bincike kan lamarin, tare da alƙawarin tara mai tsoka kan duk wanda aka kama da laifi.

    "Ban ga wani abun ɓacin rai ba, ba sai an dakatar da shi ba (Parades), kamar yadda Gavi ya shaida wa jaridar El Partidazo de COPE.

  2. Sabbin fuskokin masu horarwar da za a gani a Nahiyar Turai

    Bayan kammala gasar Kofin Duniya da aka yi a Amurka da Mexico da kuma Canada, rashin nasarar da wasu ƙasashe suka yi na neman zama sanadin kawo sauye-sauye a tawagoginsu.

    'Yan wasa da dama sun ajiye takalmansu kazalika masu horaswa. Amma wannan maƙalar za ta yi duba kan wasu ƙasashe da ke neman kawo sauyi a fannin horarwarsu.

    Faransa:

    Tun gabanin rashin nasarar da ta yi a kofin duniya ake yaɗa jita-jitan cewa za a sauya mai horarsa da tawagarta.

    An ta cewa tsohon kocinta Zinedine Zidane zai maye gurbin kocinta na yanzu Didier Deschamp.

    Amma bayan rashin nasarar da ta yi a hannun Spain managa ta ƙara ƙarfi, manyan jaridu turai ciki har da Fabrizio Romano sun rawaito cewa Zidane zai jagoranci Faransa har zuwa June 2030.

    Wannan na nufin zai jagoranci ƙasar zuwa manyan gasar da suka haɗa da Nations League 2027 Euros 2028 da kuma Kofin duniya 2030.

    Zidane ya yi wasa da Deschamp a 1998, tawagar da suka ci kofin duniya bayan doke Brazil 3-0.

    Jurgen Klopp:

    Bai zo da mamaki ba jin cewa Jurgen Klopp zai zama kocin Jamus na gaba ba, saboda daɗewa da ya yi ba tare da wata ƙungiya da yake jagoranta ba.

    Babban abin da ya tabbatar da burinsa na jan ragamar Jamus shi ne tattaunawar da aka yi tsakanin Hukumar kwallon Kafa ta Jamus da tsohon kocin tawagar Julian Negelsman ya ce sun cimma matsaya da hukumar kan ajiye aikinsa.

    Hukumar ta tabbatar da cewa Jurgen Klopp zai jagoranci Jamus sai dai ba a bayyana tsayin lokacin ba da kuma lokacin da zai fara aiki.

    Tun daga 2014 da Jamus ta ci Kofin Duniya a hannun Argentina, Jamus ba ta ƙara cin wasa ba a mataki na sili daya kwale.

    Pep Guardiola:

    Aikin gaban Pep Guardiola zai zama babba ne, domin zai farfaɗo da tawagar da ake ganin ta zama mushen gizaga.

    Hukumar kwallon ƙafa ta ITaliya ta aike da wakilai da suka haɗa da mai koyar da dabarun wasannin ƙasar wanda tsohon dan wasanta ne Paolo Maldini da mai bashi shawara Leonardo sun je har Barcelona sun tattauna da Guardiola na tsawon kwanaki uku.

    Pep wanda ya yi nasara a zamansa a spain lokacin da ya jagoranci Barcelona da zamansa a Jamus inda ya yi kocin Beyern Munich sai kuma inda da ya horas da Manchester City, watakila Itali ta zama inda zai yi kocin na gaba.

    Zai iya zama koci na biyu dan wata ƙasar da zai jagoranci Italiya kuma na farko tun shekarun1960.

    Tsofaffin 'yan wasan ƙasar irinsu Roberto Mancini da Andrea Pirlo suma sun nuna shaawarsu kan aikin.

    Guardiola mai shekara 55, aikin ba zai bashi wuya ba saboda yana jin yaren Italiya sosai, lokacin da ya zauna a ƙasar tsakanin shekarar 2001 zuwa 2003.

    Mark van Bommel:

    Mark van Bommel tsohon dan wasan Barcelona kuma ɗan asalin Netherland rahotanni na cewa zai karbi aikin horas da Belgium na tsawon shekara biyu zuwa watan Yunin 2028.

    Belgium ma kamar sauran ƙasashen da suka fuskanci koma baya a gasar kofin Duniya ta kai matakin wasan kusa da dab da naƙarshe a gasar inda gwarzuwar gasar Spain ta doke ta da ci biyu da ɗaya.

    Rudi Garcia wanda tsohon dan wasan Faransa ne shi ne ya kai Belgium kofin duniya, kuma ya kabi aikin ne a 2025.

