Mutum shida da gwamnatin Najeriya za ta gurfanar kan zargin juyin mulki

Lokacin karatu: Minti 5

Gwamnatin Najeriya ta shirya domin gurfanar da fararen hula guda shida a gaban kotu bisa zarginsu da hannu a yunƙurin da hukumomin ƙasar suka zargi sojoji da yi na kitsa hamɓarar da gwamnatin Bola Tinubu.

A watan Janairun bana ne hukumomin tsaro na Najeriya suka sanar da cewa sun samu wasu jami'an soji da laifin kitsa juyin mulki a ƙasar, wadda suka ce an yi a shekarar da ta gabata.

Cikin wata sanarwa da hedkwatar tsaron ƙasar ta fitar, ta ce ta samu wasu hafsoshi 16 da laifin yunƙurin kifar da gwamnatin shugaba Tinubu cikin watan Oktoban 2025.

Cikin watan Oktoban ne rundunar sojin ƙasar ta kama sojojin tare da ƙaddamar da bincike a kan su bayan zarginsu da abin da ta kira rashin ladabi da saɓa wa dokokin aikin soji.

Hedkwatar tsaron ƙasar ta ce ta fitar da sanarwar ce bayan ta kammala binciken, inda ta ƙara da cewa da dama cikin sojojin da aka tsaren suka tabbatar da yunƙurin juyin mulkin, wani abu da rundunar sojin ƙasar ta ce ya saɓa wa ƙa'idojin aikin soji da kundin tsarin mulkin Najeriya.

Rundunar sojin ƙasar ta ce nan gaba za a gurfanar da jami'an gaban kotun soji don yi musu hukunci.

Sai dai a daidai lokacin da ake jiran sakamakon binciken sojojin, gwamnatin ta shirya fara gabatar da fararen hula.

Daga cikin fararen hula da suka ɗauki hankali akwai fitaccen malamin addinin Musulunci a arewacin Najeriya, Sheikh Abdulƙadir Sani Khalifa Zaria, wanda ya kwana biyu a tsare.

An kama malamin ne a ranar 11 ga watan Disamban 2025, kuma iyalan malamin sun ce suna zargin an kama malamin ne bayan kyautar Naira miliyan biyu da wani ɗalibin shugaban ɗariƙar Tijjaniya ta Fityanul Islam ya ba shi, da aka yi zargin jami'in yana da hannu a yunƙurin juyin mulkin.

Mutanen da za a gurfanar

Mutum shida ɗin da za a gurfanar, duk da cewa takardar tuhumar ta ƙunshi mutum bakwai ne, inda takardar ta ƙara da cewa Timpre Sylva, tsohon gwamnan Bayelsa kuma tsohon ministan man fetur ya tsere. Waɗanda suke hannu su ne:

  • Manjo janar Mohammed Ibrahim Gana mai ritaya
  • Kyaftin na sojan ruwa Erasmus Ochegobia Victor mai ritaya
  • Insfekta Ahmed Ibrahim
  • Zekeri Omuru
  • Bukar Kashim Goni
  • Abdulƙadir Sani

Tuhume-tuhume 13

Takardar wadda aka fitar a ranar 20 ga watan Afrilu, ministan shari'ar ƙasar Lateef Olasunkanmi Fagbemi SAN da daraktan gabatar da ƙara, Oyedepo Iseoluwa Rotimi ne suka sa hannu.

