Akwai yiwuwar samun ambaliya a jihohin Najeriya 14
Hukumar kula da madatsun ruwa ta Najeriya (NIHSA) ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar a samu ambaliya a wasu sassan jihohi 14 na ƙasar tsakanin 14 zuwa 20 ga watan Yuli.
Darakta Janar na hukumar, Umar Mohammed, ya ce hasashe ya nuna akwai yiwuwar koguna su cika bayan rahotannin da hukumar ta samu.
Ya ce daga cikin wuraren da aka fi sa ran ambaliyar za ta iya shafa akwai Saminaka da ke kusa da kogin Karam da yankin madatsar Waya ta kogin Waya, da kuma Amber da ke ta wajen kogin Amber.
Jihohin da NIHSA ta ce za su iya fuskantar matsakaicin haɗarin ambaliya sun haɗa da Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Benue, Borno, Cross River, Edo, Enugu, Imo, Kaduna, Legas, Neja da kuma Filato.
Hukumar ta yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki matakan kariya ba, ambaliyar na iya shafar al'ummomi da dama tare da lalata muhimman wurare kamar makarantu, cibiyoyin lafiya, kasuwanni da sauran ababen more rayuwa.
Saboda haka, NIHSA ta buƙaci mazauna yankunan da aka fi fargabar ambaliya su koma wurare masu aminci, su kuma riƙa share magudanan ruwa, su guji bi ta hanyoyin da ruwa ya mamaye, sannan su riƙa bibiyar sanarwar hasashen ambaliya da hukumar ke fitarwa.
Hakazalika, hukumar ta buƙaci gwamnatocin jihohi da hukumomin bayar da agajin gaggawa su kasance cikin shirin ko ta kwana da shirye-shiryen kwashe jama'a daga yankuna masu haɗari da kuma wayar da kan al'umma.