Najeriya ta kammala kwashe ƴanƙasarta daga Afirka ta Kudu

Asalin hoton, TOYIN ADEDOKUN / AFP via Getty Images
Hukumomin Najeriya sun kammala kwashe ƴanƙasar daga Afirka ta Kudu bayan ƙazancewar zanga-zangar ƙyamar baƙi a ƙasar.
A yau ne jirgi na ƙarshe kuma na shida ɗauke da ƴanƙasar 306 ya sauka a filin jirgin saman Legas.
Zuwa yanzu fiye da ƴan Najeriya 1,200 ne hukumomin ƙasar suka kwaso a ƙarkashin nwani shirin gwamnatin ƙasar na mayar da ƴanƙasar gida bayan ɓarkewar zanga-zangar ƙyamar baƙi..
Zanga-zangar wadda a wasu yankunan ake yinta lafiya, ta ƙazance a wasu yankunan har da kisa.
Gwamnatin Najeriya ta ce za ta nemi diyya daga gwamnatin Afirka ta Kudu ga ƴanƙasarta, waɗanda aka tilasta wa barin sana'o'insu da gidajensu da kuma kadarorinsu a Afirka ta Kudu


















