Matar da mijinta ya cire wa ido bayan ta kama shi da wata a kan gadonsu na aure

    • Marubuci, Asha Juma
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Nairobi
    • Aiko rahoto daga, Nairobi
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Mace kan bar gidan iyayenta a lokacin aure domin zuwa ta zauna da wani wanda hankalinta ya kwanta da shi, bisa tunanin cewa za su rayu har abada.

To sai dai wani lokaci a kan samu akasi, inda za ki iske wanda kika aura ya sauya, tamakar wanda ba ki taɓa sani ba.

Irin wannan hali ne Rosana Kathure ta samu kanta a ciki, kamar yadda ta shaida wa BBC.

Bayan tunanin cewa za ta samu farin ciki a gidan aure, Asha, wadda ke zaune a yankin Meru na ƙasar Kenya ta tsinci kanta cikin mummunan yanayi a cikin aure.

Rosana ta tuno lokacin da ta hadu da uban ƴaƴanta, inda a lokacin suke soyayya tamkar su haɗiye juna.

Bayan shan soyayya na ƙanƙanin lokaci sai suka sanyo manya a cikin lamarin.

Lokacin da Rosana take tuno irin soyayyara da suka sha, ita da tsohon mijin nata, wani murmushi ne da haske a fuskarta.

''Bayan mun yi aure akwai lokacin da yakan dawo gida a buge, haka nake wanke masa ƙafafu da jiki sannan na kwantar da shi a gado ya shaƙi bacci," in ji Rosana.

Sai dai Rosana ta ce bayan wasu ƴan shekaru sai halayyar mijin nata ta sauya.

''A lokacin da na haifi ɗana na farko da na biyu, duk muna zaune lafiya. To amma a lokacin da ɗana na uku ya kai wata huɗu sai na fara lura da cewa halayyar mijina ta sauya."

''Sai ya fara shan wiwi da ganye iri-iri. Zai kama ni da duka ba tare da wani dalili ba, ya yi ta faɗa babu gaira babu dalili, har yana watsi da abinci, ni ma da na ga haka sai na fara mayar da martani,'' in ji Rosana.

Rosana ta bayyana cewa tabbas bayan da halayyar mijinta ta sauya, ita ma tata halayyar ta sauya, inda ta zama mai yawan masifa har ta riƙa yi wa mijinta barazanar yin yaji.

Sai dai duk da haka mijin nata bai saussauta ba, ya ci gaba da zama bala'ƴa'e.

"Amma yakan ce min gara ya kashe ni da hannunsa, a maimakon ya bar ni na koma gidanmu," in ji Rosana.

Lamarin ya kai ga cewa babu komai da ke faruwa a gidan Rosana sai masifa.

'Daren da bala'i ya sauka a kaina'

Abubuwa sun ƙara muni bayan da Rosana ta haifi ɗanta na ƙarshe, lokacin yana da wata biyu a duniya, a lokacin ne abin da ba ta taɓa zato ba ya faru.

Rosana ta ce ba ta san cewa rayuwarta ta kusa sauyawa ba har abada.

A lokacin da gari ya waye sai ta ɗauki jaririnta zuwa asibiti domin duba lafiyarsa, inda ta bar mijinta tare da sauran yaransu uku a gida.

Ta ce ta ci sa'a a ranar babu dogon layi a asibiti.

Ba tare da ɓata lokaci ba aka yi wa yaronta allurar rigakafi sannan ta kama hanya ta koma gida.

To amma lokacin da ta isa gida sai ta ci karo da wani abu da ba ta taɓa tsammani ba.

''Na iske mijina kan gadon aurenmu kwance da wata matashiya ƴar aji huɗu a sakandare. Wannan ne abin da ya kawo ƙarshen aurenmu," in ji Rosana.

Lokacin da Rosana da iske mijinta kwance da yarinyar, sai yarinyar ta gudu ta bar gidan kafin ta kama ta.

''Sai ya rage daga ni sai shi a ɗakin, inda yake zaune a bakin gado, ni kuma na ajiye yarona a gefe," in ji Rosana.

"Sai ya tashi ya tare bakin ƙofa, ya ce min 'kullum kina cewa za ki koma gidanku. To gara na sauya miki kamanni kafin ki koma gidanku, saboda na san idan kika tafi za ki je ki sake yin wani auren ne, gara na kashe ki kuma na kashe kaina," kamar yadda Rosana ta shaida wa BBC abin da tsohon mijin nata ya faɗi.

Ta ƙara da cewa "Kuma ya aikata abin da ya faɗa. Ya lalata min ƙwayar idona. Yanzu ba ni da ido ɗaya kuma ya yi min mummunan sara a kaina. Ya yanke ni da wuƙa a ciki, har ana ganin ƴaƴan hanji, sannan ya yanke ni a ƙafa," Rosannan tana bayar da labari tana kuma nuna tabon wuraren da ya yanke ta.

'Darasin da na koya'

Lokacin da Rosana ta fara ihu domin janyo hankalin maƙwabta, sai mijin ya sake kawo mata sara da wuƙa.

"Sai ya yanke min ido, tun daga sama har ƙasar. Lokacin da na juya sai ya sake kawo min sara a kan ɗayan idona, amma bai same ni ba," in ji Rosana.

Wannan ne abin da ya sa Rosana ta rasa idonta ɗaya.

"Lokacin da mijina ke sara ta, sai yarona wanda na ɗauka na rungume a ƙirjina ya riƙa shan jinin da ke kwararowa daga kaina," in ji Rosana.

A lokacin ne dukkanin ƴaƴanta suka fara kuka suna ihu, wanda hakan ya janyo hankalin maƙwafta suka kawo mata ɗauki.

"A lokacin da maƙwafta suka zo sai ya gudu, ya tafi wani gida mai nisa, inda ba su san abin da ya faru ba, a can ya kwana.

"Sai dai a lokacin da gari ya waye, sai aka gan shi ya rataye kansa a saman wata bishiya, lamarin da ya bai wa mutanen gidan mamaki," Rosana ta ce a haka mijin nata ya kashe kansa.

Rosana ta suma saboda zubar jini, lamarin da ya sanya maƙwafta suka garzaya da ita asibiti.

Ta bayyana cewa a asibiti ne aka cire rage-ragen idonta guda ɗaya wanda mijin nata ya lalata ta hanyar yanka da wuƙa, wanda har idon ya ruɓe ya fara wari.

"Na kwashe wata uku ina jinya, ba na iya cin abinci da kaina, ko zama ko magana," in ji Rosana.

Matar ta bayyana cewa babban kuskurenta shi ne amincewa da soyayyar tsohon mijinta.

"In da na san cewa wanda zan aura shi ne zai cire min ido ya sare min hannuna haka, da ban aure shi ba".

"Yanzu duk tabbai ne a jikina a dalilin soyayya," in ji Rosanna.

Ta bai wa mata da ke fuskantar matsala a gidajen aurensu shawara:

"Idan kina yi wa mijinki biyayya amma ya zama masifaffe kamar tsohon mijina, kada ki biye masa, ki bar masa gidan cikin lalama ba tare da kin faɗa masa ba, domin idan kika faɗa masa, to zai iya illata ki. Gara ki koma gidan iyayenki Sali-alin."

Rosana ta kwashe shekara biyu a asibiti kafin ta iya tafiya da ƙafarta.