Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 24/09/2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Tinubu da Shettima
  • Mahajjata
  • Taron UNGA
  • Mayakan Houthi
  • Wani da ya tsira daga hannun NSCDC ya bayyana mummunan halin da suka shiga a lokacin da suke tsare.
  • Abin da ya janyo mutuwar matasa 37 a Neja - Bago
  • Aisha Aliyu Ja'afar
  • Tsadar farashin mai
  • Yadda sheikh Lukuwa
  • Hoto
  • Cyber Truck
  • Adeyemi Adeniyi
  • Abdourahamane Tchiani
  • Atiku Abubakar
  • NFF

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba

  1. Wasu hare-haren jiragen yaƙin Pakistan sun kashe fararen hula huɗu

    .
    Bayanan hoto, .

    Gwamnatin Taliban ta Afghanistan ta ce hare-haren sun shafi wasu larduna da suka haɗa da Kandahar, Paktia da Khost.

    A Kandahar, wani mazaunin birnin ya ce ya ji karar jirgin yaƙi kafin wata fashewa mai ƙarfin gaske tare da tashin gobara.

    Pakistan ta tabbatar da kai hare-haren, tana mai cewa dakarunta sun kai farmaki kan wurare 10 a Afghanistan, amma ba ta bayyana takamaiman wuraren da aka kai wa hari ba.

    Islamabad ta ce hare-haren sun kasance ne kawai kan wuraren soji da aka gano. Wannan shi ne karo na biyu cikin mako guda da Pakistan ta kai hare-haren sama cikin Afghanistan, bayan wani mummunan hari da aka kai kan wata cibiyar ‘yan sanda a Pakistan a ranar 18 ga Satumba.

    Gwamnatin Taliban ta yi barazanar mayar da martani, yayin da Pakistan ta ce za ta ɗauki mataki kan duk wani abin da ta kira “tsokana”. Mai magana da yawun Taliban, Zabihullah Mujahid, ya ce hare-haren sun shafi Kandahar da Paktia da Khost.

  2. Gwamnatin Italiya ta amince da dokar hana sanya burqa da niqab a makarantu

    .
    Bayanan hoto, .

    Gwamnatin ƙasar dai ta ce za a kuma sanya iyaka kan adadin ɗaliban da ba sa iya magana da Italiyanci sosai a cikin aji guda.

    Za a sanya iyakar kashi 30% ga yaran da ba 'yan ƙasar Italiya ko kuma waɗanda ba su iya Italiyanci sosai ba, a shekarar farko ta makarantun firamare da sakandare da manyan makarantun da suka hada da kwalejoji ya zuwa jami'a.

    Firaministar Italiya Giorgia Meloni ta bayyana matakan a matsayin “matakan da ke cike da hankali waɗanda ba za su raba kan jama'a ba, amma a zahiri suna taimakawa wajen haɗa kan al'umma.”

    Sai dai jam'iyyun adawa sun zargi gwamnati da ƙoƙarin faranta ran manufofin jam'iyyar masu tsattsauran ra'ayi ta dama, Futuro Nazionale, gabanin babban zaɓen ƙasar da za a gudanar shekara mai zuwa.

    Ministan Ilimi Giuseppe Valditara ya ce iyakar kashi 30% ta shafi harshen ne kawai, ba wai dole ne sai ɗalibi na jin harshen Italiyanci ba, ya kuma bayyana dokar hana niqab da burqa a matsayin wani mataki da ya shafi daidaiton jinsi.

    An gabatar da wasu daftarin farko na dokar kafin taron majalisar ministoci na ranar Alhamis, amma manyan abubuwan da ke cikin dokar sun riga sun bayyana.

  3. Fargabar sake ɓarkewar faɗa na ƙaruwa a yankin Tigray

    .
    Bayanan hoto, .

    Rahotanni daga yankin Tigray da ke arewacin ƙasar Habashana cewa mutane sun fara sayen kayan masarufi cikin firgici, yayin da fargabar sake barkewar wani sabon yaƙin basasa a ƙasar ke ƙaruwa.

    Faɗa ya ɓarke tsakanin gwamnatin Habasha da ƙungiyar TPLFwadda ke iko da yankin Tigray. Ƙungiyar ta kuma kafa ƙawance da wasu ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai daga sauran yankuna.