    Ana sa ran Van Bommel zai jagoranci tawagar zuwa shekarar 2028, bayan gasar Euro.

  3. Nijar da Mali da Burkina Faso na son karɓar baƙuncin Afcon

    Ƙasashen Jamhuriyar Nijar da Mali da kuma Burkina Faso sun miƙa takardar haɗaka ta neman karɓar baƙuncin gasar ƙwallon ƙafa ta Afirka, Afcon a shekarar 2032.

    Jami'an ƙasashen sun gabatar da takardar buƙatar ne ga shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF), Patrice Motsepe.

    Shugabannin hukumomin kula da ƙwallon ƙafa na ƙasashen sun gana da Motsepe a birnin New York na Amurka a ranar Asabar, tare da Kanar Djibrilla Hima Hamidou, wakili a hukumar ƙwalllon ƙafa ta duniya FIFA, kuma ɗaya daga cikin manyan hukumar ƙwallon ƙafa ta Jamhuriyar Nijar.

    A ranar Talata ne hukumar ƙwallon ƙafa ta Mali (FEMAFOOT) ta sanar da ganawar da aka yi, inda ta ce za a yi amfani da gasar wajen bunƙasa "haɗin kai tsakanin ƙasashen yankin da kuma haɓɓaka ƙwallon ƙafa a Afirka."

    Miƙa takardar neman karɓar baƙuncin ta biyo bayan nuna sha'awar hakan da ƙasashen AES suka yi.

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Mali ta ce za ta yi aiki tare da sauran ƙasashen biyu wajen yin "ingantaccen shirin karɓar gasar" wanda zai kawo sabon ci gaba a harkar ƙwallon ƙafa a nahiyar.

    Har yanzu hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka ba ta riga ta zaɓi ƙasar da za ta karɓi baƙuncin gasar ta 2032 ba, gasar da ake yi duk bayan shekara biyu, tana tattara zaƙaƙuran masu taka leda na nahiyar.

    A shekarun baya-bayan nan ne ƙasashen Mali da Nijar da Burkina Faso suka kafa ƙungiyar ƙasashen yankin Sahel ta AES bayan ficewa daga ƙungiyar haɓɓaka tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka (Ecowas), bayan jerin juyin mulki a ƙasashen.

    AES ta ce manufarta ita ce bunƙasa haɗn kai tsakanin ƙasashen uku, musamman a ɓangaren tsaro da kasuwanci da kuma tattalin arziƙi.

  4. Foden ya tsawaita kwantaraginsa a Man City

    Dan wasan Manchester City Phil Foden ya sabunta kwantaraginsa a ƙungiyar na tsawon shekara huɗu zao ci gaba da zama a ƙungiyar har zuwa 2030.

    Poden mai shekara 26 kwantaraginsa za ta ƙare ne a kaka mai zuwa, amma ya amince ya tsawaita ta ya yi aiki tare da sabon kocin ƙungiyar Enzo Maresca.

    Dan wasan ya fara bugawa babbar tawagar Manchester City lokacin yana ɗan shekara 17 ƙarƙashin tsohon kocin ƙungiyar Pep Guardiola, daga nan ya buga wa City wasa 369 ya ci Premier shida da Champion Lig ɗaya da kuma FA biyu.

    Kocin Ingila da ya jagorance ta zuwa kofin duniya Thomas Tuchel bai tafi da shi gasar ba, saboda rashin ƙoƙarinsa a kakar da aka ƙare, wadda ya fara wasa 23 a cikinta.

    Forden ya ce "ya ƙagu ya fara wasa" ƙarƙashin Maresca wanda ya yi aiki tare da tsohon kocin ƙungiyar Guardiola.

  5. Martinez na shirin taka leda a Argentina

    Mai tsaron ragar Argentina Emi Martinez ya ce yana duba yiwuwar ko lokacin da zai hakura da buagawa ƙasarsa Argentina kwallo ya yi, bayan rashin nasarar da suka yi 1-0 a hannun Spain a wasan ƙarshe.

    Dan wasan mai shekara 33 ya yi nasara a wasanni 67 da ya bugawa ƙarsarsa kuma ya buga duka wasannin da suka yi guda takwas a gasar kofin duniya ba tare da an sauya shi ba ko sau ɗaya, kuma kwallo takwas kawai aka ci shi.

    Shi ne ya lashe kofin duniya a 2022, ya lashe kyautar golan da ya fi kowanne a gasar, kuma ya taka rawar a zo a gani a cikin gasar baki daya.

