Labaran wasannin BBC Hausa na 27 Yuli - 2 Agusta 2026

Wannan shafi ne da yake kawo muku labaran wasannin BBC Hausa na ranakun 27 ga watan Yuli, zuwa 2 ga watan Agusta 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Buhari Fagge

  1. An ci tarar Chelsea saboda karya ƙa'idar siyan 'yan wasa

    c

    Asalin hoton, Getty Images

    An ci tarar Chelsea fan miliyan 10 tare da dakatar da su daga daukar sabbin 'yan wasa na tsawon kaka biyu saboda karya dokar da ke da alaka biyan kudaden wakilan 'yan wasa daga 2009 zuwa 2022.

    Amma an rage wa ƙungiyar maki shida, wadda aka dakatar sai nan da 30 ga watan Yunin 2027, an kuma yanke uzurin daukaka kara.

    Mamallaka kungiyar Todd Boehly da Clearlake Capital sun ba da rahoton karya ƙa'idoji 74 na hukumar kwallon ƙafa lokacin da suka sayi ƙungiyar.

    Chelsea ta amsa yin hada-hadar fan miliyan 47 a boye ba tare da biyan wakilan 'yan wasa ba kan cinikin tsakanin 2011 zuwa 2018.

    FA ta ce za ta ci gaba da bincike daya bayan daya kan saba dokokin da aka yi.

  2. Newcaste ta tabbatar da ajiye aikin Eddie Howe

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    Newcastle ta tabbatar tsohon kocinta Eddie Howe ya yi murabus daga matsayinsa na mai horas da ita.

    Kocin mai shekara 48 ya bar ƙungiyar ne bayan kwashe kimanin shekara biyar yana jan ragamar ƙungiyar, bayan kakar da ta ƙare ba ta yi masa kyau ba inda ƙungiyar ta ƙare a matsayi na 17 ta tsallake Championship da kyar.

    Ya taimaka wa Magpies ta je Champions Lig sau biyu sannan ta lashe League Cup a 2024/25.

    "Bayan yin abin da zan iya, daga ƙarshe na yanke shawarar saua daga matsayina," in ji Howe.

    Nuwcastle ta ce tuni ta yi nisa wajen neman kocin da zai maye gurbinsa. Kuma a zahiri yake ta karkata wajen neman ɗaukar kocin nan ɗan Jamus Mattias Jaissle.

  3. Anya Infantino zai kai labari idan ƙuri'a za a kaɗa?

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    Har yanzu ana samun masu bayyana ra’ayinsu ta hanyar suka kan matakin shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa Gianni Infantino kan shirinsa na sayar da kashi 20 na haƙƙoƙin kasuwancin Gasar Kofin Duniya.

    Na baya-bayan nan su ne sabon kocin Chelsea Xabi Alonso da ya ce bai kamata a mayar da harkokin kwallon kafa ba hannun ‘yan kasuwa.

    Firaiministan Burtaniya Andy Burnham shi ma ya shiga layi inda ya ce kwata-kwata Gianni Infantino bai dace da zama shugaban Hukumar kwallon ƙafa ta duniya.

    Kuma ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan mai baiwa Infantino shawara na musamman kan shugabanci da tsara dabaru Carlos Codero ya ce ya yi murabus daga aikinsa.

    Firaiministan ya yaba da yadda Hukumar kwallon ƙafa ta Asia da ta Turai da wadda ke kula da arewa da tsakiya da kuma yankin Caribbean suka yi watsi da wannan buƙata ta Infantino.

    Shugaban Fifa har yanzu bai ko kula da sukar da ake yi mas aba, shi dai damuwarsa mfi yawan mambobin hukumar su goyi bayansa.

    Hukumar da ke da mambobi 211 idan 106 suka goyi baya to burin Infantino zai ci ka na sayar da kashi 20 cikin 100 na haƙƙoƙin kasuwancin Gasar Kofin Duniya.

    Yanzu dai Uefa na da kuri’a 55 Concacaf tana da 35 yayin da Asia ke da 46, hakan na nufin sun hada kuri’a 136 cikin 211, ko da sauran mambobin Fifa za su zabi infantino ta kudurinsa ba zai kai labari ba, indai kuri’a za a yi.

