Wane hali ake ciki kan ceto ɗaliban da aka sace a Borno?

Dalubai

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Fiye da wata biyu bayan sace ɗalibai a makarantu uku da ke garin Mussa a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, har yanzu iyaye na jiran ganin an ceto ƴaƴan nasu.

Yawaitar satar yara a makarantun Najeriya a baya-bayan nan na daga cikin abubuwa da ke nuna cewa har yanzu matsalar tsaron da ƙasar ke fama da ita na nan, duk da iƙirarin da gwamnatin ƙasar ke yi na cewa tana bakin ƙoƙarinta.

A baya-bayan nan ƴan bindigar sun ƙara ƙaimi wajen sace ɗalibai a sassa daban-daban na ƙasar.

A ranar 10 ga Yulin 2026, gwamnatin Najeriya ta sanar da ceto wasu ɗalibai da malaman makarantar da aka yi garkuwa da su a jihar Oyo, kwanaki 56 bayan sace su daga makarantarsu da ke ƙaramar hukumar Orire a yankin Ogbomoso na jihar Oyo.

Gwamnatin ta ce dakarunta ne suka ceto mutanen daga hannu waɗanda suka yi garkuwa da su, ta kuma musanta zargin biyan kuɗin fansa kafin ceto su.

Sai dai yayin a jihar Oyo ake murnar ceto ɗalibai da malaman, har yanzu ɗaliban da aka sace a ƙaramar hukumar Askira Uba, cikin har da ƙananan yara yan ƙasa da shekara biyar na ci gaba da zama a hannun masu garkuwa da su.

Wane ƙoƙari gwamnati ke yi domin ceto su?

A taya mu da addu'a - Gwamnati

Gwamnan jihar Borno

Asalin hoton, Getty Images

A tatatunawarsa da BBC, kwamishina yaɗa labarai da tsaron cikin gida na jihar Borno Farfesa Usman Tar, ya ce gwamnatin jihar tana ƙoƙarin ta wajen tallafa wa sojoji da jami'an tsaron DSS domin ganin an ceto yaran daga hannun waɗanda suka yi garkuwa da su.

Ya ce gwamnati tana aika saƙo ga waɗanda ke riƙe da yaran, ta hannun iyayensu da aika saƙo ta waya da kuma ta kafafen rediyo domin jan hankalin su cewa ''su ji tsoron Allah su saki yaran nan, saboda yara ƙanana ne ba wani laifi suka yi ba.''

Farfesa Tar ya ce gwamnan jihar da kwamishinoninsa sun kai ziyara ƙauyukan da abin ya faru kuma sun yi taro da iyayen da sarakuna da sauran manyan gari, inda aka tsara yadda za a ci gaba da ''gwagwarmaya'' domin ceto yaran.

''A cikin matakan da aka ɗauka da iyayen shi ne a yi addu'a, a ci gaba da yin addu'a, kar a yi ƙasa a gwiwa wajen addu'a,'' in ji Farfesa Tar.

Ya jaddada matsayar gwamnati a kan cewa ba ta biyan kuɗin fansa, amma tana bakin ƙoƙarin ta domin ganin an ceto ɗaliban.

Wane hali iyaye Ke ciki?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A wata tattaunawa da BBC a makon da ya gabata, iyayen yaran sun ce suna cikin tashin hankali saboda rashin tabbacin halin da ƴaƴansu ke ciki, tare da kira ga hukumomin Najeriya su ƙara ƙaimi wajen ganin an ceto ƴaƴan nasu.

Ɗaya daga cikin iyayen, Bukar Buba, ya shaida wa BBC cewa suna cikin "baƙin ciki da takaici", ganin cewa har yanzu ƴaƴansu na hannun masu garkuwa da mutane duk da cewa an saki waɗanda aka sace a Oyo.

Ya ce iyayen ba su ji daɗin yadda har yanzu ƴaƴansu na ci gaba da zama a hannun ƴan bindiga ba, inda ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta gaggauta ɗaukar matakan da za su kai ga kuɓutar da su.

"Muna cikin baƙin ciki tun bayan da aka sace mana yaranmu. Ba mu ma san halin da suke ciki a cikin daji ba, musamman a wannan lokacin na damina. Mun sha kuka tare da roƙon gwamnati ta taimaka ta ceto yaranmu, amma har yanzu ba mu ji wani labarin sakin su ba," in ji Buba.

Ya ƙara da cewa "Kwamishinan ilimi ya gana da wasu daga cikin iyayen, ya kuma gaya mana cewa gwamnati na shirin fara tattaunawa da masu garkuwa da yaran."

Gwamnatin Najeriya ta haramta biyan kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane. Wata doka da aka kafa a shekarar 2022 ta ayyana biyan kuɗin fansa a matsayin laifi, kuma gwamnati ta sha musanta rahotannin da ke cewa tana biyan kuɗi domin a saki waɗanda aka sace.

A watan Nuwamban 2025, bayan da ƴan ta'adda suka yi garkuwa da fiye da ɗalibai da ma'aikata 200 daga wata makarantar kwana ta Katolika da ke Papiri a jihar Neja, an yi ta yaɗa rahotannin cewa gwamnati ta biya "kuɗin fansa" mai yawa ga Boko Haram domin a sake su.

Sai dai Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya musanta wannan zargi, inda ya ce ƙarya ce tsagwaronta, kuma hakan zubar da mutunci da ƙwarewar jami'an tsaron Najeriya ne.

Jihar Borno ita ce cibiyar rikicin Boko Haram, rikicin da aka shafe fiye da shekara 15 ana fama fa shi.

Rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane da tarwatsa wasu miliyoyi daga muhallansu.

Duk da cewa a baya gwamnatin kasar ta yi ikirarin karya lagon ƙungiyar to amma har yanzu hare-hare da mayaƙanta ke kaiwa na cigaba da zama babbar barazana.

Jihar Borno ta sha tsintar kanta cikin matsalar satar ɗalibai a lokuta daban-daban.

A watan Afurilun 2024 Boko Haram ta kai hari kan makarantar ƴanmata ta Chibok inda ta sace ɗalibai kimanin 276 kuma har yanzu wasu daga cikin su ba a san inda suke ba.