    Farashin abinci da man fetur ya yi tashin gwauron zabi a Tigray, yayin da ake fama da ƙarancin kayan masarufi a wurare da dama na yankin.

  4. Shugaba Trump ya yaba ganawarsa da shugaba Xi na China

    .

    Shugaba Donald Trump da Shugaban ƙasar China, Xi Jinping, sun gudanar da tattaunawa a Fadar White House bayan wani taron girmamawa da aka shirya da safe domin bikin ziyarar aiki ta shugaba Xi zuwa Amurka.

    Shugabannin biyu sun yi magana cikin kyakkyawan yanayi game da yin aiki tare, amma akwai wasu manyan batutuwa masu sarkakiya da ke tsakaninsu.

    Daga ciki akwai kasuwanci tsakanin ƙasashensu, yadda za a tsara da sarrafa amfani da AI, da kuma goyon bayan da China ke bai wa Iran da Rasha. Haka kuma akwai batun ikirarin China kan Taiwan.

    Trump ya shaida wa manema labarai cewa shi da Xi Jinping sun yi “babban taro mai armashi” a Fadar White House a baya. Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

    Ya faɗi hakan ne yayin da yake zagaya wa Shugaban China Xi Jinping cikin harabar Fadar ta White House. Daga cikin wuraren da suka je har da wurin da suka hau jirgin sama mai saukar ungulu na shugaban Amurka na Marine One.

  5. An ɗage harmacin da aka sakawa manema labarai a Fadar White House

    .

    An ba da izinin komawa Fadar White House ga manema labarai na CNN, Politico da MS NOW, bayan da suka nemi kotu ta gudanar da zaman gaggawa domin a dawo musu da damar shiga fadar da aka soke.

    Kafafen watsa labaran sun zargi Fadar White House a cikin takardar da suka shigar a kotu da cewa “sau da dama ta karya” umarnin kotu na ɗage haramcin da Shugaba Donald Trump ya ƙaƙabawa kafafen yaɗa labaran guda uku.

    Sai dai Fadar White House ta bayyana a wata takarda da ta shigar cewa ta fara dawo da damar shiga ga manema labaran jim kaɗan bayan ƙarfe 09:00 na safe agogon EDT (13:00 GMT) ranar Alhamis.

    CNN da MS NOW da Politico sun bayar da rahoton cewa an ba su damar shiga bayan sa’o’i da aka hana wasu daga cikin ma’aikatansu shiga fadar. Da farko, Trump ya ce ya hana kafafen yaɗa labaran shiga ne saboda “labaran ƙarya” da suke yaɗawa. Daga baya kuma Fadar White House ta danganta matakin da batun tsaron ƙasa.

    A cikin sa’o’in farko na ranar, Alƙali Timothy Kelly ya yanke hukuncin cewa ya kamata a dakatar da haramcin na ɗan lokaci, saboda a cewarsa haramcin “mai yiwuwa ya keta haƙƙinsu na tsarin shari’a da kundin tsarin mulki ya ba su.”

  6. Trump ya tattauna da shugaban China a Amurka

    Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban ƙasar China, Xi Jinping, sun gudanar da tattaunawa a Fadar White House bayan wani taron girmamawa da aka shirya da safe domin bikin ziyarar aiki ta shugaba Xi zuwa Amurka.

    Shugabannin biyu sun yi magana cikin kyakkyawan yanayi game da yin aiki tare, amma akwai wasu manyan batutuwa masu sarkakiya da ke tsakaninsu.

    Duk da raha da annashuwar da suka nuna, ba a sa ran ganin an warware batutuwa da dama.

    Daga ciki akwai kasuwanci tsakanin ƙasashensu, yadda za a tsara da sarrafa amfani da AI, da kuma goyon bayan da China ke bai wa Iran da Rasha.

    Haka kuma akwai batun ikirarin China kan Taiwan.

  7. Sojojin Amurka 8 na jirgin USS Lincoln sun yi yunƙurin kashe kansu

    Jirgin yaƙin Amurka na USS Lincoln

    Muƙaddashin Sakataren Rundunar Sojin Ruwa ta Amurka ya ce jami’ai takwas da ke aiki da jirgin yaƙin ruwa na USS Abraham Lincoln sun yi yunƙurin kashe kansu a yayin wani aiki mai dogon zango da Amurka ke gudanarwa a Gabas ta Tsakiya.