  4. Iraola ya ce ya san wurin da Wirtz zai riƙa bugawa da ya dace da shi

    d

    Asalin hoton, Getty Images

    Sabon kocin Liverpool Andoni Araola ya ce ya san wurin da dan wasan gaban ƙungiyar dan Jamus Florian Wirtz zai riƙa bugawa da ya dace da shi a kungiyar.

    Kocin wanda ya baro Bournemouth a ƙarshen wannan kakar, ya ce zai fi kyau ɗan wasan ya riƙa raka 'yan wasan gaba masu cin kwallo, maimakon sa shi a wajen shi da kan shi.

    Wirtz ya buga duka wasannin da Jamus ta yi a gasar Kofin Duniya inda yake buga ɓangaren hagu, sai dai an cire su a zagayen 'yan 32.

    Dan wasan ya buga ɓangarori da dama a gaba tun bayan zuwansa Liverpool, inda ya ci kwallo bakwai kawai ya taimaka aka ci 10 a wasanni 49 da ya yi ya zuwa yanzu.

    "Muna buƙatar 'yan wasa irinsu Florian, mun san abin da zai iya bamu. Kuma na san zai yi daidai da salon kwallon da za mu buga," in ji Araola.

  5. Dan bayan Ingila Stones ya koma Inter Milan daga Man City

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    Dan wasan bayan Ingila John Stones ya koma Inter Milan gwarzuwar gasar Italiya, bayan ƙarewar kwantaraginsa a Manchester City.

    Dan wasan da ya halarci gasar Kofin Duniya tare da Ingila ya sanya hannu ne kan kwantaragin shekara biyu.

    Mai shekara 32 kwantaraginsa a City ta ƙare ne a ƙarshen watan Yuni bayan kwashe shekara 10 a ƙungiyar da ta mamaye Premier a tsukukun.

    Stone ya ce ya cimma komai bayan na "taimaka wa City ta ci Premier shida da Champions Lig da FA Cup biyu da League Cup biyar da Community Shields uku da Club World Cup ɗaya da Uefa Super Cup ɗaya shi ma.

    Tun bayan ƙarewar kwantaragin nasa ƙungiyoyin Turai sun ta neman shi, ciki har da Chelsea da Juventus.

    Ya ci wa City kwallo 19 cikin wasa 295 da ya buga wa ƙungiyar tun bayan komawarsa a 2016.

  6. Tsohon ɗan wasan AC Milan da Italy Baresi ya mutu yana da shekara 66

    f

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Baresi ya zama kyaftin ɗin AC Milan ne lokacin yana ɗan shekara 22

    Tsohon dan wasan AC Milan da Italiya Franco Baresi ya mutu yana da shekara 66 a duniya.

    Ƙungiyar kwallon ƙafa ta AC Milan ta ce ba za a taɓa mantawa da gudunmuwar da tsohon kyaftin ɗin ƙungiyar ya ba da ba.

    Baki ɗayan rayuwar ƙwallon ƙafara Baresi ta ƙare nene a ƙungiyar inda a fara kwallo daga 1977 zuwa 1997, ya lashe kofin Serie A shida da European Cup uku da kuma Champions Lig.

    Ana masa kallon ɗaya daga cikin mayan 'yan baya a fagen kwallon ƙafar duniya, Kyaftin ɗin ya yi kaka 15 a Milanya kuma buga mata wasa 719 tare da cin kwallaye 33.

    d

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, A kakar 1993/94 Baresi da kocin AC MIlan na lokacin Fabio Capello lokacin da suka ɗauki kofin Serie A na uku a jere da Champion Lid da kuma Supercoppa Italiana

    Ya buga wa ƙasarsa Italiya wasa 81, kuma yana cikin tawagar da ta lashe wa ƙasar Kofin Duniya a 1982. Shi ne Kyaftin ɗin Italiya a 1994 da suka buga wasan ƙarshe na kofin duniya da Brazil ta cinye su.

    A 2020 ne Baresi ya zama mataimakin shugaban AC Milan, kungiyar da ta ajiye rigarsa mai lamba shida ba a baiwa kowa ba har na tsawon shekaru huɗu.

    Baresi yana cikin 'yan bayan nahiyar turai da aka fi girmamawa tare da takwaransa Paolo Maldini da Alessandro Costacurta da kuma Mauro Tassotti.