    Shi ne golan Aston Villa tun 2020, kuma kwantaraginsa zai ƙare ne a 2029, ko da yake ana alaƙanta shi da tafiya Juventus a wannan kakar.

  6. Lokacin saukar shugaban Fifa ya yi - in ji shugaban La Liga

    Shugaban gasar La Liga ta Spain Javier Tebas ya yi kira ga shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Gianni Infantino ya sauka daga muƙamunsa.

    Ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da wani gidan jari na La Gazzetta da ke Italiya, yana cewa Infantinno ' na neman lalata hukumar Fifa'.

    Ya kuma soki yadda ake hutun shan ruwa ana tsaka da wasa a yayin gasar, da kuma wani hutu na gaira babu dalili da aka je a wasan ƙarshe lokacin da aka kammala hutun mintina 45 na farko, ka zalika ya yi batun janye jan katin da aka yi wa dan wasan Amurka Folarin Balogun da kuma shirin mayar da gasar kofin duniya ta ƙasashe 64.

    Lokacin da aka tambaye shi ya kamata Infantino ya ajiye aiki sai ya ce " a ra'ayina eh, ya kamata, ina ganin lokacinsa ya yi."

  7. Fifa ta fara bincike kan kan faɗan da aka yi bayan wasan karshe

    Hukumar kwallon ƙafa ta duniya Fifa za ta fara bincike kan mummunar halayyar ta 'yan wasan Argentina suka nuna bayan kammala wasan ƙarshe na Kofin Duniya.

    Fifa ta nemi kwamitin ladabtarwarta ya samar da wani kwamiti da zai bincike kan lamarin domin tabbatar da abin da ya faru a filin wasa na MetLife.

    Duk ɗan wasa ko koci da aka samu da hannu cikin lamarin za a dakatar da shi, kuma za a ci tarar hukumar kwallon ƙafa ta Argentina.

    Bayan rashin nasarar da ta yi a hanun Spain 1-0 a ranar Lahadi, wasu 'yan wasa da kuma mutanen tawagar kocin Argentina sun kama rikici da yan wasan Spain lokacin da suke murnar cin wasansu.

    Nahuel Molina da Leandro Parades da Thiago Almada da mataimakin kocin Roberto Ayalla duka an gansu cikin rikicin.

  8. Shugaban Uefa ya ƙauracewa wasan ƙarshe na Kofin Duniya don adawa da Fifa

    Shugaban hukumar kwallon ƙafa ta Turai Aleksander Ceferin bai halarci wasan ƙarshe ba na kofin duniya da aka yi tsakanin Spain da Argentina domin nuna adawa da Fifa.

    Ka zalika bai je wasan farko na gasar ba da aka yi tsakanin Mexico da Afrika ta Kudu a Mexico City, maimakon haka ya wuce New Jersey ne abinsa a ranar Lahadi, kuma hakan na faruwa ne sakamakon wasu hukunce hukunce da Fifar ta yi wanda yake adawa da su.

    Uefa ta nuna rashin jin daɗinta a fili bayan janye wa dan wasan gaban Amurka Folarin Balogun dakatarwar jankatin da aka ba shi saboda sa bakin da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi.

    Wannan na daya daga cikin abubuwan da suka harzuƙa shugaban Uefa ya ƙi zuwa kallon wasan ƙarshe.

    Uefa ta soki matakin da Fifa inda ta bayyana shi da abin takaici da ba a yi zato ba wanda babu dalilin yin shi.

  9. Cin da aka yi mana akwai raɗaɗi in ji Messi

    Dan wasan gaban Argentina kuma kyaftin ɗin tawagar Lionel Messi ya ce "akwai raɗaɗi" a rashin nasarar da suka yi kuma "zai ɗauki lokaci mai tsawo kan ya warke", yana magana ne kan 1-0 da Spain ta ci su a wasan ƙarshe na Kofin Duniya da aka kammala.

    Dan wasan Spain na gaba Ferran Torres ne ya jefa kwallon a raga a lokacin da aka ƙara na minti 30 bayan cikar minti 90 da aka saba na wasa, wanda hakan ya kawo ƙarshen riƙe kofin da Argentina ke yi tun 2022.

    Har da wannan Messi ya yi rashin nasara biyu a wasan ƙarshe da ya taɓa zuwa, har da na 2014 a hannun Jamus.

    Dan shekara 39, da kamar wuaya ya halarci gasar ta 2030, ko da yake har yanzu bai bayyana ko zai hakura da bugawa ƙasarsa wasa ba.