    Babban jami'in sojin ruwan an Amurka ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da ya aike wa Sanata Kirsten Gillibrand ta jihar New York, domin amsar tambayoyi kan lafiya da walwalar sojojin ruwan da suka shiga wannan aiki.

    Iyalan wasu daga cikin jami’an sun bayyana damuwa kan yadda lafiyar ƙwaƙwalwarsu ke taɓarɓarewa da kuma matsin yanayin aiki da suke fuskanta yayin aikin, wanda ke da alaƙa da hare-haren soji da Amurka ke kai wa Iran.

    Jirgin USS Abraham Lincoln na gudanar da aiki a yankin tun watan Nuwamban bara, kuma a halin yanzu yana kan hanyarsa ta komawa Amurka.

    A cikin wasiƙar, muƙaddashin sakataren rundunar ruwan, Hong Kao, ya ce an tura ƙwararru a fannin lafiyar ƙwaƙwalwa zuwa cikin jirgin domin bai wa sojojin tallafin lafiya da na tunani.

    BBC ta tuntuɓi Rundunar Ruwa ta Amurka domin neman ƙarin bayani kan lamarin.

    A amsar da ta bayar ta ce waɗanda suka yi yunƙurin kashe kan nasu sun haɗa da ma’aikatan jirgin da matuƙan jiragen saman da ke cikinsa, da kuma sojojin da ke cikin rundunar ayyukan jiragen ƙarƙashin ruwa da sauran jami’an rundunar sama da aka tura yin aiki a kan jirgin.

  8. Amurka ta soke haramcin hana wasu kafafen yaɗa labarai uku shigar Fadar White House

    Manyan kafafen yaɗa labarai uku a Amurka da aka hana shiga Fadar White House sun sanar da cewa yanzu an sake ba su damar shiga.

    CNN da MS da NOW, da kuma Politico ne suka bayyana hakan jim kaɗan bayan sun nemi a gudanar da sauraron ƙara cikin gaggawa a kotu, bayan da aka hana su shiga duk da umarnin wani alƙali na cewa a mayar musu da damar shiga.

    A daren jiya, wani alƙalin kotun gunduma ya yanke hukuncin cewa soke takardun izinin aikin jaridarsu "mai yiyuwa ne ya saɓa wa haƙƙoƙinsu na tsarin doka da kundin tsarin mulki na samun adalci."

    Shugaba Donald Trump ya yi zargin cewa waɗannan kafafen yaɗa labarai suna wallafa "labaran ƙarya da ƙarairayi," yayin da a lokaci guda yake bayyana su a matsayin barazana ga tsaron ƙasa.

    Wannan shi ne sabon rikici a taƙaddamar da ake yi kan ƴancin aikin jarida, kuma ya zo ne makonni kaɗan kafin muhimman zaɓuɓɓukan tsakiyar wa’adin mulki

  9. Iran ta yi gargaɗin cewa sabon yaƙinta da Amurka ka iya bazuwa har tekun Indiya

    Tekun Indiya

    Wani babban mai bai wa gwamnatin Iran shawara kan harkokin soji ya yi gargaɗin cewa duk wani sabon yaƙi na iya bazuwa har zuwa Tekun Indiya idan Amurka ta sake kai wa Tehran hari.

    Manjo Janar Yahya Rahim Safavi, babban mai ba shugaban Iran shawara kan harkokin tsaro da soji, ya ce rundunonin ƙasar sun riga sun tanadi tsare-tsare daban-daban domin tunkarar yanayi iri-iri, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Fars ya ruwaito a ranar Alhamis.

    "Ba mu san abin da ke cikin tunanin Shugaban Amurka Donald Trump da Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ba," in ji Safavi.

    Ya ce sojojin Iran sun shirya wa mafi muni idan har Amurka ko Isra'ila suka sake kai hari kan hukumomi ko muradun ƙasar, tare da gargaɗin cewa rikicin na iya ƙara tsananta.

    "A yanzu yaƙin ya riga ya zarce yankin Tekun Fasha da mashigin Hormuz, ya kuma bazu zuwa Tekun Maliya. Yaƙin da za mu sake yi da Amurka na gaba zai iya bazuwa har zuwa Tekun Indiya ko wasu yankuna," in ji shi.