    A lokacin da za a fara kofin duniya na 1994, ɗan wasan ya dowa daga ciwon gwiwa ne amma shi ne wanda ya hana Romario da Bebeto taka rwar gani a waasan da aka tashi 0-0.

    a

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Baresi ne kyaftin ɗin Italiya a gasar kofin duniya ta 1994, makonni uku bayan an yi masa tiyata a gwiwarsa.
  7. Ana sa ran kyaftin ɗin Newcastle Bruno Guimaraes zai koma Arsenal

    a

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni daga majiyoyi da dama sun nuna cewa ana ƙara samun tabbacin kyaftin ɗin Newcastle United, Bruno Guimaraes, zai koma Arsenal a wannan kasuwar saye da sayar da ƴan wasa.

    Majiyoyin sun shaida wa BBC Sport cewa ɗan wasan tsakiyar Brazil ya bayyana aniyarsa ta komawa Arsenal, wadda ta lashe gasar Firimiya, kuma ƙungiyar na ƙara samun kwarin gwiwar kammala cinikin ɗan wasan mai shekara 28.

    Guimaraes ya koma Newcastle ne daga ƙungiyar Lyon ta Faransa a shekarar 2022, inda ya zura ƙwallaye 31 a wasanni 195 da ya buga wa ƙungiyar.

    Arsenal ta nuna sha'awarta kan ɗan wasan tun farkon da aka buɗe kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ta bana.

    Sai dai rahotanni sun ce idan Arsenal na son kammala cinikin, za ta buƙaci ta ƙara kuɗin fam miliyan 70 da ta miƙa wa Newcastle a farkon wannan watan.

    Ana sa ran Guimaraes zai koma atisaye tare da Newcastle cikin 'yan kwanaki masu zuwa, yayin da ake ci gaba da tattaunawar cinikin sa.

  8. Uefa za ta iya ƙauracewa Kofin Duniya kan matakin Fifa

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Turai mai mambobi 55 ta kaɗa ƙuri'ar ƙauracewa Gasar Kofin Duniya ida Hukumar kwallon ƙafa ta Duniya Fifa ta aiwatar da shirinta na sayar da wani ɓangare na ta ga masu zuba jari.

    An yanke hukuncin ne a wani taron gaggawa da aka kira domin tattaunawa kan sanarwar da Fifa ta fitar a farkon wannnan makon, wadda take shirya kofin duniya.

    Uefa wadda ke shirya wasannin nahiyar Turai, ta bayyana ƙarara tana adawa da matakin bayan sakin wasu sanarwa biyu da suka nuna adawa da matakin.

    "Bai kamata a ce Kofin Duniya ya zama ana gudanar da shi ba ƙarƙashin masu zuba hannun jari," inji Uefa.

    "Babu wani wasa da ya fi kwallon ƙafa a faɗin duniya. Manyan 'yan wasa da magoya baya da kasashe ne suka gina wannan tarihin a nahiyoyi. Babu wani sashe nasa da ya kamata a sayarwa masu zuba hannun jari. Kofin duniya ba na sayerwa ba ne."

    Rashin shiga wasannin da Uefa za ta yi ya haɗa da duka wasa gasannin da Fifa ke haɗawa har da na mata, da wasan gwarazan ƙungiyoyi da dai sauransu.

  9. Rashford ya yi ban kwana da Barcelona

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    Marcus Rashford ya yi bankwana da Barcelona a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Instagram tare da rigarsa mai lamba 14 da ya riƙa sawa a kakar bara.

    Rashford ya ci kwallo 14 ya kuma bayar da 14 an ci a duka gasanni a kakar da ta gabata a zaman da ya yi na aro daga Manchester United yayin da ƙungiyar ta lashe La Liga.

    A watan Yuni, wa'adin da Barcelona ta amince da shi tsakaninta da Manchester United kan za a iya sayen ɗan wasan fan miliyan 26 daga ƙarshen zaman aronsa domin komawa zamansa na wurin na dindindin.

    Ya buga wasa shida cikin takwas a ƙarƙashin Thomas Tuchel kuma ya yi ƙoƙari a duka wasannin da ya buga.

    Dan wasan mai shekara 28 da kwantaraginsa za ta ƙare a 2028 a Old Trafford babu tabbaci kan ci gaba da zamansa a United.

    Yace "na ji dadin zamana a wannan ƙungiyar kuma zai zauna a cikin kwakwalwata har abada" kamar yadda ya wallafa.

  10. Chelsea ta ɗauki Maxence Lacroix ɗan Faransa daga Crystal Palace

    ,

    Asalin hoton, Chelsea

    Chelsea ta ɗauki dan wasan bayan Faransa Maxence Lacroix daga Crystal Palace kan kuɗi fan miliyan 52.