  • "Manjo janar Mohammed Ibrahim Gana mai ritaya da Kyaftin na sojan ruwa Erasmus Ochegobia Victor mai ritaya da Insfekta Ahmed Ibrahim da Zekeri Omuru da Bukar Kashim Goni da Abdulƙadir Sani da Timpre Sylva (wanda ya tsere) da wasu kun haɗa baki a shekarar 2025 domin kifar da gwamnatin Najeriya, kuma hakan ya sa kuka aikata laifi, inda kuka cancanci hukunci a ƙarƙashin sashe na 37 (2) na kundin laifuka na 2004."
  • "Manjo janar Mohammed Ibrahim Gana mai ritaya da kyaftin na sojan ruwa Erasmus Ochegobia Victor mai ritaya da Insfekta Ahmed Ibrahim da Zekeri Omuru da Bukar Kashim Goni da Abdulƙadir Sani da Timpre Sylva (wanda ya tsere) da wasu a bara a Abuja kun sani Kanal Mohammed Alhassan Ma'aji da wasu na yunƙurin cin amanar ƙasa, amma ba ku tona masa asiri ba, wanda laifi ne da ya cancanci hukunci a ƙarƙashin sashe 40(b) na kundin laifuka."
  • "Manjo janar Mohammed Ibrahim Gana mai ritaya da Kyaftin na sojan ruwa Erasmus Ochegobia Victor mai ritaya da Insfekta Ahmed Ibrahim da Zekeri Omuru da Bukar Kashim Goni da Abdulƙadir Sani da Timpre Sylva (wanda ya tsere) da wasu a bara a Abuja kun sani Kanal Mohammed Alhassan Ma'aji da wasu na yunƙurin cin amanar ƙasa, amma ba ku yi yunƙurin hanawa ba, wanda laifi ne a ƙarƙashi sashe 40(b) na kundin laifuka na 2004."
  • "Manjo janar Mohammed Ibrahim Gana mai ritaya da Kyaftin na sojan ruwa Erasmus Ochegobia Victor mai ritaya da Insfekta Ahmed Ibrahim da Zekeri Omuru da Bukar Kashim Goni da Abdulƙadir Sani da Timpre Sylva (wanda ya tsere) kun haɗa baki a Abuja a bara domin aikata ta'addanci a Najeriya, wanda laifi ne a ƙarƙashin sashe na 26(1) na kudin dokokin ta'addanci na 2022."
  • "Insfekta Ahmed Ibrahim da Zekeri Omuru kun halarci taron da ke da alaƙa da ta'addanci, kuma kun yi laifi a ƙarƙashin sashe 2(3) da 12(a) na kundin yaƙi da ta'addanci na 2022."
  • "Manjo janar Mohammed Ibrahim Gana mai ritaya da Kyaftin na sojan ruwa Erasmus Ochegobia Victor mai ritaya da Insfekta Ahmed Ibrahim da Zekeri Omuru da Bukar Kashim Goni da Abdulƙadir Sani da Timpre Sylva (wanda ya tsere) da wasu a bara a Abuja kun taimaka wa Kanal Mohammed Alhassan Ma'aji da wasu da saninku ko ba tare da saninku ba wajen aikata ta'addanci, wanda laifi ne a ƙarƙashin sashe na 13(1) (a) na kundin yaƙi da ta'addanci na Najeriya na 2022."
  • "Manjo janar Mohammed Ibrahim Gana mai ritaya da Kyaftin na sojan ruwa Erasmus Ochegobia Victor mai ritaya da Insfekta Ahmed Ibrahim da Zekeri Omuru da Bukar Kashim Goni da Abdulƙadir Sani da Timpre Sylva (wanda ya tsere) da wasu kuna da bayanin da zai taimaka wajen daƙile yunƙurin Kanal Mohammed Alhassan Ma'aji, wanda laifi ne a ƙarƙashin sashe na 16(1) (a) na kundin ta'addanci na 2022."
  • "Manjo janar Mohammed Ibrahim Gana mai ritaya da Kyaftin na sojan ruwa Erasmus Ochegobia Victor mai ritaya da Insfekta Ahmed Ibrahim da Zekeri Omuru da Bukar Kashim Goni da Abdulƙadir Sani da Timpre Sylva (wanda ya tsere) da wasu a bara a Abuja kuna da bayanin da zai taimaka wajen kama Kanal Mohammed Alhassan Ma'aji, amma ba ku bayyana ba, wanda laifi ne a ƙarƙashin sashe na 16(1)(b) na kundin yaƙi da ta'addanci na Najeriya na 2022."
  • "Abdulƙadir Sani a ranar 23 ga watan Satumban 2025 an tura maka kuɗi naira miliyan biyu a asusun bankin Ja'iz mai lamba 0005620270 daga kamfanin A & A Express Link Concept, kuma kuɗi ne da ya kamata ka san yana cikin kuɗin ɗaukar nauyin ta'addanci, kuma laifi ne da ya saɓa sashe 18(2)(d) na halasta kuɗin haram na 2022 wanda sashe na 18 (3) ya tanada wa hukunci."
  • "Bukar Kashim Goni a watan Satumban 2025 a Abuja aka tura maka naira miliyan 50 a asusun bankinka na First Bank mai lamba 3021511166 daga kamfanin A & A Express Link Concept, kuma kuɗi ne da ya kamata ka san yana cikin kuɗin ɗaukar nauyin ta'addanci kuma laifi ne da ya saɓa sashe 18(2)(d) na halasta kuɗin haram na 2022 wanda sashe na 18 (3) ya tanada wa hukunci."
  • "Zekeri Omuru a watan Satumban 2025 a Abuja ka karɓi kuɗi naira miliyan 10 daga Kanal Mohammed Alhassan Ma'aji ba tare da zuwa cibiyar kuɗi ba, wanda kuma ya saɓa da sashe na (18)(2)(a) da na 19(1)(d) da kundin hana halasta kuɗin haram kuma sashe na 19(2)(b) ya tanada wa hukunci."
  • "Zekeri Omuru a watan Satumban 2025 a Abuja an tura maka naira miliyan 8,800,000.00 a asusun bankinka na Zenith mai lamba 2006041878 wanda kuma ya kamata ka gane cewa kuɗi ne na ɗaukar nauyin ta'addanci, wanda kuma laifi ne da ya saɓa da sashe 18(2)(d) na kuma sashe na 18 (3) na kundin yaƙi da halasta kuɗin haram ya tanada wa hukunci."
  • "Insfekta Ahmed Ibrahim a watan Satumban 2025 a Abuja ka karɓi naira miliyan 1 daga Kanal Mohammed Alhassan Ma'aji wanda ya kamata a ce ka san kuɗin ɗaukar ta'addanci ne, kuma laifi ne da ya saɓa sashe 18(2)(d) na halasta kuɗin haram na 2022 wanda sashe na 18 (3) ya tanada wa hukunci."