Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 25/08/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 25 ga watan Agusta, 2026.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi

  1. Katafaren jirgin ruwan yaƙin Amurka zai je Thailand don hutawa

    Jirgin ruwan dakon jiragen yaƙi na Amurka USS Abraham Lincoln zai isa tashar jiragen ruwa a Thailand a mako mai zuwa bayan kwashe tsawon lokaci a cikin ruwan teku a Gabas ta Tsakiya, in ji hukumomin Thailand.

    Wannan na zuwa ne bayan rahotannin nuna damuwa game da mummunan yanayin da sojojin da ke cikin jirgin ke ciki, wanda ya hada da taɓarɓarewar lafiyar ƙwaƙwalwa da sauran abubuwa.

    Wani ɗan majalisar dokokin Amurka na jam’iyyar Democrat ya ce jirgin ya kafa tarihin kwashe sama da kwana 200 a kan teku ba tare da hutawa ba.

    Jami’in gwamnatin Thailand wanda bai so a bayyana sunansa ba ya ce kimanin sojoji da ma’aikatan jirgin 5,000 za su isa Thailand inda za su huta, bayan shafe tsawon lokaci yana aiki a teku.

    Rundunar sojin Thailand ba ta yi martani ba a lokacin da aka bukaci tsokacinta kan lamarin.

  2. Ya kamata a yi wa Najeriya addu’a kan matsalar tsaro – Tinubu

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya buƙaci al’ummar ƙasar su dage wajen yin addu’o’in magance matsalar tsaro da sauran bala’o’i da ƙasar ke fama da su.

    A cikin saƙon da ya fitar na ranar Maulidi ta hannun mai taimaka masa kan yaɗa labarai Bayo Onanuga, Tinubu ya ce “ya kamata Musulmai su dage wajen yin koyi da koyarwar Annabi Muhammad.

    “Akwai darussa masu kyau da za a koya daga ɗabi’un (Annabi Muhammad) na dagewa, juriya, haƙuri da juna, ƙankan da kai da rashin nuna son kai,” in ji Tinubu.

    Haka nan shugaban ya buƙaci malaman addini a ƙasar su yi amfani da lokacin wajen yi wa ƙasar addu’a tare da yi wa al’umma huɗubar koyi da Annabi Muhammad a al’amuransu da suka jiɓanci kishin ƙasa.

    A ranar Litinin ne al’ummar Musulmi a faɗin duniya ke murnar ranar haihuwar Annabi Muhammad.

    Hakan na zuwa ne yayin da Najeriya ke ci gaba da fuskantar matsaloli na tsaro da tattalin arziƙi, yayin da alummar ƙasar ke kokawa kan tashin farashin man fetur da kayan masarufi waɗanda suka ta’azzara tun bayan hawan Bola Tinubu mulki a shekarar 2023.

  3. Gwamnatin Indiya za ta fitar da albasa daga rumbu don sassauto da farashi

    Gwamnatin ƙasar Indiya ta ce za ta fitar da albasar da ta jibge a rumbunanta a wani yunƙuri na sassauta farashin albasa da ya yi tashin gwauron zabi a ƙasar.

    An saba cewa farashin albasa kan tashi a ƙasar Indiya cikin watan Agusta sanadiyyar yadda ake matuƙar buƙatar kayan-gwari domin bukuwa - to sai dai a wannan shekarar farashin ya kusa nunka yadda aka riƙa sayen ta a shekarar da ta gabata.

    Gwamnati za ta yi amfani da jiragen ƙasa wajen jigilar albasar zuwa birane kamar Chennai da Kochi, kuma ta ce motoci za su riƙa zagayawa suna sayar da alabasar a unguwannin Delhi, babban birnin ƙasar.

  4. An ga wani jirgin sojin Amurka ya sauka a Rasha

    Fadar shugaban ƙasar Rasha ta ƙi cewa uffan game da rahotannin da ke cewa wani jirgin jigilar kaya na sojojin Amurka ya sauka a filin jirgi na Vnukovo da ke birnin Moscow.

    Manhajar bibiyar zirga-zirgar jiragen sama ta FlightRadar ta nuna jirgin na barin sansanin sojin sama na Andrews Airbase da ke jihar Maryland a Amurka sannan ya sauka a Riga, babban birnin ƙasar Latvia, kwana biyu da suka gabata.

    Akwai raɗe-radin da ke yawo a kafafen yaɗa labarai na Rasha cewa ko dai za a yi musayar fursunoni ne ko kuma watakila jirgin ya kai jakadan shugaba Donald Trump ne domin tattaunawa kan Ukraine.