    Dan shekara 26 da ya bugawa Faransa wasa sau bakwai ya sanya hannu kan kwantaragi a Stamford Bridge zuwa 2032.

    A 2024 ne ɗan Faransan ya koma Palace daga ƙungiyar Wolfsburg ta Bundesliga kan kuɗi fan miliyan 15.5 ya kuma yana ɗaya daga cikin masu muhimmanci a ƙungiyar a ƙarƙashin Oliver Glasner.

    Maxence Lacroix ya buga wasa 55 a duka gasanni ciki har da wanda Palace ta lashe Uefa Conference, kuma shi ne wani babban kofi da ƙungiyar ta taɓa ɗauka.

    Dan wasan ya buga wa ƙasarsa Faransa wasanni uku a gasar kofin duniya ciki har da wasan neman na uku da suka fafata da Ingila suka yi rashin nasara.

    Lacroix shi ne ɗan wasa na uku da Chelsea ta ɗauka a wannan tsukukun baya fa Morgan Rogers da Marco Palestra, duka ƙarƙashin sabon kocin ƙungiyar Xabi Alonso.

  11. Lokacin Howe a Newcastle - Yadda ya fara

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    • Ya karɓi ƙungiyar a wasan Oktoban 2021, bayan kammala karɓar ƙungiyar da masu zuba jari daga Saudiyya suka yi
    • A watan Nuwanbar 2021 aka naɗa Howe a hukumace a matsayin kocin ƙungiyar lokacin tana ta 19 a teburi, kuma tana neman maki biyar kacal ta tsira daga faɗawa Championship.
    • A Janairun 2022 - Howe ya ɗauki Kieran Trippier da Bruno Guimares da kuma Dan Burn waɗanda daga baya suka taimaka aka ci kofi da su.
    • A watan Mayun 2022, ya mayar da ƙungiyar ta kammala gasar Premier a matsayi na 11
    • A watan Agustan 2022 - ƙungiyar ta kashe fan miliyan 120 inda ta sayo mai tsaron raga Nick Pope da Alexander Isak cikin mutum huɗu da aka ɗauka a ƙungiyar
  12. Messi ya koma atisaye a Inter Miami

    ,

    Asalin hoton, Inter Miam X

    Dan wasan Argentina LIonel Messi ya koma atisaye da ƙungiyarsa ta Inter Miami bayan wani ɗan ƙaramin hutu da ya yi na bayan Kofin Duniya.

    Bayan kammala gasar da kwanaki 10 wadda Messi ya yi rashin nasara a hannun Spain da ci 1-0, kyaftin ɗin zai koma atisaye cikin abokan wasanta na Miami.

    ,

    Asalin hoton, Inter Miam X

    Kungiyar da ke zaune a Florida ta sanya hotonsa lokacin da ya shiga filin atisayen nasu tare da abokan wasansa, hotunan sun ja hankalin magoya baya nan da nan.

    Dawowarsa ta karawa magoya baya kwarin gwiwa wadanda suka kalli wasanni biyu ba tare da shi ba.

    m

    Asalin hoton, Inter Miam X

  13. Za a fara Premier bana da sabbin koci tara cikin 20

    a

    Asalin hoton, Getty Images

    Yayin da ya rage saura kwana 22 a fara Premier 2026/2027 an samu sauye-sauye masu yawa a gasar kama daga ɓangaren 'yan wasa zuwa na masu horaswa da kuma na mamallaka.

    Cikin sauye-sauyen da aka samu ya zuwa yanzu daga ɓangaren masu horaswa, ƙungiyoyin Liverpool, Chelsea, Manchester City, Bournemouth, Crystal Palace, Nottingham Forest, Fulham, Ipswich da kuma Newcastle za su fara gasar da sabbin koci.

    Ya zuwa yanzu sabbin koci tara ne aka samu sauyi cikin 20, kuma ba a sani ba ko kafin nan da a fara gasar za a iya samun wani ƙarin sauyin.

    Wannan ce kaka ta farko da aka samu gagarumin sauyi daga masu horaswa.

    Yayin da a gefe guda kuma 'yan wasa da dama suka tsawaita kwataraginsu wasu kuma suka sauya sheƙa.

    Kakar da aka ƙare dai, Arsenal ce ta zama gwarzuwarta, bayan lashe kofin da ta kwashe shekara 22 ba ta ci ba.

