DR Congo za ta karɓi baƙin hauren da aka kora daga Amurka

Asalin hoton, Flex X
Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango za ta karbi 'Yan kasashen waje da aka kora daga Amurka, karkashin wata yarjejeniya da gwamnatin Trump.
Kinshasa ta ce Washington zata biya kudaden da za a yi amfani da su wajen hidimar mutanen da zasu fara isowa a wannan watan.
An kulla yarjejeniyar ya yin da Washington ke ƙoƙarin sulhu tsakanin Kwango da Rwanda.
Amurka ta aike da ƴan ƙasashen waje da suka fito daga ƙasashen Afrika da dama da suka hada da Ghana da Kamaru, sai dai wannan mataki ya janyo suka daga kungiyoyin kare hakkin ƴan Adam da kuma masana shari'a.

















