Mun goyi bayan matakin INEC kan ADC - Jama'iyyar APC

Asalin hoton, APC
Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta ce ta goyi bayan matakin da hukumar zaɓen ƙasar, INEC ta ɗauka kan jam'iyyar hamayya ta ADC.
INEC ta soke shugabanci ADC tare da janye sunayen shugabannin jam'iyyar, tsagin David Mark daga shafinta saboda wani hukuncin kotu.
Cikin wata hira da BBC daraktan yaɗa labaran sakatariyar APC, Mallam Bala Ibrahim ya ce hukumar zaɓe, kamar alƙali ne, ba ta goyon bayan kowane ɓangare a harkar zaɓe, aikinta shi ne ta yi adalci ga kowa.
Dangane da zargin da ADC ke yi wa APC na amfani da hukumar zaɓe domin muzguna mata kuwa, Mallam Bala Ibrahim ya ce sam ba haka ba ne.
''Rikicinsu ne na cikin gida, magana tana kotu, kuma yayin da magana ke gaban kotu kamata ya yi a bar kotu ta kammala aikinta'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa matakin da INEC ta ɗauka yana kan doron shari'a, saboda biyayya ne ga hukuncin kotu.
''Mu mun yarda da matsayin da hukumar zaɓe ta ɗauka na janye goyon bayan shugabancin kowane ɓangare na David Mark da na Bala Nafi'u'', in ji shi.