    Messi ya fashe da kuka bayan tashi daga wasan lokacin da aka sa masa sarƙar da ake bayarwa ga wadanda suka buga wasan ƙarshe.

    "Ina taya Spain murna da lashe kofin nan da ta yi, ta zama gwarzuwar duniya", in ji Messi.

    An yi ta sukar Fifa bisa zargin cewa tana dauke kai kan Argentina a gasar da aka kammala, sai dai daga Fifa har Argentina babu wanda ya ce uffan kan zarge-zargen.

  10. Tsohon ɗan wasan Liverpool da Newcastle Keegan ya rasu

    Tsohon ɗan wasan Ingila kuma koci Kevin Keegan ya rasu yana da shekara 75.

    Rasuwar tasa na zuwa ne bayan sanar da kamuwa da ya yi da ciwon Kansa da ta kai mataki na huɗu.

    Daya daga cikin 'yan wasan Ingila da suka fi samun kyautuka a duniya, Keegan ya buga kwallo a Scunthorpe United, Liverpool, Hamburg, Southampton da kuma Newcastle lokacin da yake kan ganiyarsa.

    Daga baya ya zama kocin Newcastle da Fulham da Ingila da kuma Manchester City.

    A watan Yuni ne Keegan ya bayyana cewa yana fama da kansa a mataki na huɗu, wanda shi ne mataki mafi haɗari da ke nuna kansar ta bazu zuwa wasu sauran sassan jikinsa.

  11. Colossal Cubarsi

    Pau Cubarsí yana gaban duk wani dan wasa da ya halarci Kofin Duniya wajen:

    • Ya taɓa kwallo sau (139)
    • Ya ba da fassin ba tare da matsala ba sau (121)
    • Kashi (96%) na kwallo da ya ke bayarwa na zuwa daidai
    • Hana fassin kaiwa inda ake so (21)
    • Cire kwallo (6)
  12. 'Yan Spain na ci gaba da murna a Madrid

    Daren jiya tamkar rana ya kasance ga magoya bayan kwallon ƙafa a Spain.

    Ko mutum na kallon kwallo ko baya yi, dole yasa wani gagarumin lamari na faruwa a kasar.

    Haka aka wayi gari, kuma ana ci gaba da jiran tawagar ƙasar ta dawo daga Amurka.

    Wata murnarma sai sun iso.

  13. Spain ta isa gida

    Bayan kammala gasar Kofin Duniya babu abin da yake yin saura sai kuma kowa ya kama gabansa.

    Tawagar zakarun gasar Spain kamar kowa, ita ma ta nufi gida, kuma tuni ta isa.

    Ga dai yadda ta isa gida cikin hotuna.

    Kyaftin Rodri ɗauke da kofin duniyan a saman matattakalar jirgin, yayin da kocin tawagar Luis de la Fuente, ke tsaye a gefensa, suna dagawa masoya hannu.

    Wannan je motar da aka turo domin ta kwashi 'yan wasan Sifaniya da suka dawo daga gasar kofin duniya.

    Yan wasan Sifaniya na fitowa daga cikin jirgin, bayan kyaftin dinsu Rodri ya buɗe musu hanya.

    Duka 'yan wasan sun sakko daga jirgi suna jiran azo a ɗauke su.

  14. Duk da ya ci kwallo takwas amma bai ci kyauta ba

    Yadda gasar Kofin Duniya ta ƙare ga Messi ba abu ne mai dadi ba.

    Dan wasan mai shekara 39 ya fara gasar ne da cin kwallo uku rigis a wasan farko da suka buga da Algeria suka ci 3-0, inda ya yi kunnen doki da dan wasan Jamus Miroslav Klose da ke da kwallo 16 a gasar kofin duniya.

    Ya wuce nan har ya kai ga kafa tarihin wanda ya fi kowa cin kwallo a gasar kofin duniya ya kai kwallo 21.

    Amma damar ta kuɓuce masa ne bayan ɗan wasan Faransa Kylian Mbappe ya ci kwallo biyu a wasansu da Ingila da suka yi 6-4, ya haɗa kwallo 10 a gasar ya kuma zama wanda ya fi cin kwallo a duka gasar ta maza da kwallaye 22.

    Wannan ne ya hana Messi kai wa ga lashe gasar.

  15. Messi bai samu dama ba

    A cikin minta 15 da fara wasa tsakanin Spain da Argentina, Lionel Messi sau daya ya iya samun damar taba kwallo tun da aka fara.

    Sau 54 kacal ya iya taba kwallo cikin mintina 120 da aka yi har da na ƙarin lokaci - kuma bai iya taɓa kwallo ba ko sau daya a cikin yadi na 18 na Spain a duka wasan.