  10. Sojojin Habasha sun ce sun kashe mayaƙan TPLF 100 a Tigray

    Sojojin ƙasar Habasha sun yi ikirarin kashe sama da mayaƙan ƙungiyar TPLF 100, wadda ke iko da arewacin yankin Tigray.

    Gwamnati ta ce ta maida martani ne bayan dakarun TPLF sun karbe ikon filayen jirgin sama 3 da kai wa sojojin Habasha hare-hare a sassa daban-daban na kasar.

    Kawo yanzu TPLF ta bai wa dakarunta umarnin ɗaukar matakin kare kai da maida martani ba kuma za su ja da baya ba har sai sun cimma nasara.

    A baya yaƙi tsakanin ɓangarorin biyu, ya yi sanadin mutuwar dubban farar hula, yawanci saboda matsananciyar yunwar da yaƙin ya haddasa.

    Rahotanni daga yankin Tigray na cewa mutane na ta siyan kayan abinci, ana fargabar yawanci ma sun kare a kasuwanni.

  11. Kotu ta soke takarar gwamna da Pantami ke yi a Gombe

    Pantami

    Babbar kotun Tarayya da ke zamanta a Gombe ta rushe takarar Farfesa Isa Ali Pantami ɗantakarar gwamnan jihar na jam'iyyar PDP.

    Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Amina Aliyu Mohammed, ta yanke hukuncin ne a wata ƙara da Usman Aliyu Garry ya shigar, inda yake ƙalubalantar fitowar Farfesa Isa Ali Pantami a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Gombe.

    Wani makusancin Farfesa Pantami da BBC ta zanta da shi ya ce tawagar lauyoyin ɗantakarar na PDP na nazarin hukuncin.

    Kotun ta buƙaci jam'iyyar PDP ta sake gudanar da zaɓen fitar da gwani domin tabbatar da wanda zai yi wa jam'iyyar takara

    A watan Yuni ne PDP ta bai wa Pantami tikitin takarar gwamnan Gombe bayan da ya gaza samu tikikin jam'iyyar APC.

  12. EFCC ta sake ayyana Abdulrasheed Maina a matsayin wanda take nema

    ...

    Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon ƙasa, EFCC, ta sake ayyana tsohon shugaban kwamitin gyaran harkokin fansho, Abdulrasheed Maina, a matsayin wanda take nema ruwa a jallo.

    A wata sanarwa da EFCC ta fitar ranar Laraba, 23 ga Satumba, 2026, hukumar ta ce tana neman Maina.

    Hukumar ta ce tana nemansa ne bisa zarginsa da hannu a karɓar kadarorin da ake zargin an sace.

    A sanarwar da kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya fitar, hukumar ta buƙaci duk wanda ke da sahihin bayani da zai taimaka wajen gano inda Maina yake da ya sanar da ofishinta.

    Ba wannan ne karon farko da Maina, mai shekara 61, ya shiga matsala da EFCC ba.

    A shekarar 2015, hukumar ta taɓa ayyana tsohon shugaban kwamitin gyaran harkokin fanshon a matsayin wanda take nema.

    A wancan lokacin, EFCC ta ce tana son ya bayyana domin amsa tambayoyi kan rawar da ake zarginsa da takawa a wasu kwangilolin tattara bayanai da hukumar ta yi zargin an gudanar da su ta hanyar almundahana.

    Hukumar ta kuma zargi Maina da tsohon shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, Steve Oronsaye, da wasu mutum biyu da almundahanar sama da naira biliyan biyu na kuɗaɗen fansho.

  13. Sauye-sauyen da gwamnati ke aiwatarwa na haifar da sakamako mai kyau - Shettima

    Kashim Shettima

    Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya ce ƙasar ta tsallake wani muhimmin mataki a sauye-sauyen tattalin arzikinta, kuma yanzu tana kan hanyar samun ci gaba mai ɗorewa.

    Bayanin na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha ya fitar.

    Shettima ya ce sauye-sauyen da gwamnatin ke aiwatarwa sun fara haifar da sakamako na zahiri, inda ya bayar da misali da ƙaruwar ajiyar kuɗin ƙasashen waje zuwa sama da dala biliyan 55, da ingantuwar kasuwar musayar kuɗaɗen waje, da kuma ƙaruwar tattalin arzikin ƙasar da kashi 4.45 cikin 100 a rubu’i na biyu na bana.