    A baya akwai rahotannin da ke cewa jakadan Trump, Steve Witkoff da Jared Kushner za su iya halartar bikin ranar ƴanci ranar Litinin a birnin Kyiv, sai dai ba a ga hakan ba.

  5. Isra'ila na ci gaba da kashe mutane a Gaza - MDD

    Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa hare-haren Isra'ila na ci gaba da kashe fararen hula a Gaza.

    Ma'aikatan lafiya a yankin sun ce an kashe wata yarinya ƴar shekara 10 da kuma wani yaro ɗan shekara huɗu a cikin kwana ɗaya da ya gabata.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ba ta da masaniya game da kisan yarinyar, inda ma'aikatan lafiya da dangi suka ce harsashin bindiga ya samu Amal Abu Khater a baya sa'ilin da take zaune tana cin abinci a cikin tantin da take zama da iyalanta a Khan Younis.

    Ofishin bayar da agajin jin-ƙai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce hare-haren Isra'ila sun lalata rumbunan ajiye kaya guda uku mallakinsa a garin Deir al-Balah.

  6. 'Yadda Annabi ke kyautata wa yara shi ya sa nake son Maulidi'

    Yayin da ake murnar Maulidin Annabi Muhammadu (SAW), wata budurwa a Kano, Zainab Sanusi ta bayyana mana shirye-shiryen da take yi na murnar ranar.

    Ta yaya za ku yi murnar wannan rana?

  7. An kama tsohuwa ƴar shekara 101 da zargin sayar da wiwi

    An kama wata tsohuwa wadda hukumomi suka ce shekarunta 101 a Najeriya bisa zargin sayar da tabar wiwi, wani abu da ya ja hankalin al’umma.

    A ranar Asabar ne Hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce ta kama Esther Ogunmabo, wadda aka ce tana da jikoki, a jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya.

    Mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi ya ce an kama matar ne da “ƙulli-ƙullin wiwi wadda ta kai nauyin giram 90, inda ta ce tana sayarwa ne ga mutunen unguwa”.

    NDLEA ta ce matar ta ce ta shiga harkar sayar da ganye ne bayan gobarar da ta lalata shagonta na kayan masarufi. Amma an bayar da belin ta.

    Hukumar ta ce wata ƴar tsohuwar ce da ke zaune a birnin Legas ake zargi da tura mata tabar bayan kwana hurhuɗu, inda ita kuma tsohuwar ake zargin tana sayar wa mutane kulli-ƙulli a cikin unguwa.

  8. An buƙaci mutanen Tigray su yi bikin Maulidi a cikin gida

    Majalisar kula da lamurran addinin Musulunci ta yankin Tigray a ƙasar Ethiopia ta buƙaci Musulman yankin su yi bukukuwan maulidi a cikin gida ko ɗakunan taro, sannan kada su je masallatai sai cikin dare domin gudun hare-hare daga sojojin ƙasar.

    “Majalisar ta ce ba za a yi bukin Maulidi a manyan dandalin taruka ba, a maimakon haka za a gudanar da maulidin ne a masallatai, inda za a yi addu’o’i da wa’azi,” a cewar bayanin.

    Al’ummar Ethiopia na hutu a yau Talata domin bikin maulidin haihuwar Annabi Muhammad, wanda ke gudana a ƙasashe da dama na duniya.

    Majalisar addinin Musuluncin ta yankin Tigray ta ce za a yi bukukuwan na masallatai ne a cikin dare domin gudun hare-haren jirage marasa matuƙa na sojojin gwamnati.

    Ana samun rahotannin hare-haren jirage marasa matuƙa a yankin Tigray daga sojojin gwamnatin Habasha, inda irin waɗannan hare-hare suka faɗa birnin Makelle da wasu sassan yankin, lamarin da ke haifar da asarar rayuka da raunata fararen hula.

    An samu irin wannan hari a ranar 18 ga watan Agusta a birnin na Makelle.

    Ethiopia ta dade tana yaƙi da mayaƙan ƙungiyar ƴanta al’ummar Tigray ta TPFL, lamarin da ya haifar da asarar ɗimbin rayuka da tarwatsa mutane daga muhallansu.

  9. Dakarun Amurka sun fara horas da na Najeriya a Bauchi

    Dakarun Amurka sun fara horas da twakwarorinsu na Najeriya kan yadda ake sarrafa jirage marasa matuƙa da kuma kula da sojojin da suka samu rauni a lokacin yaƙi a wani ɓangare na alaƙar tsaro da ƙasashen biyu suka ƙulla.

