Kotu ta ce Jonathan zai iya tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, babban birnin Najeriya ta ce tsohon Shugaban ƙasar Goodluck Jonathan zai iya tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
A makon da ya gabata ne wani ɓangare na Jami'iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki ya amince wa Jonathan ya yi wa jam'iyyar takara.
Sai dai wani Johnmary Jideobi ya shigar da ƙara yana neman kotu ta hana Jonathan takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Wanda ya shigar da ƙarar tun farko ya nemi kotu ta hana INEC amincewa ko ma wallafa sunan Jonathan cikin jerin ƴan takarar shugaban ƙasa.
Ya kuma buƙaci kotu ta fayyace ko Jonathan ya cancanci ya sake yin takarar shugaban ƙasa bisa tanade-tanaden sashe na 1(1), (2), (3) da 137(3) na Kundin tsarin mulkin Najeriya.
Sai dai a hukuncin da ya yanke yau Talata, alƙali Peter Lifu ya ce Jonathan zai iya takara a zaɓen na 2027.
Ya kuma buƙaci Jideobi ya biya tsohon shugaban Najeriyar tarar naira miliyan 20 sannan kuma ya biya tarar naira miliyan ɗaya ga babban atoni janar na Najeriya.
Alƙali Lifu ya ce Jideobi ba shi da hurumin shigar da ƙarar kasancewar babu wata asara gare shi kan takarar Jonathan a zaɓen 2027.