    Mataimakin Shugaban Najeriyar ya bayyana haka ne ranar Laraba yayin wata ganawa da ’yan Najeriya mazauna Amurka a New York, a wai ɓangare na babban taron zauren Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81.

    Ya shaida wa mahalarta taron cewa duk da ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta, gwamnatin Tinubu na aiki domin sake fasalin tattalin arzikin ƙasar, musamman a fannonin ilimi da lafiya da kimiyya da fasaha da kuma noma, tare da samar da yanayin da zai jawo masu zuba jari.

    Sanarwar ta ruwaito Shettima na cewa “Ku kwantar da hankalinku cewa duk da munanan labaran da kuke ji da gani a kafafen sada zumunta, ƙofar Najeriya a buɗe take domin kasuwanci. Mun tsallake wani muhimmin mataki, kuma muna kan hanyar samun ci gaba mai ɗorewa.”

    Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje da su taka rawar gani wajen ci gaban ƙasar, yana mai bayyana ilimi da ƙwarewa da basirar da suke da ita a matsayin muhimman kadarori ga yunƙurin Najeriya na sauya fasalin tattalin arzikinta.

  14. Isra'ila ta ce ta kashe wani jami'in Hamas

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarunta sun kashe Mohammed Abu Alwan, shugaban sashen kuɗi na Hamas, a wani hari da suka kai Khan Younis da ke kudancin Zirin Gaza ranar Laraba.

    Sanarwar rundunar sojin Isra'ila, IDF, ta ce Abu Alwan “ya taka rawa wajen tsara kasafin kuɗin dukkan rassan Hamas.”

    Rundunar Isra'ila ta kuma ce a ƙarƙashin jagorancinsa, an tura sama da shekel biliyan ɗaya, kwatankwacin kusan dala miliyan 330, domin ɗaukar nauyin ayyukan Hamas.

    A cewar IDF, Mohammed Abu Alwan ya kasance “muhimmin jigo ne a ci gaban Hamas da ikonta.”

  15. 'Hare-haren Pakistan sun kashe farar hula huɗu a Afghanistan'

    Afghanistan ta ce hare-haren sama da Pakistan ta kai wurare da dama a ƙasar sun kashe fararhula huɗu, tare da alƙawarin mayar da martanin da ya dace.

    Zargin na zuwa ne bayan da Pakistan ta ce ta kai hare-hare kan wasu wurare a Afghanistan da ake amfani da su wajen ƙaddamar da hare-haren jirage marasa matuƙa da ke ƙetara iyakar ƙasashen biyu.

    Jami'an Pakistan sun ce sun kakkaɓo jirage marasa matuƙan, amma hukumomin Taliban sun musanta cewa su ne suka harba su.

    Mazauna Kandahar, inda babban jagoran Taliban yake, sun ce an kai hari a tsakiyar birnin.

    Taliban ta ce an kuma kai hare-hare a lardunan Paktia da Khost.

    Pakistan na zargin Taliban da bai wa mayaƙan da ke kai munanan hare-hare a arewacin Pakistan mafaka, zargin da Taliban ɗin ke musantawa.

  16. Ya kamata China da Amurka su zama abokan hulɗa ba na hamayya ba - Xi

    ..

    Xi Jinping: Ya kamata China da Amurka su zama abokan hulɗa maimakon abokan hamayya

    Shugaban China Xi Jinping ya yi kira ga ƙasarsa da Amurka su zama abokan hulɗa maimakon abokan hamayya, a kalaman da kafafen yaɗa labaran gwamnatin Chinan suka wallafa sa'o'i bayan isarsa Washington domin wata muhimmiyar ziyarar aiki.

    Mista Xi ya ce muradun ƙasashen biyu suna da alaƙa sosai, saboda haka ya kamata su ci gaba da haɗin gwiwa, su kuma yi gogayya bisa tanadin doka.

    Ana sa ran ziyarar Xi ta kwanaki uku, wadda Shugaba Donald Trump ke karɓar baƙuncinsa, za ta ƙunshi tattaunawa kan batutuwa masu sarƙaƙiya da suka haɗa da cinikayya da fasahar AI da Taiwan da kuma Iran.

    An kuma sanar da tsawaita wa'adin yarjejeniyar sassauta takaddamar cinikayya tsakanin ƙasashen biyu zuwa Janairu.

  17. Gwamnatin Nijar ta karɓi kashi 40 na aikin haƙar uranium

    ..

