Ranar Mata ta Duniya: 'Yaran da ake haifa da larurar kwakwalwa ba ƴaƴan aljannu ba ne'

An wallafa

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

A matsayinta na uwa kuma wadda ta sadaukar da rayuwarta gaba ɗaya wajen kula da ƴaƴanta biyu masu buƙata ta musamman, kusan ta fi shan wahala fiye da sauran iyaye mata.

Fatima Ahmed, mahaifiyar ƴaƴa uku ce, takan shafe yininta tana hidimar kula da ƴaƴanta biyu -- daga ciyarwa da tsaftace su da kuma yin wasa tare da su.

Ta shaida wa BBC cewa ƴaƴanta biyu suna da fama da nau'in ciwon da ya shafi ƙwaƙwalwa. Danta na biyu dan shekara biyar yana da wani nau'in ciwo da ya shafi kwakwalwa da ake kira Cerebral Palsy.

Haka ma ƴarta ta uku kuma yar shekara ɗaya da rabi tana fama da ciwon da ya shafi kwakwalwa da ake kira Downs' Syndrome a turance.

"Ina rayuwa mai cike da ƙunci da ƙalubale. Amma bayan na haifi ƴata, ta biyu da ke da matsala, sai na yanke shawarar zama a gida don fahimtar girman matsalar da kuma hanya mafi dacewa da kula da ƴaƴana," in ji ta.

Ta ce ko wannensu ba ta samu matsala ba na laulayin ciki, kuma har zuwa lokacin da ta gama zuwa awon ciki ba a gane cewa akwai matsala ba har sai da ta haihu sannan aka gano yaran suna dauke da matsala ta daban.

An kiyasta cewa kimanin mutum miliyan 25 ne ke fama da nakasa a Najeriya, amma duk da girman matsalar ba a damu da kula da buƙatunsu ba, musamman samun kulawar lafiya da ilimin da ya dace.

Babban ƙalubalen shi ne yadda ake nuna musu ƙyama, musamman yaran da aka haifa da nakasa.

Dalilin wannan rayuwa da Fatima ta tsinci kanta a ciki ne ya sa ta ƙirkiri wata ƙungiya domin wayar da kan iyaye da ke da yara masu buƙata ta musamman domin fadakar da su kan irin waɗannan nau'in cutukan da kuma yadda za su tafiyar da rayuwarsu ba tare da sun samu matsala ba.

A matsayinta na uwa, burinta shi ne sauya yanayin musamman ga yaran da kuma masu kula da su.

Fatima na wayar da kan mutane ne a shafukan sada zumunta. "Na lura yawanci a arewa ba a maganarsu musamman kan wannan nau'in cuta da ake akalantawa da aljannu ko a ce ƴaƴan ruwa ne."

"Ina amfani da ilimina da kuma yadda na yi rayuwa da ƴaƴana, domin wayar da kan mutane cewa wannan matsala ce ta asibiti idan ana kulawa za su rayu har su yi aure.

Ƙalubale

Fatima ta ce babban kalubalen da ta fuskanta ya shafi ɓangaren lafiya ne. "Ba a cika samun maganin da zai tafi daidai da ciwonsu ba ko kuma kulawar da suke bukata dole sai an fita zuwa kasashen waje."

"Ba mu samun kulawar da ta dace musamman wannan da ke tattare da matsaloli. Kuma wannan matsala ce da ke buƙatar kuɗi."

"Akwai yausayi a matsayina na uwa saboda rashin samun kulawar da ta dace musamman a asibiti da kuma tsadar ilimi da makarantu da suke tsawwala hidimar ilimin yaran," in ji ta.

Babu dai wasu alƙaluma na hukuma da suka tabbatar da yawan masu buƙata ta musamman a Najeriya, amma yawanci suna fuskantar kyara da kuma dnaganta su da matsaloli da suka shafi al'adu.