  16. Abin da ya yi bai dace da kwallon kafa ba - Alan Shearer

    Tsohon dan wasan Ingila Alan Shearer ya yi martani kan abin da dan wasan Argentina [Leandro] Paredes ya yi bayan kammala wasan karshe na kofin duniya.

    "Shi ne ya je ya same su. Abin da ya yi baya cikin kwallon kafa.

    "Mun san muhimmancin kofin a wajensu, mun san zafin rashin nasara. Amma akwai yadda ake tafiyar da rashin nasara, in ji Alan.

    Ya ce an ta ganin Argentina suna irin wannan wasan na rashin girmama abokan wasansu.

    Ya ce abin da dan wasan ya yi bayan an tashi ba daidai ba ne.

    "Sun doke kasashe da dama a baya, saboda me su ba za a doke su ba". in ji dan wasan.

    We know how much it means to them and we know how much it hurts to lose, but there is a way to lose.

    Too many times we have seen that from Argentina.

    The reaction after the final whistle is terrible.

  17. Mbappe ya lashe kyautar wanda ya fi cin kwallo sau biyu a jere

    Kyauta ɗaya kacal da Spain ba ta mamaye ba ita ce ta wanda ya fi zira kwallaye a gasar.

    Dan wasan Faransa Khlian Mbappe ne ya lashe gasar karo na biyu kenan a jere.

    Dan wasan gaban ya ci kwallo 10 a wasa takwas da ya buga inda ya zarce Messi da lwaoo biyu.

    Ya ci kwallo takwas a gasar 2022 da aka yi a Qatar hakan ya sa a nan ma ya lashe irin kyautar a karo na farko.

    Dan Real Madrid din shi ne dan wasa na farko da ya fara cin kwallo 10 a gasa ɗaya a tarihi tun bayan dan wasan Jamus Gerd Muller a 1970.

    Magabacinsa a Faransa Fontaine da ya taba cin 13 a 1958, sai kuma na Hungary Sandro Kocsis da ya ci 11 a 1954, sune kawai suka taba cin kwallayen da ya fi na Mbappe a gasa ɗaya.

    Ya kuma zama wanda ya fi kowa cin kwallaye a tarihin gasar Kofin Duniya inda ya ci kallo 22 - yana saman Messi wanda ya ci kwallo 21, ya samu damar hakan ne bayan cin kwallo biyu a wasan neman na uku da suka yi da Ingila da aka tashi 6-4.

  18. Spain ta wawashe kyautukan Kofin Duniya

    Bayan mamayar da Spain ta yi a cikin filin wasa, mamayar ta ci gaba har zuwa bayan fage.

    'Yan wasan Spain sun cin ye kyautukan gasar, inda Kyaftin Rodri ya lashe dan wasan da ya fi kowa a gasar.

    Mai tsaron ragar tawagar da aka sa wa kwallo ɗaya kacal a gasar ya zama wanda ya fi kowa hazaka.

    Dan wasan bayan kasar And Pau Cubarsi mai shekara 19 ya zama dan baya mafi ƙoƙari a gasar.

  19. Yadda aka ga rana haka aka ga dare a Spain

    Ba a yi bacci ba a manyan biranen Sifaniya irinsu Madrid da Barcelona da dai sauransu.

    Yadda aka ga rana haka aka ga dare a biranen.

    Wata murna da suka kwashe shekaru 16 rabonsu da ita, kuma irinta ce ta biyu a tarihin kasar a Kofin Dunya.

  20. Matashiya kan wasan karshe na duniya

    Bayan wasanni 104 da aka buga cikin kwanaki 39 tsakanin ƙasashe 48, Spaniya ce ta lashe kofin bayan doke mai rike da kofin Argentina da ci 1-0.

    Dan wasan Barcelona Ferran Torres ne ya ci kwallon a mintina na 106 bayan Nico Williams ya dawo masa da ita a ka shi kuma ya maka ta cikin ragar kuma ta kwanta.

    Wannan nasara ce da kocin Spain Luis de la Fuente da ke rike da kofin Europe ya cancanci samu, bayan mamaye wasan da ya yi kan garzuwar Copa America.

    Argentina ta kammala wasan da mutum 10 bayan korar dan wasanta na tsakiya da ke wasa a Chelsea Enzo Fenendez, wanda ya samu katin gargaɗi guda biyu.

    Ferran Torres ya zama tamkar Iniesta da ya ci wa Spain kwallon da ta lashe Kofin Duniya da ita a 2010.