  14. Howe ya kawo ƙarshen shekaru 70 na Newcastle ba ta tare da kofi ba

    a

    Asalin hoton, Getty Images

    Eddie Howe ya maye gurbin Steve Bruce ne a matsayin kocin ƙungiyar a 2021 kuma ya ci mata kofi na farko cikin shekaru 70.

    Ya kai ƙungiyar ta Magpies zuwa gasar Zakarun Turai a 2023 da 2025.

    Ko shakka babu ɗaya daga cikin abubuwan da za a ci gaba da tunawa a Newcastle shi ne kofin Carabao da ya ci wa ƙungiyar a 2025.

    Dan Burn be ya fara ci kafin daga baya Alexander Isak ya ƙara su samu nasara kan Liverpool da ci 2-1 a filin wasa na Wembley.

    A watan Oktobar 2023, wata fitila ta haska a Filin James Park ƙarƙashin Howe inda ya samu nasara kan gwarzuwar gasar Zakarun Turai ta ƙasar Faransa PSG da ci 4-1.

    Shekaru 20 da suka yi ba su je gasar ba, amma daga baya ya kai su tare da farin ciki mai tsayi.

  15. De Zerbi na son Spence ya ci gaba da zama a Tottenham

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    Kocin Tottenham Roberto de Zerbi ya ce yana son ɗan wasan bayan ƙungiyar Djed Spence ya ci gaba da zama a ƙungiyar saboda jita-jitar da ake yi na kansa ta sauya sheƙa.

    Dan wasan mai shekara 25 da ya sanya hannu kan doguwar kwantaragi a bara, ana raɗe-raɗin zai bar ƙungiyar ya koma Inter Milan ko kuma Everton.

    De Zerbi ya ce yana ɗaukar Spence a matsayin mai muhimmanci a shirin da yake da shi a ƙungiyar, duk da cewa yana son ƙaro wani ɗan wasa a hannun a wannan bazarar.

    Ƙungiyar da ta tsallake rijiya da baya a Premeir bara, ya zuwa yanzu ta kashe fan miliyan 237 wajen sake gina ƙungiyar domin tunkarar kakar da za a fara a Agusta.

    Dan wasan na Ingila an fara wasanni 23 da shi cikin 30 da ya buga a bara, duk da cewa ƙungiyarsa ta kammla gasar a matsayi na 17.

    Dan wasan Spain da ta ci Kofin duniya da shi Pedro Porro yanzu haka shi ne ya mamaye wurin da Spence yake bugawa na ɓangaren dama a baya, don haka ya fi buga ɓangaren hagu.

  16. Eddie Howe zai bar Newcastle

    a

    Asalin hoton, Getty Images

    Kocin Newcastle Eddie Howe ya shirya barin ƙungiyar cikin gaggawa kamar yadda wata majiya ta shaida wa BBC Sports.

    Howe ya shiga matsi ne a ƙarshen kakar da ta gabata bayan ya kammalata Premier bara bayan rashin nasara 17 da ya yi cikin wasanni 38.

    Wasan kocin na ƙarshe shi ne wanda ya sha kashi a hannun Bristol City da ci 4-1 a wasan sada zumunta na share fagen kaka a ranar Laraba.

    Ana tsammanin Atthias Jaissle da ke kocin Al-Ahli da ke Saudiyya ne zai maye gurbin koci Eddie Howe.

    Ya koma Newcastle ne a Numabar 2021, wata guda bayan masu zuba jari daga Saudiyya sun zuba kudi a ƙungiyar.

  17. Savinho ya shirya barin City zuwa Tottenham

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    Dan wasan gefe na Manchester City Savinho ya nuna buƙatar barin ƙungiyar bayan nuna muradin da Tottenham suka yi a kan shi.

    Savinho ɗan Brazil mai shekara 22 yana daga cikin waɗanda kocin Tottenham Roberto de Zerbi ke son saya.

    Bayanai sun ambato ɗan wasan shi ma na son barin City a yayin wannan kakar ta saye da sayerwa, inda yiwuwar komawarsa tawagar da ke arewacin London ta fi ƙarfi.

    Dan wasan ya koma City ne daga Troyes kan kan kuɗi £30.8m a watan Yulin 2024, inda ya ƙarar da kakar da ta gabata a matsayin aro a Girona da ke Spain.

