An samu wasu daga kayan atisayen Ingila da aka sace kafin ta je Kansas City, Gasar kofin duniya

Asalin hoton, Getty Images
Tawagar Ingila ta samu nasarar samun mafiya yawan kayan atisayenta da aka sace kafin isa birnin Kansas City ranar Asabar.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an dawo da kayan da aka sace bayan da aka fasa motocin da ke jigilar kayan zuwa sansanin horo na tawagar a ƙauyen Swope Soccer da ke Kansas City.
Koci, Thomas Tuchel da ƴan wasansa za su isa Kansas City da yammacin Asabar, kuma an shirya cewa kayan za su kasance a birnin tun kafin isowarsu.
Daga cikin kayan da aka sace akwai takalman ƴan wasa, amma ba a sace manyan takalman ƙwararru ba, kuma babu wani muhimmin kayan da aka ɗauka da zai shafi wasanni wasan farko da za ta yi a cikin rukuni..
Jami’an ƴansanda, waɗanda ke ci gaba da tattaunawa da Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila (FA), sun isa wurin tun a daren Juma’a domin gudanar da bincike kan lamarin.
An kuma fahimci cewa an kama mutane biyu da ake zargi da hannu a cikin wannan satar.
Ingila za ta fara atisaye da sanyin safiyar Lahadi.
























