Ukraine ta zargi Rasha da kai har ga fararen hula

Asalin hoton, LightRocket via Getty Images
Ukraine ta zargi Rasha da ƙara kai hare-hare kan ababen more rayuwa da fararen hula ke amfani da su, bayan wasu sabbin hare-hare da aka kai kan gidajen mai, da harkokin sufurin jiragen ruwa da kuma layukan dogo. An kashe mutane biyu, yayin da sama da 40 suka jikkata a Kyiv, babban birnin ƙasar, inda jirage marasa matuƙa suka shafe mafi yawan yini suna shawagi a sararin samaniyar birnin. Da yake jawabi a wani taron kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya, ministan harkokin wajen Ukraine, Andrii Sybiha, ya ce bai kamata a ɗauki yaƙin a matsayin wani abu na yau da kullum ba. Ya ce Ukraine ta amince da tsagaita wuta gaba ɗaya, nan take kuma ba tare da wani sharadi ba, tare da yin kira ga Rasha da ta yi hakan. Jakadan Amurka a Majalisar Ɗinkin Duniya, Mike Waltz, ya yi Allah wadai da duk wani yunƙurin faɗaɗa rikicin.



