    A bara ma ta so ɗaukar ɗan wasan, sai dai Etihad ba ta shirya sai da shi ba a lokacin.

    A watan Oktoban da ya gabata ne ya sanya hannu kan kwantaragin shekara biyu wadda za ta kai shi zuwa 2031 a City.

  18. Tunisia ta naɗa Moin Chaabani a matsayin sabon kocinta

    a

    Asalin hoton, Reuters

    Tunisia ta naɗa Moin Chaabani a matsayin sabon kocin ƙasar zuwa 2030, kamar yadda Hukumar Kwallon Kafa ta Tunisia ta sanar.

    Moin Chaabani ya maye gurbin ɗan ƙasar Faransa Herve Renard wanda ya karɓi jagorancin tawagar a wasanni biyu na ƙarshen kofin duniya da aka kammala.

    Hakan ya biyo bayan korar tsohon kocin tawagar Sabri Lamouchi wanda ya kai ƙasar gasar kofin duniya ta 2026 da ya sha kashi a hannun Sweden a wasan farko da ci 5-1.

    "Kwamitin ƙoli na hukumar kwallon ƙafa ta Tunisia ya naɗa Moin Chaabani a matsayin sabon kocin tawagar ƙasar na tsawon shekara huɗu," in ji sanarwar.

    Shi ma Renard bai iya kai tawagar ga nasara ba saboda kashin da suka sha a hannun Japan da ci 4-0 da kuma Netherlands da ci 3-1.

  19. Jurrien Timber ya bar sansanin atisayen Arsenal saboda raunin da ya ji

    a

    Asalin hoton, Getty Images

    Jurrien Timber ya koma London daga sansanin atisayen Arsenal da ke Spain, sakamakon raunin da ya ji a ƙafarsa wanda ya hana shi buga wasannin ƙarshen kakar da aka kammala.

    Dan wasan Netherlands ɗin bai buga wasannin wata biyu ba na ƙarshen kakar da ta gabata saboda raunin da ya ji a idon sawunsa, amma ya dawo a wasan ƙarshe na gasar Zakarun nahiya Turai da suka yi rashin nasra a hannun PSG.

    Kuma jinyar da yake yi a matse-matsinsa ce ta ja bai buga gasar kofin duniya ba.

    Duk da cewa an ji labarin ya koma London amma majiyoyi na cewa ya koma ne domin ganin likita ba wai domin wata sabuwar matsala ba.

    Ana sa ran Jurrien Timber zai koma Spain ya ci gaba da atisaye tare da abokan kwallonsa.

    Dan wasan ya buga wasa 30 a gasar Premier wadda suka lashe a bara.

  20. Wane sauyi Infantino ke son kawowa Fifa da Kofin Duniya?

    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya Fifa, ya rubuta wasaƙa zuwa ga hukumomin kwallon ƙafa 211 cewa za a ba su dalar Amurka miliyan $40m, idan suka goyi bayan ƙudurinsa mai cike da taƙaddama na shirin sayar da wani ɓangare na gasar kofin duniya.

    Infantino ya sanya ranar 19 ga watan Satumba ga Hukumomin Kwallon Ƙafa na ƙasashe su nuna amincewarsu ga shirin nasa idan har suna son samun ainihin kuɗaɗen da suka kai $20m.

    Hukumar kwallon ƙafa ta duniya ta ce tana son samar da wani ɓangare na kasuwanci zai iya tafiyar da ainihin abubuwa ciki har da Kofin Duniya, kuma masu zuba jari na waje za su iya zuba kudade domin samun hannun jari.

    Cikin ƙasa da kwana guda da wannan sanarwa Fifa da Infantino suka fara shan suka daga hukumomin kwallon ƙafa na Turai da Asia da kuma Arewacin Amurka.

    Akwai bayanan da ke cewa Infantino bai janyo mataimakansa takwas ba a cikin shirin nasa, wanda ake tsammanin zai samar musu da kuɗin shiga da ya kai dala biliyan 10.

    Infantino ya sanya hannu kan wata wasiƙa mai ɗauke da shafuka biyar da BBC ta samu kwafi, inda ya yi bayani filla-filla kan shirin nasa.

    Wasiƙar ta ce idan mambobin Fifa suka amince da shirin nan da lokacin da aka ɗiba to za su samu dala miliyan 20 ba tare da bata lokaci ba daga nan zuwa 1 Janairun 2027.