Liverpool da United na son Thiaw, Chelsea za ta taya Scott

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Liverpool da Manchester United na bibiyar ɗan bayan Jamus Malick Thiaw, mai shekara 25. Sai dai Newcastle United ba ta da niyyar sayar da ɗan wasan. (Caught Offside)

Ɗan wasan gefe na Sunderland, Chemsdine Talbi, mai shekara 21, na daf da cimma yarjejeniya da ƙungiyar Saudiyya ta Al-Ittihad. (Football Insider)

Fulham na shirin fara tattaunawa kan sabon kwantiragi da ɗan bayanta Calvin Bassey, mai shekara 26, wanda Inter Milan ke nuna sha'awarsa. (Teamtalk)

Ɗan wasan gefe na Bournemouth, Rayan, mai shekara 20, yana da sharadin saye na fam miliyan 130 wanda zai fara aiki a kasuwar musayar 'yan wasa ta bazarar shekarar 2027. (David Ornstein via the Athletic - subscription required)

Ɗan wasan tsakiya Joe Willock, mai shekara 27, zai samu sabon kwantiragi daga Newcastle United idan ya ci gaba da nuna bajinta a ƙarƙashin koci Matthias Jaissle. (Football Insider)

Tsohon ɗan wasan tsakiya na Real Madrid, James Rodriguez, mai shekara 35, na tattaunawa da ƙungiyar Serie B ta Italiya, Avellino, wadda tsohon ɗan bayan Italiya Alessandro Nesta ke horarwa.(Marca)

Chelsea na shirin gabatar da tayi domin sayen ɗan wasan tsakiyar Ingila na Bournemouth, Alex Scott, mai shekara 23, a kasuwar musayar 'yan wasa ta watan Janairu. (Teamtalk)