    A wani bayani da rundunar tsaron Amurka da ke da mazauni a Afirka ta wallafa a shafinta, Africom ta ce horon wanda ke gudana a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya na mayar da hankali ne wajen tabbatar da cewa dakarun Najeriya sun laƙanci kasancewa cikin yanayin ko-ta-kwana da kuma bunƙasa yadda suke aiki.

    Rahoton na Africom ya ce horon ya mayar da hankali kan sarrafa jirage marasa matuƙa, sarrafa makamai, cire bama-bamai, kula da waɗanda suka ji rauni da kuma dabarun yaƙi ga ƙaramar tawagar soji.

    "Amurka da Najeriya na gudanar da aikin bayar da horo a sansanin horon soji da ke a Bauchi, Najeriya, bisa manufar musayar ƙwarewa, ƙarfafa abokan hulɗa da kuma yauƙaƙa alaƙa tsakanin ɓangarorin biyu," a cewar bayanin.

    Horon na zuwa ne bayan a watan Yuli Amurka ta sanar da janye akasarin dakarunta da ta tura Najeriya domin wani aikin yaƙi da ta'addanci na musamman, yayin da ƙasashen biyu suka ci gaba da shirinsu na musayar bayanan sirri da tsaro.

    A ƙarshen shekarar 2025 ne ƙasashen biyu suka ƙulla wata alaƙa ta tsaro bayan shugaban Amurka Donald Trump ya yi zargin cewa ana gallaza wa Kiristoci a Najeriya tare da matsa wa hukumomin Najeriyar lamba kan su magance matsalar tsaro.

  10. An samu nasara a tattaunawar sulhu da Iran - Pakistan

    Pakistan ta ce an samu gagarumar nasara a tattaunawar da wakilanta suka yi da shugabannin Iran a Tehran, wadda ta mayar da hankali kan hanyoyin samar da zaman lafiya.

    Shugaban hafsoshin sojin Pakistan, Field Marshal Asim Munir, ne ya jagoranci tawagar kasar a ziyarar.

    Rahotanni sun ce tattaunawar da ya yi da shugaban Iran da ministan harkokin wajen kasar da kuma shugaban majalisar dokoki ta mayar da hankali ne kan matakan dakile ci gaba da rikicin, da sake bude Mashigar Hormuz, da kuma neman hanyoyin kawo karshen yaƙin da ake yi tsakanin Iran din da Amurka.

    An kuma ruwaito cewa Field Marshal Munir ya tuntuɓi Shugaban Amurka, Donald Trump, kafin tafiyarsa Tehran.

    Rahotanni sun ce Amurka ta nemi Pakistan ta yi amfani da tasirinta wajen shawo kan Iran ta koma teburin tattaunawa.

    Sai dai kawo yanzu babu wata sanarwa daga Washington game da sakamakon ganawar.

  11. 'Takunkumi ba sabon abu ba ne a wurinmu'

    Iran ta mayar wa da Amurka martani da cewa, Amurkar ta daɗe ba ta tsaurara mata takunkumin tattalin arziƙin da take mata barazana da shi ba, tana mai cewa tana da ƙwarin gwiwa cewa abokan hulɗar kasuwancinta za su bijire wa duk wani matsin lamba daga Washington.

    Ministan kudin Iran, Ali Madanizadeh, ya ce takunkumi ba sabon abu ba ne ga ƙasarsa.

    Ya ce, idan maƙiyan ƙasar suka ƙaddamar da abin da ya kira "ta'addancin tattalin arziƙi", Iran ma tana da nata hanyoyin mayar da martani kuma ta san yadda ake takun-saƙar - ba layance mata za a yi ba.

    Shugaban majalisar ƙoli ta tsaron Iran, Mohsen Rezaei, ya yi gargaɗin cewa Tehran a shirye take ta dakatar da dukkan fitar da man fetur daga ƙasashen yankin Tekun Fasha.

    A jiya Litinin Sakataren Baitulmalin Amurka, Scott Bessent, ya ce bankuna da kamfanoni da kuma ƙasashen da suka ci gaba da hulɗa da Iran za su fuskanci irin yadda ake mayar da Iran saniyar-ware a fannin tattalin arziƙi, idan suka ki katse dangantakarsu da ita.

  12. Barka da Maulidi!

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata a wannan shafi na BBC Hausa, inda muke kawo muku muhimman labarai kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a Najeriya, maƙwaftanta da kuma sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook, instagram da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.