    Gwamnatin mulkin soja ta Nijar ta cimma yarjejeniya da kamfanin haƙar ma’adanai na Madaouela don sake fara aikin haƙar uranium, wani sabon mataki mai muhimmanci ga tattalin arzikin ƙasar.

    A ƙarƙashin yarjejeniyar da aka rattabawa hannu a Yamai ranar Laraba, gwamnatin Nijar ta karɓi kashi 40 na aikin haƙar uranium.

    Ana sa ran yarjejeniyar za ta ƙunshi biyan gwamnati dala miliyan 10 da farko, tare da samar da ayyukan yi kusan 1,000.

    Kamfanin dillancin labaran Nijar ANP ne ya ruwaito yarjejeniyar.

    Wannan mataki ya yi daidai da manufofin gwamnatin mulkin sojan Nijar na ƙara wa gwamnati iko kan albarkatun ma'adinai na ƙasar, tare da sake duba yarjejeniyoyin haƙar ma'adinai da kamfanonin ƙasashen waje.

    Madaouela na daga cikin manyan wuraren da da arzikin uranium, inda aka kiyasta cewa yana ɗauke da kimanin tan 52,800 na uranium.

    Kamfani dillancin labarai na AFP ya ce ana farfaɗo da aikin ne bayan kawo ƙarshen yarjejeniyar da aka yi a baya da kamfanin GoviEx na Canada.

    Wannan wani misali ne na yunƙurin mahukuntan Nijar na ƙara wa gwamnati iko da albarkatun ƙasar da kuma ƙarawa gwamnati kuɗaɗen shiga.

  18. Ministocin harkokin wajen Pakistan da Iran sun gana a New York

    ..

    Mataimakin Firaministan Pakistan kuma Ministan Harkokin Wajen ƙasar, Ishaq Dar, ya gana da takwaransa na Iran, Abbas Araghchi, a wani ɓangare na taron babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya.

    Ma'aikatar Harkokin Wajen Pakistan ta bayyana a shafinta na X cewa ɓangarorin biyu sun tattauna kan dangantakar ƙasashensu, tare da musayar ra'ayoyi kan abubuwan da ke faruwa a yankin da kuma duniya baki ɗaya.

    A cewar Pakistan, Mista Dar ya jaddada muhimmancin tattaunawa da diflomasiyya da kuma ci gaba da mu'amala domin ƙarfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

    Bangarorin biyu sun kuma amince su ci gaba da tuntuɓar juna.

    Pakistan na ɗaya daga cikin manyan masu shiga tsakani tsakanin Iran da Amurka.

  19. Kifewar kwale-kwale ya yi sanadin mutuwar mata huɗu a Jigawa

    Hatsarin kwale-kwale

    Wasu mata huɗu sun mutu bayan da kwale-kwale ɗauke da mutum takwas ya kife a tafki Dudduru da ke ƙaramar hukumar Dutse a jihar Jigawa.

    Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Laraba.

    Daily Trust ta ruwaito Shugaban hukumar tsaro ta NSCDC a jihar ya tabbatar da lamarin ta cikin sanarwar da kakakin hukumar, ASC Badruddeen Tijjani Mahmud ya fitar.

    A cewar sanarwar, kwale-kwalen yana ƙoƙarin kai fasinjojin takwas zuwa kasuwar Chai Chai Sabuwa daga ƙauyen Kwadige a lokacin da jirgin ya kife.

    Matan da suka mutu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito matasa ne da shekarunsu ke tsakanin 12 zuwa 13.

    Shugaban NSCDC a jihar ya ce tuni aka yi jana'izar mamatan kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

  20. Gagarumar fashewa ta afku a Kudancin Lebanon

    Wata gagarumar fashewa ta afku a birnin Khayyam da ke Kudancin Lebanon, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ƙasar ya bayyana.

    Lamarin ya kuma shafi wasu yankuna da ke maƙwabtaka da wajen.

    Rahotanni su ce cibiyar fashewar ta kasance a wani yanki mai tsawon kimanin mita 300.

    Kamfanin dillancin labaran ya sanar cewa ƙarfin fashewar ya kai ga garuruwan Marjayoun da Al-Qalia da ma wasu yankunan da ke kewaye da su.

    Zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, babu ƙarin bayan ikan abin da ya haddasa fashewar.