Hotunan manyan coci-coci 8 mafiya kyau a duniya

An wallafa

Wadannan hotuna ne na wasu daga cikin manya-manyan coci-coci mafiya kyau fadin duniya.

Cocin St. Peter's Basilica da ke Vatican City
Bayanan hoto, Cocin St. Peter's Basilica da ke Vatican City. An fara gina cocin a 18 ga watan Afrilun 1506 aka kuma kammala a 18 ga watan Nuwambar 1626.
Cocin Florence Cathedral
Bayanan hoto, Cocin Florence Cathedral da ke kasar Italiya. Asalin suna cocin shi ne Cattedrale di Santa Maria del Fiore, kuma an fara ginata a 1296 aka kuma kammala a 1436.
Cocin Hagia Sophia
Bayanan hoto, Cocin Hagia Sophia da ke kasar Turkiyya kuma an gina ta a shekarar 537.
Cocin Liverpool Cathedral
Bayanan hoto, Cocin Liverpool Cathedral da ke Ingila kuma an kammala gina cocin a 1978.
Cocin Milan Cathedral
Bayanan hoto, Cocin Milan Cathedral da ke Italiya kuma an kammala ginin cocin ne a 1965.
Cocin San Petronio Basilica
Bayanan hoto, Cocin San Petronio Basilica da ke Italiya. An fara ginin cocin ne a 1390, sai aka kammala a 1954.
Cocin Seville Cathedral
Bayanan hoto, Cocin Seville Cathedral da ke kasar Spain kuma an kammala ginita a 1528.
Cocin Ulm Minster
Bayanan hoto, Cocin Ulm Minster da ke kasar Jamus kuma an fara ginin Cocin a 1377 sai aka kammala a 1890.